Over the moon
Inna da kanta washegari ta samu baba inda tayi mai bayanin komai duk da hakan baiji dadin haka ba , amma ba yanda zaiyi zahra ce ake magana farin cikin ta yafi mai komai kuma tunda Allah ya hada Mahmoud da rahama alhamdulillah itama kamar ya ce a wajen shi addua ya bi da Allah yasa haka shi yafi alheri
Haka Alh Malik sabo da Alh tukur babba suka zauna inda suka yanke shawara sa bikin yayan nasu nan da wata uku masu zuwa date daya aka sa wanda hakan yayi ma yaran dadi sosai kasancewar sun shiga ajin karshe a makaranta tunda aka sa biki zahra bata kara jin ango nata ba tun abun na dan damun ta har ta cire a rai su rahama kuwa soyaya baa kama hannu yaro shi kanshi Mahmoud ba karanmin dadin canji da rayuwar shi tayi ba yake ji gaba daya ya watsa da komai jin rahama yake yi kaman ita kadaice tauraruwa ga rahama ta iya biyewa kullum suna nan manne da waya koh yazo gidan su, iyayen kansu abun na masu dadi duk weekend kuwa suna tare manne kaman cingam
Zahras POV :- Fanin su zahra kuma abbah kawaici kawai yakeyi abunka da fulani bai taba tambayan ta Imran ba koh maganar shi tunda suka gama magana da iyaye hakan ba karamin dadi yayi mata dan ita kanta duk abunda zai sa abbah ya tsareta da tambaya gudun shi take kasancewar bata da kwakwaran ansar bashi dining suka gama cin abinci Abba ne yace mamana zo nan dan tsiruru nayi kasancewar bansan me zai ce ba labarin imran naji yana ta bani wanda abun ba karamin mamaki ya bani ba nane naji ashe baya kassar yaje wani course na sati shida dan yake nayi inda abbah ke mun murna ya kusa dawowa da yake nayita bin Abba har muka gama hira shima kyaleni yayi a tunaninshi kunya ce ta hanani sakewa inyi magana bayan na koma daki ne nike tunani lalle ashe duk abunnan baya nan shine bazai iya kirana ya gaya mun ba raina ba karamin bacci yayi ba amma sai dai na danne dan bansan asan da wani abu,
Imran POV :- tunda mummy ta dawo daga gidansu Zahra ta kwashe duk yanda sukayi da ita ta gaya mun duk kunya ta isheni shikenan mummy taje ta gama tona mun asiri gaba daya a gaban yarinyar, banda yanda mukayi da muktar kan in dinga zuwa hira har mu saba amma ina mummy ta riga taje ta dana bomb duk da bansan mai zahra zata dauka ba amma zuciyata cike da fargaban rejecting offer na wani course nayi filling a Sweden wanda koh su daddy basu Sani ba cikin kwana biyu na wuce dan zafin da kaina keyi I really need a break
Tun zuwa na maida hankali kan abunda ya kawo ni dan na gama yanke shawara in har Allah baiyi zahra matata bace toh kawai nan zanyi settling dan bazan dawo Nigeria ba sai sanda Allah yayi tunda safe muktar ke damuna da waya ganin tarin miss calls dinshi yasani tsoron dauka dan bansan me zanji ba sai can daga baya nace bari in kira shi nayi cikin fargaba bugun farko ya dauka yana fada haba maza na kira inyi ma albishir amma shiru tunani na farayi wane albishir din ganin ban gane ba yace mun guess what hadda rai nayi kaman ya gani nace spits it out dan dariya yayi yace Baka da hakuri dadi na da kai banza dashi nayi magana da ya gaya munne naji kaman a mafarki sai da na dan cire phone din dan in tabbatar da gaskia hakan wai ni imran aka bar zahra wani farin cikin da bai misaltuwa naji wanda shi kanshi muktar din murna yake taya ni
Toilet na shiga nayi alwala na daura nafila ina gode ma Allah da wanan kyakyawar kyauta da yayi mun baccin da naka yi kenan ranar kamil na kira one of our escort da nasa ya taba mun bincike akan zahra sa shi nayi ya dinga binta yana daukar ta hoto yana turo mun though I sound like a stalker amma I don't give a damn most of her pictures da ya turo na makaranta she's looking as gorgeous as ever, su suka zama mun abun kallo kullum dan yanzu I have her own collection of pictures zaman Sweden gaba daya ya isheni Allah Allah nikeyi mu gama course dinnan in dawo gida koh dan inga
YOU ARE READING
Hasken-taurari book 1
RomanceHighest Ranking A love story about fateema zahra from a fulani tribe she's the naive and innocent girl starting from the days of her college life with her best friend rahama who is the exact opposite of zahra, Imran a guy from a wealthy royal fami...