Acting like a lost puppy
Imran POV:- Haka na kasance kusan rabin zamana a gidansu muktar ne kuma ba dan komai ba sai dan inga zahra har muktar ya fara dagoni amma kiri kiri nayi denaying kwaleni kawai yayi yace in tayi tsami ai munji, Zahra:- haka zamana ya kasancewar gida mummy cikin jin daddi da walwala dan gaskia mummy na kula damu sosai shirye shirye biki ya kankama abba ba dan yaso ba dole ya bani muka ci gaba da shirye shiryen mu dan yanzu haka na tattaro kayana na dawo Gida
Abun mamaki shine imran kullum sai ya shigo gidan nan har kamar yasan lokacin dawowar mu daga makaranta wata rana mu ganshi a waje watara mu ganshi a cikin gida tuni na gane imran ya fara jin sona saboda nasha kamashi yana kallona amma yayi kaman bashi ba sai dai tsabar girman kanshi da miskilanci shi yaki bari ya yadda da haka
Shigowar mu kenan mun dawo daga makaranta kasancewar ni na kaimu yau imran ne a ciki saman kujeru irin na shan iska nan gaida shi mukayi kafin muka wuce ciki rahama ce ta zunguro ni cewar anya sist yaya imran bai kamu da sonki ba kuwa dariya kawai nadan yi mata kara tabo ni tayi wai Toh inje mudanyi hira mana harara na dallah mata saboda nice karshen marar kunya mutumin da ko cewa yana sona baiyi ba kuma zan iya zuwa ya disga ni ma sai nice zanje wajenshi rahama ce tace hakane fah zaka iya zuwa ya halin rashin mutunci shi rabu dashi shi kawai haka muka muce amma har a cikin raina how I wish ace imran da gaske zaice yana sona his just the perfect piece of art
- Bayan munyi sallah wayata ce ke ta ringing Mahmoud ne rahama nasa ta dauka cewa yayi zaizo wanda already rahama ta gaya mai inda muke ta dadde da cemun ya zo amma haka nayi ta bata lokaci sai can na jata tana bata zuwa wai kullum haka nikeyi sai in barsu su biyu suyita magana da kyar dai na jata muka je
- An aje mai lemo da snacks nan muka gaisa tambayan mu yakeyi akan school muna bashi ansa karar tahowa mukaji da yake fallon farko muka sauke shi rahama guduwa ciki tayi ta barni da shi yaya muktar ne da imran suka shigo wanda dole in zasu wuce side dinsu sai sun bi ta fallo gaba daya Imran ya daure fuska kana ganshi kasan mood dinshi na yau bana wasa bane gaida su nayi wanda muktar ne kawai ya ansa hannu mahmoud ya ba shi suka gaisa wanda kafin ya ba Imran shi har ya wuce ciki what's wrong with this guy...??? Shine tambayan da yayi mun ni kaina bani da ansa wanan
Muktar shigar su kenan ya dauki waya rahama ya kira cewar duk abunda takeyi taje fallo wajen zahra ta taya su hira zunburo baki abunda bai taba mata ba toh inama ruwanshi mummy ta gayamawa nan take dariya tare da cewa kedai jeki abokinshi yake tayawa kishi haka dole na tashi na tafi duk daga Yaya muktar din har imran din haushi su nike ji haka nan su dami rayuwar mutum mtsw
- Ina tafiya ina tunani maganar mummy watau Yaya Imran da gaske killa son zahra yake tsaki kuma nayi wanan mutumin wa ma zai iya da halinshi ya tsaya nan yana bata lokacin muka samu wani da take so sai dai yaji a salansa fallo na shigo kaman an dauke wuta ba wani abun kirki tsokansu nayi tayi ina dan jansu da hira har kowa ya saki jiki munata hira imran yazo tafiya sallama mukayi ba wanda ya share mu gaba daya kaman ba dashi ake ba haka ya wuce bayan tafiyan shine Mahmoud ma yayi mana sallama sannan muka shiga ciki
- Shigar mu kenan sai ga mai gadi yazo da leda biyu yace inji Mahmoud haka mukayi godiya tsarabar South Africa 🇿🇦 koh me guda biyu ya siya kuma iri daya hakan ba karamin dadi yayi mu ita kanta rahama taji dadin haka hadda mummy sai dai lura da nayi mummy kaman bata son taraya ta da Mahmoud
YOU ARE READING
Hasken-taurari book 1
RomanceHighest Ranking A love story about fateema zahra from a fulani tribe she's the naive and innocent girl starting from the days of her college life with her best friend rahama who is the exact opposite of zahra, Imran a guy from a wealthy royal fami...