Getting over mr arrogant
- [ ] Tun daga ranar da muka hadu da imran a Tutty-fruity na dauki alwashin duk wani abu da zai hadani dashi zanyi avoiding dinshi dan rahama tasha gaya mun kada inje in jefa kaina inda fitowa zai mun wahala kuma wanda akeyi dan shi baima san kana yi ba
- [ ] Kwana biyun nan gaba daya na maida hankalina akan karatu na kullum daga makaranta sai islamiyya sai kuwa Mahmoud da kullum sai ya kira in naga dama in dauka in banga dama ba kuma in bata tasha ringing har no rahama na bashi nace in yana neman abokiyar hira ni kuwa kora da hali ne amma bazan iya fitowa kiriri ince mai bana so ba
- [ ] Bazan taba manta wani weekend ba ranar Saturday rahama ce kaman an jefo ta yanda na ganta ni kaina sai da hankalina ya tashi dan kana ganinta kasan akwai matsala fallo ta sameni tambayanta ma nikeyi amma ta kasa bani ansa daki kawai ta shige binta nayi gado ta fada kuka takeyi irin kukan nan marar sauti duk nima sai na rasa me ke mun dadi barin ta nayi sai da tayi mai isarta sanan ta shiga toilet tayi wanka ta kabara sallah tea naje na hado mata tare da banana cake sauran wanda nayi ma baba dazu a gefen gado na sameta cup din na bata ba musu ta karba sai dai hankalin ta na can wani waje
- [ ] Haka tasamu tadan sha tea din kadan cake din koh taba shi batayi ba kwanta tayi nima cup din ta cake din na maida kafin nazo na kwanta ranar dukkanmu mun dadde bamuyi bacci ba duk da ba mai magana cikin mu amma koh ma menene ba karamin taba rahama yayi ba dan ramaha duk inda take bata boyuwa kullum tana cikin hira da raha abunda zai sa tayi shiru toh ba karami ba koh ma dai menene nasan zata gaya mun da wanan bacci ya kwasheni
- [ ] Haka muka tashi da safe har mukayi shirin school kayana ma tasa tan koh kayanta batazo dasu Haka muka karya duk da dukkanmu ba wani abun kirki muka ci ba dan fuska rahama har yanzu ba walwala school mukaje har muka dawo ganin bata da niyar gaya mun komai ne kawai nima na share har yamma yayi muna daki ina ta typing a system sai naji ta fara magana
- [ ] Sist kiyi hakuri kinga jiya nazo duk a hargitse gashi na tada miki hankali ni kaina abunda banta expecting (tunanin ) zai faru ba jiya ya faru tun last month Faisal ke damuna inji inga gidanshi ni kuma banga dalilin hakan ba har last week mukayi fada saboda haka kinsan dai yadda bansan baccin rai Faisal gaba daya yanda hankalina ke tashi har mukayi kwana biyu bamu waya ban kawo komai a raina ba haka na kira shi na bashi hakuri muka shirya sai jiya ya kirani cewan in shirya zamu fita so yake through out muna tare kinsan mummy baza ta yadda da fita ba wani kwakwaran dalili haka nace wajen ki zanzo Faisal yazo ya daukeni nayi mamakin canza mota shi dan wanan har da tint kuma irin mai duhun nan sosai ban kawo komai a raina ba saboda this is Faisal a tunanina ai na sanshi mu danyi ciye ciye mun kafin mukaje wani park ni kaina inda mukayi ta kutsawa da mota banyi tunani ana zuwa wajen ba dan ya shiga can ciki gashi ba mutane sai da daya kuma yawanci saurayi da budurwa zaka gani and abunda sukeyi ba abun birgewa bane ma'ana kana ganin wanda yazo wajen toh kasan ba mutumin kirki ba gabane ya fadi kallon faisal nayi naga koh a jikin shi yanda yake kara shigewa can ciki yasa na tabbatar wanan ba zuwan shi na farko bane can ciki inda ba mutane mukayi parking hannuna ya fara murzawa kallon da yake mun kadai yasa naji yan hanjina sun kunle zanje hannuna nayi tare da cewa Faisal meye haka to my surprise smiling yayi tare da kara kamo hannu kiss yazo zai kaimu na juya aikuwa abun ya bashi haushi tsoro ne ya kara kamani da na tuna labarin da wata kawarmu ta bamu na rape da akeyi a mota koh a park ban Ankara ba sai hucin numfanshi shi dana ji dai dai fuska ta ture shi nayi tare da cewa wai Faisal meye haka fisabillah dan dariya mai kama da yake nan yake gayamun shi gaskia ga bukatar shi inalillahi shine abunda ya fito a bakina rokon shi na fara yi ina hadashi da Allah amma kaman kara tunzurashi nikeyi locking motar yayi gaba daya yayo kaina gaba daya na gama tsorata bansan sanda na gartsa mai cizo ba har sai da naji yayi ihu lock din na bude wanda kafin in fita ya kasheni da mari yana ta huci wai bai taba sanin ni yar kyauye bace sai yau ashe hakanan nike banma waye ba amma sai ya nuna mun koh wa na mara wani yakushi na kaima fuska shi da nasan har idonshi na taba kafin Allah ya bani saar fitowa da gudu ko mayafi babu gudu kawai nike security kansu tambayana sukeyi amma ba ansa a tunanisu kila banda hankali mota kawai nike tsadawa na samu taxi shine fah nazo nan
Tun da ta fara labarin ni kaina kuka nikeyi Haka muka rungume junna muka sha kukanmu mai isar mu ba mai bama kowa hakuri lallai Faisal ya bani mamaki shiysa nike tsoron taraya da maza dan yanzu zamani ya zama abun tsoro Allah ka shirye mu ka kuma kara tsare mu da zuriar mu baki daya ameen lallai Faisal ya karya alkwari kuma yaci amana amma dayake Allah ya tuna asirin shi dan tabbas halinshi ne Allah ya baiyana mana hakuri nayi ta bata da kwantata mata jarabawar ubangiji akan bawansa dan yaga ya rauni imaninshi yake nan wayata ce ta fara ringing mummy ce dauka nayi tare da gaisheta inda taketa fada wai wata irin shiririta ce zata bar wayarta harda jaka a motan faisal hakuri na ba mummy Allah yasa mummy na ji dani yasa tabar maganar dayima fada da nan gaba ai sai a lura kada azo ana neman mu ba waya insha Allah zamu kiyaye mummy shine abunda nace mata kafin mukayi sallama rahama ce ta kalleni tare da rungume ni thank you sist you're the best dan smiling kawai nayi mata nace anything for you 😊
YOU ARE READING
Hasken-taurari book 1
RomanceHighest Ranking A love story about fateema zahra from a fulani tribe she's the naive and innocent girl starting from the days of her college life with her best friend rahama who is the exact opposite of zahra, Imran a guy from a wealthy royal fami...