Chapter 28

6 2 0
                                    

Meeting his mum
Zahra POV fita ta kenan naji dawowar abbah da sauri naje ba tare shi tare da karban abun hanun shi jawoni yayi fallo muna ta hira ina dariya sam nama manta da bakin ciki basu kai ga tafiya ba abbah ne ke cewa aah mamana ashe baki mukayi a gidan sai lokaci ne na tuna dasu kasa suka sauka gaba daya tare da gaida abbah cikin girmamawa ansa yayi ni dai ciki nayi na barsu nan
Bayan tafiya sune Abbah yasa akayi kirana abinci yasa na kawo mishi nan yake tambaya na mamana wani yaro Yaya ku muktar ya kawo akan magana ki, kowa yazo sai nayi bincike a kanshi kuma kinsan mun riga mu karbi maganar Mahmoud kada mu zama masu magana biyu shiyasa su muktar din ma na saida musu da maganar wani a kanki saboda haka bazanyi musu alkwari komai ba sai dai godiya da nayi musu nidai tunda Abba ya fara magana kaina kasa yake har ya gama amma duk sai naji ba dadi har shima abban yaso ya gane wani abu, mamana dafatan dai ba wata matsala dan yake karfin halin nayi nace mai babu komai Abbah albarka ya shi mun tashi nayi na koma ciki
      Daddyn imran da na muktar bayan sun gama yanke shawara zuwan wajen abbah zahra waya sukayi inda sukayi zasu sameji ranar juma'a da yamma haka kuwa akaiyi Maman imran ma ba barta a baya ba ita da aminiyar ta Maman rahama dan ta fi kowa son ganin wanan yar tasu da har tasa dan nata rikicewa haka
Fallo maza suka zauna inda su kuma suka shiga ciki wajen inna aka kai su nan akaiyi ta kwasar gaisuwa abunka da fulani yaga dan uwa ai  tuni Maman Imran da inna aka canza harshe su mummy sai dai suka zama yan kallo ana haka sai ga su zahra da rahama sun dawo islamiyya ana rige-rigen zuwa wajen inna suna shiga sai ga baki sukayi turus gaishesu sukayi inda mummy su rahama tace toh yan nema ga mamanku nan na kawo muku yau sai kuzo ku gaidata nan kuwa suka kara gaida Maman Imran zahra ce mai saurin fita inda Maman Imran ta tsaida ta dacewa zahra wajen ki nazo yau fah zaro ido tayi cikin jin kunya tace toh nan take cewa inba komai magana nike son muyi ita dai zahra duk kunya ta gama cika ta dakin ta suka je inda mummy ta samu guri ta zauna wanan shine ganin ta da zahra na farko amma tuni taji yarinyar ta shiga rainta saboda yanda yarinya ke komai ma abun burgewa ne a natse ga girmama na gaba dole dan nata ya kyasa
       Kasan carpet zahra ta samu waje ta zauna wanda ba yanda mummy batayi da ita ta zauna kan kujera ba taki magana ta fara mata zahra na dadde da yi ma Dana fatan samu mata irin ki mai adding,ilimi, mai kunya ga tarbiyya kaman ki sai gashi lokaci daya shi da kanshi imran ya rike saboda ke kaina kasa yake amma sai da tasa na dago kai na kalleta dan murmushi tayi irin na manya tace sanin kanki ne ba yanda zaayi muyi mai auren dole ba tare da yadda shi ba amma abun mamaki tun ranar da yaje gidansu muktar yaji labarin aurenki gaba daya ya rikece mana wanda har sai da ya kwanta asibiti kila ke da kanki kin san imran akwai shi da zurfi ciki kuma tunda nike dashi ban taba ganin ya damu da wata ba bare har ya tadda hankali akai sai ke shiyasa nazo in rokeki dan Allah a taimake shi zahra ki yadda ki auri imran na miki alkwari bazaki taba da na Sani ba da ikon Allah kuma in har kuka saba sai kinyi mamakin shi his very caring
Nidai har ta gama magana ta haka na rasa dadi zanji ko haushi zanji abu daya da nasan bai mun dadi ba shine ciwon imran sai naji duk ba dadi albarka ta samun tare da cewa sai ta jini sallama mukayi dan zasu tafi ni duk nauyi ta ne ya gama cikani ita kuwa rahama kaman jira take su tafi hadda rawa wai Yau mummy imran da kanta tazo wajen zahra hadda su guda sai da na fita na ban mata dakin can wajen inna naje na rakube ina ta tunani kala kala

Hasken-taurari book 1Where stories live. Discover now