part 37

144 16 1
                                    

*_NANAH AYSHA_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........37

Still har sannan ban iya ce masa komi ba hannayena dake bayansa da na k'ank'amesa dasu na sakesa ina son na raba jikina da nasa na fara janye fuskata daga tashi kafin nai nasarar janyewar daga garesa baki d'aya na juya na koma can karshen gado na zauna,inajin yadda gabana yake fad'uwa amman hakan bai hana ni tuno dukkan kalaman sa na d'axun amota ba,biyoni yayi inda na zauna na tattare k'afafuna wuri guda sannan na saka fuskata cikin cinyoyina nai tsit kamar ruwa ya cini.
Durk'ushinsa naji a wurin yana ta jan numfashi daker daker hannunsa daya d'ora gefen fuskata yaja naji yadda jikinsa yake k'ara d'aukar zafi naji yana magana ahankali kamar zai kuka "ina jin haushin kaina fiye da kima saboda nayi silar saki cikin k'unci,don Allah Aysha na kar kiyi fushi da yawa dani kinji I'm sorry"
Wani iri nakeji saboda yadda muryarsa take fita silently cike da soyayya yake saka kasala tana rufeni,amman ban motsa ba balle nace masa wani abu.
Wayarsa aka kira ya zaro ya duba sunan yaga faisal ne ya k'araso sai ya maida wayar aljihu yace "zan tafi cutie ba zaki ce mun komi ba."
Nan ma nai banza na kyalesa aganina wlh wannan k'adai bai isa ba ni so nake naga hawaye cikin idonsa,haka zaifi tabbatar mun da cewar bazai iya cigaba da rayuwa mai dadi ba muddin babu ni,kuma bayan ni bazai iya kula kowa ba.
Tashi yayi yana d'ago fuskata sosai ya sunkuyo ya sunbaci goshina na lumshe idona shima idon yayi masa,na turo baki sai kawai naji ya dora mun nashi bakin cikin wani yana yi mai tsayawa arai yai magana bakin yana nan inda yake yace "I love u cutie,and I want be with u forever and ever,good night love"
Ya sakar mun wani zazzafar light kiss da saida na sauke wata gauruwar ajiyar zuciya,sannan akasalance ya juya ya fita daga d'akin yana jamun kofar ahankali.
Fad'a wa nai kan gadon nace da d'an karfi "wayyo Allah na wallahi zai illata mun zuciya"
Filo na jawo na k'an k'ame ajikina yana sauke ajiyar zuciya,idona rufe nake tariyo duk abunda ya wakana tun daga dadad'en kalamansa masu shiga rai da zuciya,har zuwa kan zafafan kisses d'insa da suke kwance mun kaina na nemi dukkan natsuwata na rasa,na ji ko ina na jikina ya anasar su.
Wani munafukin murmushi na saki nace "tun yanxu har ka susuce?kofa kwana d'aya ba ai ba!uhmmm zaka gane ne"

Yana fitowa yaga su mami har sun kashe komi sun tafi su kwanta,can wurin get ya wuce ya gansa zaune saman teburin shazali yana isa ya bashi hannu suka gaisa ya kallesa yace "baka lafiya mus'ab"
Lumshe idonsa yayi y abude yace "muje daki na"
Bai musa ba ya tashi suka nufo dakin mus'ab d'in ruwan da zainan ta kawo masa da abincin yai mata tayi,aiko daman yunwa yakeji ya zauna yaci yai hani'an yasha ruwan da lemun sannan ya maido hankalinsa kan abokin nashi.

"Ina jinka me yake faruwa ne?"

Kanshi da fuskarsa yake shafawa yafara magana cikin kasala "faisal ban san dame zan fara maka bayani ba,hkr zan fara baka ko sanar dakai dalilin kiran shine ban sani ba,saboda ina jin kunyarka data baba."

Murmushi faisal yayi yace "koma ta inane nidai ka gaya mun ai kasan zan fahimceka ko?"
Ya gyad'a kai sannan cikin damuwa yace "faisal da fari nayi tunanin zan yi adalci tsakanin Aysha da hafsat idan na auresu,tunda k'addarar Aure ta riga ta had'ani da Aysha naji inason na Auri hafsat ban san abun zaizo mun ahaka ba,sai gani dumu dumu cikin kaunar yarinyar nan!faisal tunda na sanar da Aysha batun auren nan ta tashi hankalina ta kuma tashi nata hankalin,sannan ita kanta mami ta goyi bayan abunda take ban zaci zan shiga halin da nake ciki ba saida naga dagaske ta watsar dani,kuma ashirye take data juyama soyayyata baya harfa cewa tayi bata sona bata kaunar aurenmu bata buk'atar xama dani,faisal wlh ko Auren hafsat nayi nasan wataran saina cuceta bazan yi mata adalcin da ake bukatar mai mata biyu yayi ba,inajin wanan tsoron saboda ayau na tabbatar ba karamin so nakewa Aysha ba,saboda yini guda na gigice na fita hayyacina,yanxu haka jinake kamar masassara nake,kaina kamar zai fashe haka nakeji.ga hafsat na ta kirana na kasa d'auka saboda ban san abunda zance mata ba,tausayinta nakeji don Allah ka bani mafita wlh ina cikin damuwa."

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now