Chapter 32

7 2 0
                                    


His coming back
Tun a Sweden duk abun da nagani sai inji ina son siyan ma zahra akwati daya nayi mata na kaya shima dan ina ma kaina fada saboda da jirgi wanda in a daa ne yar gift bag ma ya isa a mommy da dad koh in sa musu tsaraba su a kayana na tun ranar da na dawo naso zuwa gidan su zahra amma haka na daure saboda tsokana da mommy da muktar sukeyi sai washegari phone na dauka number muktar na kira da yazo ya rakani sai da ya gama tsokanan shi banza dashi nayi ganin zai sa mun ciwon kai yasa nayi ending call din can kuwa sai gashi muka tafi sai gidan su zahra Farouk ya tarbe mu hanya yayi mana alama da muje wani garden ne so simple zahra na hango ta dan kishingida saman swing dariya takeyi da alama tana jin dadin waje koh da wanda suke tare kanana kayana jikinta sun bala'in yi mata kyau yanda gashin kanta ke bouncing duk curls ba dankwali daga gani bata dade da zuwa gyara shi ba hakanan sai naji bansan muktar ya ganta haka am I jealous..???
Wanda kafin in ankara har ya fara gaida wata dattijuwa nima kaman yanda yayi haka nayi fulanci da naji ta mun yasani murmushi ina ansa ta sai a lokacin naga kaman ta da zahra dan koh ba fada ba yana yin jikin su da fuska sai dai wanan zaayi ce mata kakarta ce duk da ina yi ina kallon zahra tashin inna sunan da naji zahra ta kira ta dashi kenan shiga cikin Gida muktar ma sallama yayi mana wanda naji dadi haka kujera na jawo wanda na gani a nan wajen zahra nazo na zauna duk da nasan na dan jawo kujera kusa da yawa I know that am playing with fire but I can't help it , tsintar kaina nayi da kasa daina kallonta dan ta kara mun kyau sosai da kwarjini kuma after all wanan shine karo na farko da nayi mata kallon kusa maganar da nayi ta bitar ( practicing) 😂fada tun jiya na samu na fadi wanda ni kaina nayi ma kaina kama da mai koyon magana after na gama mata godiya da sakon mommy zuwa muktar yasa nayi mata sallama godiya tayi mun inda muka tafi feeling more alive shawara na yanke ma kaina na in dan dinga zuwa at least mun saba kafin lokacin biki yayi amma tunda muktar yayi mun rashin kirki cewa bai kara rakani nasan hanya boom shikenan sake komawa ya mun wuya duk da kullum son zahra karuwa a yakeyi a cikin zuciyata
- [ ] Shirin aure ya kankanma ba kama hanun yaro inda amare duk aka cika su da akwatuna komai dozen inna da kanta ta dage tana gyara jikar ta, irin gyaran su na fulani take mata wanda mommy su rahama ma tasa ana musu nasu ba wani event da yawa zasuyi ba Friends eve ne sai dinner sai kuwa su mommy da ta dage sai tayi Mother's Day, karon farko da baabar mamie a baya komai tana dan shiga wanda nasan ba komai bane illah Allah Allah da takeyi da inbar Gida duk da haka naji dadi koh ba komai baki zasu zo and there will feel at home, zasu samu sakewa ango imran tun zuwan shi amarya zahra bata kara sashi a ido ba, sai dai sabuwar wayarta kasancewar ya riga ya hadama ta komai kafin aka kawo yakan turo mata message duk da yawanci gaisuwa ne watarana da safe koh da daddare amma bai taba trying kira ba dan message din haka har ta saba dashi mom dinshi kuwa kullum sai munyi waya ya zama har mun saba sosai dan mace ce mai Jan mutum Ajiki kuma gaskia ta daukeni kamar diyar da ta haifa shiyasa wata rana nima sai in dan kira mu gaisa
- [ ] Yau biki saura sati biyu inda su baffa tsoho kyautar shanu hudu yayi ma abbah banda tarkace irin nasu na ruga su manshanu kwai zabi da dai sauransu wanda har gidansu rahama sai da aka kai ina zaune fallo wajen abbah yau saura sati daya biki munata hira can yake tsokana ta akan zaiyi rashin abokiyar hira har ya sani kwala kafin yayi ta tsokana ta da ba aziki sai da nayi dariya wayar tace ta fara ringing number imran na gani ciki da mamaki na bar fallon tare da dauka wayan gaisawa muka fara yi nan yake gaya mun yana wajen gidanmu mamaki shi kawai nike the nerve of this guy, toh da bannan fah maganan shi ya katse mun tunani yayi, inda yake tambayana in abbah nan abbah naje na gaya mawa university wanda cikin farin ciki yace maza aje a shigo dashi nidai gida na koma abuna tun bayan laasar har magrib suna tare bayan nayi sallah ina zauna banma tashi ba sai ga message dinshi cewar in sameshi a waje akwai sakon mommy sai anan ne nama san baitafi ba haryanzu veil nasama Kaina na fita samun shi nayi ya(sauke glass din window mota )looks totally wine-down kanshi na kan sit and his eyes close ( idon shi a rufe suke) har na ida isowa bai bude ido ba duk da nasan yana sane da zuwan nawa dan daurewa nayi na gaishe shi bude ido yayi tare da ansawa kaman mai jin bacci kin yadda mu hada ido nayi bude kofar yayi tare da zuwa boot din mota wata katuwar paper bag ya dauko mota shi ya sake budewa wata envelope ya dauko tare da sata cikin paper bag din alama yayi mun da in bishi ba ba musu gaba nayi yana bina har muka shiga cikin Gida sai da ya kaini dai dai main entrance ( kofar shiga cikin gida) jakar ya bani tare da mun sallama godiya nayi mai tare da shigawa ciki wajen ina na wuce straight inda hadda kanne mamana biyu dasu ka zo jakar na mika mata hararata tayi tace kaji yar nema toh ai sai ki bude ki ga menene ba wai ki mika mum jaka ba, budewa nayi wani material lace ne mai bala'in kyau black ya nada ratsin silver sai stones an riga an dinka shi daga gani zaimun daidai a jiki, sai dayan box din pandora products ne dan simple silver earring da sarkan shi hadda abun hannu( bracelet) takalmi da jaka suma a wani box din irin yar clutch bag din da amare kan rike lokacin biki adda ce ta sani gwadawa ita ke bi ma mamana dubai take zama da aure komai dai dai ni wanda nasan koh da aikin mommy toh hadda rahama wajen bada measurements da size kayan ba karamin karbana sukayi ba dayan envelope din kuma kudi ne bandir din dari biyar sababi sai kuma bandir din yan dari biyu sababi dan karamin note nagani an rubuta please manage this zahra iyayen nawa guda suka rangada wanda har yasani jin kunya sunata santi kayan
- A kwana a tashi yau ba wuya wajen Allah yau ake sa lalle kuma anjima Mother's Day baki duk sun hallara kowa sai sa albarka yakeyi venue da zaayi dinner nan aka kama ma Mother's Day wanda family su hada kansu dan tare zaayi ma amare su rahama ma an shirya anji kayan alfarma wanda aiki mommy ne haka ma zahra lifaya suka sa iri daya sai dai kowa da kallan nashi sunyi kyau sosai masha Allah iyaye da yan uwa da abokan arziki sai sa albarka sukeyi

Hasken-taurari book 1Where stories live. Discover now