*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........46
*ABUJA*
Tun bayan sasantawarta da fafa sai gabaki d'ayan hankalinta ya kasa kwanciya,babu second din da zai buga ba tare da tunanin gudan jininta ba,tunda ya sanar da ita kullin yana mak'ale cikin ranta tana suffanta yadda ya koma shin ya kamanninsa suke?da wa yake kama ita ko fafa?har tasleem take tambayarta "ummi kamar bakida lfy meyene yake damunki don Allah"
Murmushi ummin tayi tace "bby Allah ne ya cika mun burina na tsawon shekara ashirin da tara"
Xaro idonta tayi da mamaki duk da kasancewarta yarinya amman kwalwarta da tunaninta irin na manya ne tace "ummi tsawon shekara ashirin da tara kinda dakon sa?ummina menene wannan don Allah?"
Shafa kanta take cikin soyayyar yarinyar tace "bby bayan ke ina da wani d'an,kafin na auri babanki nayi wani aure na haifi brother naki,wani dalili yasa bai tashi tare damu ba,ya b'ace b'at tsawon shekarun nan,to shine fa kwana nan akace anganoshi yana kano."
Ai yadda taga bby tana murna abun ya bata mamaki tsalle take tana dariya da farin ciki tace"ummi I'm so happy wlh don Allah ummi ki shirya muje wurinsa na k'agara na ganshi,ashe nima ina da brother su anwar zasu daina mun gori."
Murmushi ummin take tana jawota cikin jikinta tana rungumeta cike da tausayi tace "zamuje soon baby na,kiyita addua Allah ya tabbatar mani da abunda yafi alkairi kinjiko."
Tace "insha Allah ummi duk sallah ta zan miki addua dashi brother na d'in"
Tun daga ranar tasleem ta addabi ummi akan maganar sabon brother dinta,tana mata magiyar don Allah su shirya suje me suke jira.
Tun dai ummin tana lallashinta da nuna mata akwai lokaci har itama taji ta gaji da jiran lokacin,tunda dai zab'i ya rage nata taba fafa dama shine zai saka tayi ido biyu da gudan jininta,sai zuciyarta ta shiga tunani kala kala na abunda sukai ta faruwa agidan fafan,tsoron komawar yana shigarta don ance in maciji ya sareka inkaga tsumma saika razana,to kusan hakan nne har gobe bata manta da wuyar data sha ba amman sai ta dage da addua sosai ba dare babu rana,haka in dare yayi zata tashi tayi nafilfilu ta sanar da ubangiji damuwarta sannan ta nemi zab'insa na alkairi adukkan abunda ta saka gaba,kusan sati biyu tana abu guda taji ta samu natsuwa kuma ashirye take da ta koma gidansa,shiyasa ta shirya taje gidan baffa anan garin don sun baro riga tuni don Abbyn anwar ne yaje ya tattaro shi da iyalinsa suka dawo burni.
Sai kuma daga baya tayi tunanin su fara yin maganar da Abbyn Anwar tukun,tunda dai ko bakomi wajensa take dukkan wasu nauyinta yana d'auke mata su harda na baby,shiyasa sai ta barshi akan su fara yin magana da shi d'in inyaso sai shi ya sanar da baffan.Falon abbyn anwar taiwa tsinke kasancewar weekend ne kowa na gida ta same sa da khaleesat tana had'a masa breakfast,tunda ta shigo ya tsareta da ido yana adduar Allah yasa tazo masa da magana mai dadi,don tunaninsa sharetan da yayi cikin kwanakin ta canza shawara.
"Momyn anwar an tashi lfy"
Ummin ta fad'a tana zama cikin kujera tasleem kuma ta isa ga Abbyn anwar d'in tana hayewa cinyarsa,wani banzan kallo ta watsa ma ummin bata ansa ta ba ta cigaba da abunda take ummin bata sake ce mata komi ba ta maida hankalinta ga ogan tace.
"Yaya ina kwana"
Cikin sakin fuska ya ansa "lafiya lau dr antashi lafiya ya baby"
Tana murmushi tace "Alhamdulillah ga baby nan"Yaja hancinta yace "baby anyi breakfast"
Tace "eh munyi Abby,amman mu ba muci wainar kwai ba."
Murmushi yayi yace "to gyara zamanki yanxu sai kici."
Khaleesat na gama zuzzubawar ta samu waje ta kame ta dora kafa d'aya kan d'aya tana jiran jin abunda ummin ta zo dashi,shikuma baya son sunyi magana gabanta sai yace "momynsu don Allah ko zaki had'o mun bak'in tea da citta saboda mak'oshin nan har yanxu bai washe ba,jiya da kika had'a mun naji dadinsa."
Maganar da ya fad'a yasa tatashi tana wani lank'wasa gaban ummin tace cikin kissa "Haka akeso ai Abby,daman nasan zakaji dadinsa bari naje in kawo maka"
Ta fice tana danna ma ummi harara murmushi kawai tayi tana girgiza kai ta d'ago tana kallonsa shima ita yake kallo tace tasleem "bby na kije waje zan magana da Abbynku"
Tatashi da wainar kwai ga hannunta tace "to ummi"
Ta fice waje sai tamaido idonta kanshi,ya tsareta da kallo sai ta kauda idonta tace "yaya na yanke wani hukunci ne,shiyasa nace zan sanar dakai saika sanar da baffa komi kenan dai can saikuyi tsakaninku."
Gyara zama yayi yace "ina jinki."
Sadda kai tayi tace "daman *NA YANKE SHAWARAR ZAN KOMA GIDAN MINISTER*"
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...