The talking
A fallo na samu Mahmoud gaisawa mukayi inda na samu guri can nesa dashi na zauna hakuri ya fara bani akan abunda ya faru jiya a cewar shi sunyi magana da babanshi har yace yana son a bamu lokaci tunda dukka dukka bamu gama fahimtar junna ba amma sam yace ba haka dan da zafi-zafi akan buji karfe kada aje a haifo da mai ido daya
Ko da aka zo gaisuwa shi bai Sani tsakaninsu ne shi da Abba sai kuwa da daddare shima yake yi duk yanda naga ya damu yasa nadan yi mai yake nace mai ba komai ai iyaye ne kuma suna da hakin yin abunda suka ga ya dace dan ajiyar zuciya yayi kafin nace ni kuwa akwai tambayan da nike so inyi maka
Bismillah yace mun ba damuwa tambayan shi nayi yanda suke da yasmin kasa yayi da kai sai da yayi shiru na dan wani lokaci kafin ya fara magana cewa dama koh nan tambayashi ba yayi niyar zai gaya mun komai kafin ayi building wani relationship labarin rayuwar su shi da yasmin ya bani bai boye mun komai da dalilin da yasa ya barta
Da kuma tunda Allah yasa yazo gidanan zuwan farko yaji ya tsani duk wasu halayen bazan da abunda yayi abaya ya daukan ma kanshi alkwari zaiyi iya kokarinshi wajen gani ya bar halaya shi nan yake gaya mun addua kawai yake so in taya shi dashi kuma maganan aure shi bazai mun dole ba zai bani iya lokacin da naga dama Allah ya zaba mana abunda yafi alheri ameen sallama mukayi na koma cikin Gida
Maganganu Mahmoud sun tsaya mun a rai lallai rayuwa bawa ya kaleta kawai kuma ba iyawar mutum bane da kame war sa kawai shiriya ce da tsarewa na ubangiji shiysa a kullum a koda yaushe neman tsari da addua akan Allah ya shirya mana zuria ba karamin abu bane koh ba komai yanda Mahmoud bai boye mun komai ba abun yayi mun dadi kuma ya burgeni saboda it took lot of courage for someone to accept his mistakes ( ba karamin mutum bane zaiyi laifi kuma ya yadda ya ansa wanan laifi) duk wanan bai sa na ji ina son shi ba amma kuma nan kyamace shi dan jarabace shi tashi jarabawar kenan Allah ya bashi ikon fin karfin zuciyar shi ameen
Bikin Yaya muktar yaa kankanma wanda in ka gani ni da rahama ka rantse cewar mune amaren kullum bamu kasuwa ba mu Gida ga gyaran jiki munyi musanman mommy ta siyo mana kayayaki na sakawa masu dan karen kyau da tsada kathy Antony muka ba dinkuna mu baki daya wanda akaiyi mana na gani na fada kaman an zana shi a jikin mu mai kwalliya kuwa musanman muka daukota har a gama biki Home sick
- Zahra's POV :- event din farko bridal shower akayi rashin sa'a na tashi da wani irin ciwon ciki duk da ni ba gwanar mestural pain bace amma wannan karan sai gashi yazo mun wanda gaba daya na kasa sukuni dole nasha magani na kwanta event din da banje ba kenan na ranar
- Imran yau kusan wata daya har da sati rabon da inga zahra kasancewar tafiyar da nayi nayi tunani distance zai sa in manta yarinyan nan in dawo my old self amma hell no the distance hurt like a bitch kullum kana cikin tunani kala-kala ban yadda ina sonta ba ma sai da bana kasar dinkuna na mussanma nasa akayi mun dan kawai in burgeta wanda tunda nikeyi ina yin dressing din da naga dama ne kawai amma this time I use extra effort poor me 😃
Yau kwanana biyu da dawowa dan aure my best man dole ina nan tunda na dawo nike son ganin zahra amma kasancewar gidan su yanzu a cike yake dole na hakura dan ni ba mai son hayaniya bane nasan shiga ciki is not my thing wayar muktar ne ya shigo inda yace in fito mu wuce kaman ince ban zuwa amma muktar ne dole inyi mai kara dropping dinshi wani abokin mu yayi da mota ta na dauke su shi da amarya wanda ina gaba suna baya amma ko a jikina ban damu dan insan ma abunda suke yi ba nidai driving kawai nike muje ko nadan ga zahra
Haka event anata activities yan mata masu rawa nayi masu hotuna nayi wanda nike son gani bata ba dalilinta har rahama na gani yafi sau biyu muktar ne ma naji yana tambayan rahama ina zahra bai ganta ba koh hoto bata zo akayi ba anan ne take cemai ai yau zahra bata lafia duk sai naji ba dadi
Bayan an tashi mun maida amarya muktar bai bata mun lokaci ba kuma naji dadin haka har ya dago ni dan zunguroni yayi yace ance dai ba wani ciwo bane kuma tasha magani dalla mai harara nayi gidansu muka wuce kasancewar dare yayi sosai yawanci mutane sunyi bacci sama muka hau har dakin rahama nidai bin muktar kawai nikeyi dai dai kofar ya tsaya dan knocking mukayi amma shiru tura kofar nayi zahra ce kwance tana bacci fuskanta sai kwali yakeyi ta kara haske sai dan yatsina dake fuskan ta da alama haryanzu bata jin dadi bansan sanda kafafuwana suka kaini har wajenta ba goshinta na taba ba zafi sai hannun ta da na kura ta dafa marar ta da alama nan ke mata ciwo wani abu naji duk ba dadi duk tausayinta ya kamani remote din AC na dauka tare da rage mata dan dakin yayi sanyi sosai bargo naja na rufa mata tare da kashe wuta muktar bina kawai yake da kallo tare da mamaki kafin muka bar dakin sallama nayi mai na wuce Gida duk jikina ba kauri ranar da tunanin zahra na kwana
YOU ARE READING
Hasken-taurari book 1
RomanceHighest Ranking A love story about fateema zahra from a fulani tribe she's the naive and innocent girl starting from the days of her college life with her best friend rahama who is the exact opposite of zahra, Imran a guy from a wealthy royal fami...