Chapter 27

6 2 0
                                    

Home coming
Imran POV :- shi kanshi smiling yayi tare da kwale shi saboda yau dole ya amayar da abunda ke cikin shi ko zai samu sauki cigaba da gaya mai yayi  ranar da ya fara ganin ta da Mahmoud ji yayi kaman zai mutu dan haushi aikuwa mai muktar zaiyi banda dariya har yana fadowa a kujera banza dashi imran yayi a cewar shi ya daina bashi labarin toh , haka dai muktar yayi ta lallaba shi har sai da ya gama jin komai hadda bincinke da imran yayi akan zahra wanda yasan yanda babanta ke ji da ita da yanda take da friends dinta even muktar is impressed dan abokinshi yau yayi mai bazata da ban mamaki
       Mummy's duk abunda suke fadi kaf a kunne ta hakanan ta tsinkanta da hawaye wanda ita kanta bata sanda sukayi ta fitowa ba lallai dan nata ya bata tausayi kuma tayi murna dan dai ba'anan gizo yake saka ba dan in har yarinyar bata son shi kuma kaman yadda akace ansa mata aure ya zama ba rabon shi bace bata san halin da zasu shiga baki daya ba nan take ta yanke shawara gobe gobe nan suma zasuje neman aure dan gara su gwada sa'a koh Allah zai sa adace
      Haka daren mummy batayi baccin kirki ba Allah Allah takeyi gari ya waye haka ta shirya sai wajen Aminiyar tata Maman muktar wanda koh karin safe basu yi ba bayan sun gaisa nan take gaya mata magana imran da zahra wanda ba karamin farin ciki ta nuna ba dan dama ta dadde tama yayan nata sha'awar aure zahra dan yadda ta dauki rahama da muktar haka take jin zahra kuma dan kwana kin da tayi a gidan bata ga alamun tana son Mahmoud dinba sai ma kawarta dake rawar kai akanshi bari sukayi sai da babansu muktar ya dawo sukayi magana iyayen maza suka yanke shawara zuwa gidan su zahra ganin abban nata
        Dawowar su kenan haka ta tarar da dan nata duk ba walwala duk da bai fito yace musu ga abunda ke damun shi ba daga ita har daddy wajen imran din suka tsaya suna ta dan janshi da hira har aka rage rana
Zahra POV yau ne yayi dai dai da ranar dawowar su gida Nigeria tunda suka tashi suke shirye shirye wanda jirgin su karfe 6pm dai dai ya sauka a kasa Nigeria
Imran shi kam baisan wainar da iyayenshi ke tonawa ba shi a dole bazai karaya ba muktar ne ya kirashi a waya inda yake gaya mai ya shirya zai raka shi wajen wani business partner  tashi yayi tare da wanka kanana kaya ne jikinshi so casual and simple dan his not in business mood today kawai baison ba abokin nashi kunya ne minti 30 sai ga waya muktar ne ke gaya mai yana waje fita yayi ya same shi suka kama hanya wani farin Gida sukaje wanda tsarin gidan yayi kyau sosai tunda daga wage kana gani kasan mai gidan ba mai son tarkace bane so simple and modern hatta yanda fulawowin waje suke a tsare gashi komai fari tun daga gate har fenti da sauran abubuwan gidan shiga sukayi ciki wanda mai gadi ya gaidasu cikin fara'a fallo muktar yayi gaba yana binshi a baya shi dai magana is not his thing amma when it comes to business he always has many ideas kujera suka samu suka zauna abubuwa sha da kayan ciye-ciye aka kawo magana yaji yana mamakin mai muryan da me ya kawota gidan rahama ce gaida su tayi ansa kawai yayi dan shi his confused muktar ne ya dan bata rai tare da tambaya ta ina zahra...??? Gabana ne ya fadi lallai muktar watau ni ya raina ma wayau kenan ban gama tunani ba akayi sallama that captivating voice that got me yearning for more and that her beautiful face da bana gajiya da gani zahrace ta shigo jallabiya ce jikinta sai mayafin abaya da ta rufe kanta dashi wani dadi naji har cikin raina na ganin ta kawai gaida mu tayi cikin ladabi muktar ne ya rigani ansawa harara shi nayi kafin nadan yi gyaran murya tare da ansawa fita zatayi muktar yace ai zahra yau wajen ki muka zo waje ta dawo ta samu nesa da mu tare da zama nan muktar ke cewa yaji anzo kawo gaisuwa amma baa sa rana ba eh ta bishi dashi cikin jin kunya nikam kallon yanda take ta wasa da yatsun hannu nata nikeyi wanda ba lallai ka gane hankalina yana kanta ba amma duk abunda akeyi ina sane dashi jin muktar na fadin muma munzo zahra in ba damuwa abokina imran na ciki bamu Sani ba ko zaa dace ai bansan sanda na kware ba ruwan dake aje tuntuni naki ko kallo ba aziki Na dauka na fara sha shi kam the bastard smiling kawai yakeyi kaman wanda yaci wata gasa
     Zahras pov dama tunda muka dawo sam banji dadi nidai gani kawai rahama ce ke gaya mun tayi waya da Yaya muktar zaizo Gida ni kaina nayi mamakin zuwan nashi dan in ba mummy ta aiko shi ba ko ya dawo da mu ba abunda ke kawo shi Gida amma sai na tsincin kaina cikin jin dadi addua nayi Allah yasa yazo da Yaya Imran ko da naje banyi tunani gani imran ba wanda ganishi kadai yasa na manta da rashin jin dadin da nikeyi bare da yaya muktar yayi mun magana duk da ba imran din bane da kanshi amma wani farin ciki naji ya lullube ni
Godiya nayi ma yaya muktar nan nike cemai na gode amma ko menene dole sai abunda abbah yace dan duk son da nike ma wani in abbah bai amince ba, dole in hakura inyi ma abbah biyayya muktar dinma godiya yayi tare da tashi barin fallon yayi daga ni sai imran haka muka zauna shiru wanda har ya bani haushi ko ba komai shi yazo gidan mu dan haka shi ya kamata yayi mun magana amma sai wani mulki mtsw gajiya nayi nima in rashin magana ne toh bismillah haka muka dauki lokaci wanda tun ina sake sake har na gaji dawowar Yaya muktar yasani jin dadi sallama nayi musu tare da shigewa ciki  ko kara kallon fallo banyi ba

Hasken-taurari book 1Where stories live. Discover now