Back to square one
Biki ya kare komai ya dawo dai dai zahra ce ke shirin komawa Gida daga ita har rahama ba mai jin dadi amma is high time dole in koma jiya mun kwanta nike ma rahama gulman imran cewar tunda Yaya muktar yayi aure bamu kara ganinshi ba tsaki tayi tace kinsan shi da miskilanci kuma abokinshi baya nan ba lalle mu ganshi ba koma ya bar kasar, wa yasani kinsan kaman agogo yake da aiki koh an gama biki alhamdulillah duk da Abba tuntuni ya kira mummy akan in koma rokon shi tayi a ka karamun kwana uku acewarta da kanta zata maidoni gida tayi godiya
Fallo muke zaune dukkan mu sallama akayi sai ga imran wani dadi naji da bansan dalili ba koh ba komai zan kara ganin shi kafin in tafi waje ya samu yadan zauna tare da gaida su mummy da nan daddy ke mai tsiyar tunda abokinshi yayi aure ai yanzu ganin shi zaiyi wuya dan sosa kai kawai yayi tare da smiling gaida shi mukayi ansa yayi tare da kallona na dan wasu second kafin ya mai da kai daddy ne keta dan Jan shi da hira yana bada ansa sallama yayi zai fita inda mummy kaji dan nema yaushe rabon da kazo gidan kuma shine har zaka tafi toh sai ka ci abinci sanan yanda ta nunawa mai no room for arguments ( ba alamar gardama) dole ya tsaya dining tasa dukkan mu mukaje zahra zo kiyi serving yayan ki shine abunda mummy tace mun ba musu na dauki plates rasa me zan sa mai nayi gashi duk abunda nikeyi akan idonshi abinci nayi serving dai dai yanda nike tunanin zai isheshi naje na aje cup na dauka tare da samai juice sai bottle water ( ruwan gora) da na aje mai thank you yace yace so low wanda nima dan ina kusa dashi ne yasa na ji dagowa nayi dan inga dani yake kuwa ko kuma ina dagowa muka hadda ido ashe ni yake kallon dan smiling nayi mai tare da barin wajen da sauri su rahama yan sa ido hankalinta na wajen naga sai wani murmushin munafunci takeyi abinci nasa mana kasancewar munyi ciye ciye a school kadan muka dan kara duk a takure nikeyi na riga kowa barin fallon kafin rahama ta biyo ni daki ta sameni tare da tsare ni da ido tace my sweet sister and bestie what a show dan hadda rai nayi alaman ban gane me take nufi ba gefena ta zauna bakiga movie da kukayi casting bane a fallo dariya ma ta bani tare da dan ture ta, itama dan hada rai tayi tace wlh da gaske nikeyi kinga yanda yaya imran yake kallonki kaman zaki bashi duniya ke kuma sai wani lallaba sai abinci kikeyi and he talk to you right...??? Wlh yau naga abunda ban taba gani ba game dashi dan smiling kawai nayi ita keta surutunta koma dai menene time will tell ai
Washegari mummy ta maida ni Gida ita da rahama sukayi ma baba godiya da uban kayan biki, exams muke tayi yi yau saura kwana bakwai inna tazo duk na kosa kullum cikin lissafi nike da murna a satin muka gama jarabawa rannar da inna tazo ai ranar anga murna dama dakin da zata sauka nasa an gyara mata shi shi tsab ga abinci dai dai irin wanda zata iya ci shi muka sa akayi da sauri sauri na shirya dan abba ya gaya mana sun sauka lagos an sata jirgin abuja wanda nasan ba daddewa zata sauka dukkan mu mukaje taho da ita amma banda mamie dan duk abunda mukeyi kaman bata ma san anayi ba muke cin karen mu ba babbaka, muna isa ko da na hangota da gudu naje tare da rugeta Farouk ne kemun tsiyar kada in karya musu yar tsohuwa abunka da jikin fulani baza ma kace ta kai shekaru ta ba, dan jikinta mai kyau ne hadda kwala jin dadi ita kanta taji dadin ganin mu,ai tun a hanya take shan surutu har su ameera dadi zuwanta sukeji dan tsohuwar akwai ta fara'a ga son mutane haka muka wuce sai Gida
Bayan mun dawo Gida an gama gaishe gaishe sai ga mamie tazo gaida ta cikin sakin fuska da fara'a inna ta ansa gaisuwan ta daga nan ta koma ciki tunda ina tazo kullum ina wajena haka ma sauran yaran Gida mamie kan sauko kullum su gaisa daga nan ta kama hidimar gaban ta duk abunda ina ke so ni ke saws ayi mata sai Abba da kullum cikin tambayan me ake bukata yake yi yau haka nasa ina ta shirya na kaita saloon wanda ban gaya mata inda zamuje ba da kyar ta bari aka wanke kannan a cewarta sai dai ta wanke a Gida daga saloon gidan su rahama na kaita wajen mummy ai nan rahama tace wlh itama ta kusa dawowa gidan dan fulanci zata zo ta koya dan in muna tare takan yawan yi mun fulanci wanda har na saba ni kaina ina maidawa ba laifi
Haka suka sha hira da mummy bamu muka koma Gida ba sai can# please vote and comment is an encouragement thanks 🙏
YOU ARE READING
Hasken-taurari book 1
RomanceHighest Ranking A love story about fateema zahra from a fulani tribe she's the naive and innocent girl starting from the days of her college life with her best friend rahama who is the exact opposite of zahra, Imran a guy from a wealthy royal fami...