Chapter 23

6 2 0
                                    

Getting better
Washegari haka na tashi jikina da sauki sosai tunda wuri nayi wanka na shirya dan bansan ana hidima kuma ni ina kwance dankwali nike daurawa wayar Mahmoud ya shigo dauka nayi muka gaisa inda yake mun ya jiki rahama na dalla ma harara tare da warning din zamu hadu ciwon da nace kar a gaya ma kowa shine duk taje ta gama broadcasting mtsw this my friend bayan mun gama waya a cewar shi shi zai kaimu dinner Allah ya kaimu nace nasan rahama ta bashi IV kuma ba dadi in disga shi
Yau ake kamu amma sam nace ban zuwa da mommy zan zauna wanda hakan ba karamin haushi ya ba rahama ba haka ta tafi tanata kumbura baki wai ita taji haushi gobe dai baki isa ki ki zuwa dinner ba Allah ya kaimu goben zamu gani ai da wanan ta fita ta barmu nan, kara faking ciwo nayi dan in tsaya da mommy to be on the safe side ni kaina kada inje ciwo ya dawo in rasa yanda zanyi mommy shigan mun tayi a cewarta ciwon ciki akwai takura message ne ya shigo wayana kaman haka " can't watch you getting sick speedy recovery fadimatu zahra'u". Shine abunda aka rubata a message din ( bazan iya ganin ki baki lafia ba ki warke da sauri fadimatu zahrau) number ba duba amma ba number mamaki nayi waye wanan da har yasan ban lafia kuma sakon duk da ya mun dadi amma sai yayi mun kama da na masu hacking account tunda haka yazo ba suna ba number sako kawai, haka nan kuma sai na barshi ba tare da goggewa ba , addua kawai nayi yauma baccina nasha dan yau na tashi tun asuba kuma ban koma ba
Yau aka daura aure Yaya muktar da amarya shi Hafsat yarinyar kirki mai son mutane ga natsuwa dole Yaya muktar ya like mata kowa san barka yakeyi anata guda da kade kade sam mummy ta hana kowa hawan sama kasancewar babban gida ne daga can kasa muke jiyo hayaniyar su sai kuwa masu aiki mommy da ta kan turo su wajen mu yau cikin ikon Allah na tashi garas kaman ba nice shekaran jiya ke juye juye a gado ba sai dai kodewar da fuska ta tayi wanka na shiga ina fitowa na tadda tray din abinci da magani a gefe wani kuka cikina yayi dan kwana biyun nan abincin ma bana iya ci wani dadi naji dan gaskia mummy ta daban ce tuwo ne miyan agushi sai sinasir da pepper chicken ga kunun aya mai sanyi yunwa da banma san inaji ba, tasowa nayi plate na dauka tare da sa abinci naci na koshi kafin na sha magani shirya wa nayi cikin sabon dinki mu amma is very light and comfortable tv na kuna food network ina kallon chopped rahama ce ta shigo inda tasa ni muka fita saloon can mukayi gyaran gashi da gyaran jiki bamu muka dawo ba sai wajen 8pm koh da muka dawo har an fara shirin zuwa dinner
Makeup artist na zauna simple make up nace ayi mun wanda ni kaina nasan na fito a zahra ta kasancewar ba African time da wuri muka shirya duk da muna fita har duk an tafi ba motoci daga masu aiki sai mai gadi dan turus nayi ina zare ido rahama ce ta jawoni muna fita waje sai ga motan Mahmoud duk da banson haka ba amma I have no other option yau Allah yasa yazo da abokin shi baya dukkanmu muka shiga inda rahama tayi directing dinsu muka wuce wagen event din
Imran's POV :- tun jiya danaga zahra duk na tsinci kaina bani da sukuni sam bana jin dadi tun magrib muktar ke damuna da in shirya da wuri jinshi kawai nikeyi kasancewar gidanmu nan muke zama duk da barin guest site din nikeyi in wuce main site dinna sai dai nakan dan shigo incase in suna da bukatar wani abu tunda koh ba komai nine host, kowa ya shirya da wuri banda ni, nine last hatta ango ya shirya fara tafiya wajen event akayi inda na bar ango da wani friend dinmu har friend din amarya suka so inje indauka hell no, ego na ma bazai barni motocin gida kawai muka kara gidansu muktar na wuce straight don't know why kawai zahra naji ina son dauka a mota amma me...???

- [ ]Ina waje nayi parking inata sake sake zahra naga ta fara fitowa da wanan rigimanman kawar ta, wani material lace ne yanda akayi dinki kanshi a bun kallo ne tayi kyau dan ko amarya a ganina ba abunda zata nuna mata kasancewar ina dan nesa dasu can nesa da gidan nayi parking, sai a lokacin hankalina ya kai ga motan dake wajen damn it that brat is still here his really getting on my nerve wani rage naji yazo mun wuya how comes ban lura da motan ba sai yanzu

Hasken-taurari book 1Where stories live. Discover now