*_NERNER AYSHER_*
By
Mrs bb
Mom muhseen.Wattpad name
Humaira3461🅿️......1
Sunana nerner Aysher Abbakar sadiq an haifeni agarin Kano unguwar nasarawa,mahaifina babban dan kasuwane mai suna Alh Abbakar sadiq mai atamfah wannan shine inkiyarsa,duk inda ka fadi sunan *Alh Abbakar mai atamfa* to kuwa tsaf za'a kawoka har kofar gidanmu.
Mahaifina su biyu ne maza shida kanensa Abba sufyan,sai kanwarsu goggo sabira wadda itace suke uwa daya uba daya da Abba sufyan,shi Abbuna mahaifiyarsa shikadai ta haifa. Allah yasaka ma dukiyarsa albarka,ta ko ina Abbu arxikinsa bunk'asa yake,tun yana sarin atamfofi yana kaiwa garuruw,da kasuwanni.
Har takai ga Abbu ya bude katafaren company Atamfa anan cikin garin kano,wanda ya dauki ma'aikata masu dama don karfafa company,gaskiya Abbu yasamu kudi koma ince yana kan samu,don yanxun haka yana kokarin bude wata masana'antarsa ta sumunti.
Ga kuma canjin kudi da yakeyi kowan irin kudi na kasash kakeson canji abbu yanayi,kudi ke shigo masa ta ko ina nikaina bazan iya fadar adadin dukiyar abbu ba.
Abbuna mutum ne mai tsananin alkairi abun hannunsa bai rufe masa idoba,inhar kana tare dashi to zaka ringa samu alkairai kala daban daban,duk wanda ya sansa yasansa da alkairi. Duk yadda Abba sufyan yake jin zafin abbu,yake nuna masa hassada da kyashi hakan bai hana ya sanya sa cikin dukiyar sa ba dumu dumu,haka goggo sabira duk wata Abbu ya yankar mata albashi yana bata.
Hakika Abbu mutumen kirkine badan yana mahaifina ba,aa ita gaskiya duk inda take fad'arta ake.Acikin gidanmu dai mace d'aya ce matar Abbu itace mami,asalin sunanta kuma rashida.
Mami rashida itace mata ta biyu waje abbu wadda ya aura bayan rasuwar mahaifiyata mai suna Nanah Aisha.
Nikadai ta haifa kuma naci sunanta,saboda son da Abbuna yake mata.ta rasu inada wata tara aduniya,sai rik'ona ya koma hannun yan reno saida Abbu yayi shekara daya da rabi bai sake aure ba,daga baya aka ishesa da surutu kafin ya auri yar uwar mahaifiyata da suke abokan wasa,auren mami yasa rik'ona ya dawo hannunta.saidai duk da haka Abbu gani yake batayin kokari wajen kulawa dani,nima saina ke kin yarda dan ita,karshe dai sashen Abbu na koma shine komina shine wankana shirin makarantana,ya bani abinci ga baki ya kuma kaini makaranta da kansa,hakan da yake yana matukar bata ran mami amman ko kusa bata nuna hakan ba,tunda Allah ya gani tana bakin kokarinta.ai koda badan diyar yar uwarta bace zata kula dani ganin marainiyace banda uwa,ita Allah baisa tana da zuciyar cutar dawani ba mezai sa ta cutar da yar yar uwarta.
Abbu yana matukar sona komi nakeso duk kudinsa duk wuyarsa saiya samo munshi,ya shagwabani fiye da jaririn da yazo duniya,haka baya barin duk abunda zai sani kuka.
Abbu shine duk wani farin cikina aduniya shine nake gani nakejin dadi,ban dauki mami abakin komi ba banda yar aiki.
Kwata kwata bana mata kallon wata mai muhimmanci acikin gidan,saboda dai shi kansa abbun bata ita yake ba.
Ko dawowa yayi daga wajen aiki nice abokiyar hirarsa,iyakarta ta hada masa ruwa yayi wanka takuma yi saving dinsa abinci,ko kwana tare bana bari suyi saboda yarinta ko ince kishi,saboda tun ina yar mitsitsiyata nakeda tsananin kishi tabbas nayarda da akace duk masu suna Aisha kishin tsiyane dasu.
To haka nake ina taya mamana kishi sai yamun wayau yakaini dakina har nayi bacci kozai samu keb'ewa da mami,baiwar Allah bata fushi kullin cikin yimasa uxiri take.Ahaka na fara girma ina kara wayau kuma girman kaina yana karuwa,saboda Allah yasa inada wani hali marar kyau watau ban dauki talaka mutum ba,gaka bana daraja mutane duk girmanka.
Sannan ba wanda ya isa ya bani umurni bacin mahaifina,shikadai ne mutum mai mutunci ga idona.
Shine nake rusuna kaina gabansa,bacin shi babu wani da nakejin tsoronsa ko nake jin shakkarsa ko yabani umurni nabi,wadannan sune munanan halayena dasuka kai ni ga dana sani.Inda shekara biyar mami ta haifi kanwata safiyya,hakika bayan Mama na data rasu sai Abbu babu abunda naji ina masifar so sama da safiyya,wata irin kauna nake ma yar uwata,har hakan yaba mami mamaki saboda batai tunanin zan so jininta ba saboda ganin kamar na tsaneta.
Ni ban tsani mami ba kawai dai har yanxu ban dauketa matsayin uwata bane,ina ganin batakai darajar mamana ba,sau dayawa Abbu zai nuna mani cewar na shaku da mami itace kamar mahaifiyata,idan nafara masa kuka har sai kansa yayi ciwo saboda wannan maganar,daya gane hakan sai yadaina yimun.
Yace yana fatan wataran zan gane hakan,nikuma ince babu rana.
Safiyya nada shekara biyar ita kuma mami ta sake haihuwa,wannan karon d'a namiji ta haifa mai kama da Abbu sak,wannan yasa na karajin soyayyar Abdulrahman sunan da na zaba masa kenan.Rayuwar gidan mu ba laifi gwanin sha'awa nida kannena,nizam tasasu gaba mutai makaranta.
Tunda suka shiga makaranta na hana Abbu yana kaini,nace tare da kannena zan ringa tafiya hakan ba karami dadi yayi masa ba.
Shakuwa ta shiga tsakaninmu sosai suna sona ina sonsu,har abinci sai ince ma mamin su ta had'a mana.
Don ban tab'a kiranta da mamina ba,ko magana zan mata inta zama dole zance mamin sofy kaza da kaza.
Ni ala dole ba mamin bace ba.Kash inata surutu ban gaya maku suffataba
Da fari ni fara ce amman ba fari irin na sosai din nan ba,amman tabbas daka kallan zaka tabbatar ni fara ce.kuma inda hanci sosai kuma siriri irin na mamana,bakina dan daidai shibai karami ba haka bai cika girma.inada cikar gira sannan ina da yawaitar gashin jiki watau galgasa,amman akaina babu gashi sosai don kalar gashin su Abbu na dauko,bawai kwaikwaido garan ba yana fakin amman bai kawo kafad'ata ba.Abbu yace dana biyo mama danai gashi sosao don gashinta har tsakiyar bayanta yake.
Inda dumful guda biyu left and right,sune suka kawata fuskata ainun,koda banyi murmushi ba ko dariya,magana ma idan inayi gasunan abun sha'awa friends dina suyita tsokata da cewar pointed beauty,banda kiba amman inada cikar hallitta sosai,hakan kesa aga kamar inda yar kibar.
Don bombom dina cike suke sun fidda shaf din hips dina masha Allah,haka boobs dina suma zaka rantse na wata katuwar mata ne,duk da ba jibga jibga bane amman tubarkallah.
Ba yadda Abbu bai dani akan na ringa saka hijab ba nace Allah ya kyauta saikace wata kidahuma,wlh bazan saka wata hijab ba.
Yace "to kuwa saidai ki daina saka riga da siket ko riga da wando English wears kina fita,dole ki suturta jikinki,beauty na ko kinfison Allah ya konaki nima ya konani?"
Girgiza kai nayi ina turo bakina mai kyau murmushi yayi yace "to kiyi hkr kinjiko,Allah baya son fidda tsiraici haramune kin sani kuma.inhar bazaki saka hijabi ba to kitabbatar kin rufe jikinki yadda wani namiji nazai ji kindauki halhakinsa ba,ba kyau anjima kishirya keda sofiyya sai kushiga kasuwa kusiyo duk abunda bakuda shi,kinjiko nernerh ta."
Na d'aga kaina ina mik'ewa zan tafi yakirani "zonan nernerh"Dawowa nai yace "fushi kike da babanki,nine fa abbunki,meyasa don nagaya maki gaskiya kike fushi."
Rausayar dakai tayi tana jan yan yan yatsunta tace "Aa Abbu bana fushi dakai kayi hkr"
Yace "ok smile inga wannan point din mai kara maki kyau."
Ban san sadda na saki murmushin ba ina shagwabe wa nace "kai Abbu."
Dariya yayi yace "yawwa yar gidana ko kefa,kiduba wayarki nai maki alert kamar nawa kikeso."
Na yamutsa fuska nace "Abbu nidai kaga dole zan sake zubin kayana tunda ka hana saka wadanda zasu fidda tsiraici ko,don haka gaskiya saidai ka zuba mana 1 million."
Murmushi yayi yace "ta isa ko akwai kari" nace "aa its ok hakan shima don zan canza kayan wadrop dina da mezan da kudi har haka,kasan bana kashe kudi sosai ko."
Murmushin yake sosai don ita nan wai wayau gareta,yace "haka ne nasan baki kashe kudi sai yar sofy ta wannan"
Dariya sukai baki daya saboda dai tasan sofyn bai wuce ta kashe ten k akasuwar ba.
Nace "to sauran na sofyn Abbu."
Yace "kirata ta fad'a da kanta zaifi."
Na turbune fuska nace "au baka yarda dani ba kenan,shikenan kirata d'in"
Na juyar da fuska girgiza kai kawai yayi yace "shikenan nawa takeso ita kiyi mata counting"
Murmushi nake ina kalon sa kasa kasa dariya yake yace "ina jinki fita zanyi fah"
Nace "ita abata 500k ai zai isheta ko."
Bai musa ba yace "duk zan transfer ta acc dinki,amman ku dawo da wuri kinsan zaki wuce makaranta gobe kuma baki shirya komi ba,sannan karki sake kifita da mota tunda ba kwarewa kikai ba. *mus'ab* driver na yana nan kuce ya kaiku."Ba dan raina yaso ba nafito,saboda dai wannan d'an rainin hankalin driver nasa banda girman kai bai iya tsiyar komi ba,shiba wani shege ba sai girman kai saikace dan gidan masu kudi.............bangaren su sofy na wuce na samu mamin a falo.
Fuskata ba walwala na gaidata ciki ciki "mamin sofy ina wuni,sofy ta shirya yanxu zamuje kasuwa inji Abbu."Murmushi tayi mun tace "to Nernerh tana dakinta wanka take ki isa kigaya mata mana"
Nai hanyar waje ina cewa "inbaki gaya mata kibari."
Na fice na barta nan na wuce nawa d'akin son na shiya.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...