*_NERNER AYSHER_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461🅿️........21
Shidda na safiyar Alhamis jirginmu ya sauka kano amugun gajiye nake jikina sai ciwo yake,waya ya fiddo yana kiran mami sofy sai mik'a take tana hamma.
Ya sanar da mamin saukar mu tace zata turo mani yanxu,wuri muka samu muka zauna kowa ka gani yana bukatar yaje yai fresh up d'in kansa.Mun d'an jima ba laifi sannan mani driver ya iso yazo ya dauki kayan mu ya saka cikin but sannan muka shiga muka tafi,kowa shiru kamar bamu da lafiya haka muka isa gidan.
Muna gama parking na fito naci karo da zainabu,cak na tsaya ina kallonta na kasa hkr yin shiru nace "mekike zo yi nan?"
Ta sadda kai kasa tana risinawa "Anty nanah sannunku da zuwa."
Dogon tsaki naja nace "dalla wuce anan kafin nai kwallo dake"
Ahanzarce tai hanyar cikin gida amman kafin ta karasa matakalar shiga ciki taji muryarsa yana cewa "zo nan zainab."
Kamar wadda k'wai ya fashewa aciki ta dawo kallonsa nai cikin takaici nace "mezatai maka."
Wani kallo yayi mun yace "ina ruwanki?"Sofy dai ta gaji da tsayuwa yasa tai ciki tana jaye da trolley d'insu,jikkar kayansa ya mik'a mata da mukullin d'akinsa yace "ki kai mun jikkar sannan ki gyara mun dakin zan fita."
Idona kamar zai fad'o kasa saboda kallonsa ita dai Abule wuce warta tayi hanyar dakin mus'ab d'in,ya maido idonsa kaina wadanda suke lumshewa suna budewa saboda gajiya.
Yace "inhar baki son mu ringa samun sab'ani dake ko na gaya maki maganar da batai maki dadi ba karki sake hantararta,ban hana kiyi mata kallon banza ba don wanna baya k'ari amman magana cikin masifa bana so,yadda baki takura sauran yan aikin ba to bakida hujjar da zaki ringa kwatsarta."Kallan idonsa nake da b'acin rai sosai afuskata nace "akan waccen kake kokarin kodayaushe ka bak'anta mun raina?kana nufin tafini muhimmanci kenan?"
Dan murmushi yayi yana cusa hannunsa cikin kansa ya lumshe ido ya bude yace "ni kawai ina son na koya maki daraja d'an adam,domin baka san ya kimarsa take wajen Allah ba balle ka ringa wulakanta shi,sannan ni bance tafiki muhimmanci ba kuma bazance kin fita muhimmanci ba...............nai nadamar jin wannan maganar akunnuwana.
Sai kawai na juya na dauki ledar kayana nai ciki daker nake tafiya saboda yadda kaina ya cushe da bacin rai,har wani jiri nake gani bana gane inda nake saka kafata,Allah dai kadai ya kaini dakina lafiya banci kasa ba.
"Safiyya ina yayanku?ba tare kuke dashi bane.?"
Mami take tambayar sofy bayan ta taddata dakinta ta fito wanka.
Tace "wlh ban sani ba nadai barosu shida yaya nanah tsaye waje yanxu haka fad'a sukai akan zainabu."Girgiza kai mami tayi tace "nikam da nasan rashin jituwa zai shigo tsakanin nanah dashi da bance yarinyar nan ta zauna ba,ni bada wannan manufar na zaunar da ita ba."
Sofy yace "Amman mami acan basuyi wani fad'a ba gaskiya,inaga dai yaya nanah tafara kishi."
Murmushi mamin tayi tace "tana iya yuwuwa hakan,shikuma ya gaza ganewa.kullum dai Addua nake Allah ya daidaita tsakaninsu,bari na kirasa naji inkin shirya ga breakfast can kije kiyiwa yayarku magana ta fito."
Mamin ta fita tana kiran mus'ab d'in.
"Salamu alaikum mami ina hanyar isowa gidane."Tace "to saika iso"
Ta kashe ta wuce d'akinta bayan ta sanar da asabe aikin da zatai mata.*****
Har na gama wanka maganganunsa ne suke soya zuciyata,abun bakin cikin shine yadda yake fifita waccen k'azamar yarinyar,amman duk laifi nane akan yadda nake nuna damuwata dashi.Na shirya cikin rigar atamfa doguwa na saka turare na gyara fuskata sannan na fito ina rik'e da wayata zan kira nabla,lokacin har takwas da rabi tayi.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...