Chapter 21

5 2 0
                                    

The happy and the sad one
- Wata Friday ina daki gidanmu cike da baki bayan sun tafi ameera ce tazo kirana inji Abba mayafi Na dauka tare da binta fallo muka taddashi gaida shi nayi ya ansa cikin fara'a tare da shimun albarka
      Yar nasiha ya fara mun wanda yasa gabana ya fara fadi dan Abba ba wai baya fada koh nasiha ba amma girma da naga yata daurawa mun ne yasa na fara jin tsoron abun da zai biyo baya
     A cewar shi bazai yimun auren dole ba amma shi da Alh baffah watau mahaifin Mahmoud suna son hada mu aure dan wanan wani tsohon burin su yake gaya mun gashi yaga alama ni da Mahmoud dinma kaman muna fahimtar junna
         No nooooo not me and please, shine abunda nike ta cewa a zuciyata amma na kasa fadi a fili saboda na dadde banga Abba cikin farin ciki haka ba abunda na lura indai abu ance nawa ne Toh fah Abba bai hadda abunnan da komai ba wanan yana daya daga cikin dalilin da yasa mamie bamu jituwa da ita                                    - Tunani nane ya katse inda Abba ke gaya mun shi da abokinshi sun gama yanke shawara yanzu haka shi ta gurin shi suke jira dan yasan wajen dan shi baza samu matsala ba
         Shiru nayi bance komai ba har naga Abba abun yadan bashi tsoro sake tambayana yayi mamana yana ji kinyi shiru dan yake dole nayi nace Abba ba komai Allah yasa haka shi yafi alheri addua ya bini da ita yanata shi mun albarka
          Nan yake gaya mun inna zai sa a dauko daga kwatono tazo ta zauna har lokacin bikin yayi bansan sanda na washe baki gaba daya ba har nama manta da abunda aka fada a baya duk maganar da mukayi mamie na nan zaune a fallon hankalinta na kan tv Abba ne yace toh Zainab ga yarki nan kin dai ji yanda mukayi da ita in akwai wata shawara koh wani abu da kika gani sai kiyi magana muji dan yatsina fuska tayi tace ai duk abunda zance ka riga ka fada sai dai mu jira lokaci kawai
         Ina komawa daki na fada kan gado kuka nayi mai isata anan ne na kara missing uwata koh ba komai ita dole tasan halin da nike ciki I understand Abba shi aganin shi farin ciki zai Samar mun ni kuma bai san ida dagula mun lissafi zaiyi ba dan gaskia bana ma Mahmoud son aure sai dai na mutunci kawai
     Waya tace take ta ringing kaman bazan dauka ba kafin nadan matse Na dauka rahama ce keta surutu a dayan layin nidai bance komai ba nan yake gaya mun ita da mummy sunyi missing dinta gidansu yanzu ba dadi ba kamar ina nan ba
       Dan dariya nayi nace nima nayi missing dinku tambaya ta tayi saboda muryana da ya shake saboda kuka naso boye mata amma sannin halin rahama cikin darena zan iya ganinta gidan nan yanda mukayi da baba na kwashe na gaya mata ba karamin razana tayi ba dan tasan sam bana son mr handsome sai ma tura mata shi da nikeyi kullum hakuri tayi ta bani dace kada in damu insha Allah Allah bazai barmu hakanan ba mun dadde muna waya har sai da tasa na manta tana ta bani labari kafin mukayi sallama.
      Haka cikin dare na kasa bacci alwala kawai nayi nazo nayita nafila da addu'oi washegari tun da safe sai ga wayar Mahmoud da bazan dauka bama wata zuciyar tace dai in dauka bayan mun gama gaisawa cewa yayi yana son ganina anjima in ba komai Allah ya kaimu nace mai mukayi sallamaa

Hasken-taurari book 1Where stories live. Discover now