part 7

91 5 0
                                    

*NERNER AYSHER*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3561

🅿️..........7

Tunda asuba mus'ab ya kira Mami awaya hankalinsa in yayi dubu ya tashi saboda ganin halin da Abbun yake ciki,daman jiya basuyi bacci sosai ba daya farka xaice "mus'ab ka kula mun da ahalina,mus'ab na dank'a amanar ahalina wajenka,katsaya masu ka zama bango majinginarsu"
Tun wannan lokacin ya sare da rayuwar Abbun,saboda har takai ga bayama gane waye kansa.
Babu shiri nida su mami muka garzayo asibitin tun agida na fara kuka na tashin hankali nida sofy,abdulrahman kuwa idonsa yayi wani irin fitinanen jaa.sai fad'a mami ke mana akan kukan nasan itama na karfin haline.

Muna isa muka samu sunna gay abakin k'ofar d'akin yana rungume da hannunsa ga kirji,kallo guda idan kai masa zaka gane irin tashin hankalin dake tattare dashi,mami na kallonsa saida duk yan cikinta suka kad'a muryarta na rawa tace "mus.......mus'ab Ab....Abbun yarasu ne."
Idonsa ya kad'a yayi mugun jaa ya girgiza kai muryarsa ashak'e yace "Aa hajiya,likitoci ne akansa tun safe nima jiran da nake masu kenan."
Zama tai jikinta yana rawa saman kujerun dake jere awajen,sofy fuska tai jajir don kuka ta matso kusada shi da hawaye share share tace "yah mus'ab jikin Abbun yayi tsanani ne har haka?don Allah idan akwai wani abu daya faru ka sanar damu."
Mugun tausayinta yaji ya dirar masa,wani feeling yakeji na kamar ya rungumeta yai ta lallashinta,sai yakejin duk damuwar ta tafi damunsa akan ta kowa.
Cikin lallashi da kalami mai dadi,wanda bata tab'a samunsa awajensa ba yace "kiyi hkr sofiyya kibar kukan nan haka kinji ko,insha Allahu ba zamu rasa Abbu ba.kuma tun bayan tafiyarku lafiyarsa kalau,cikin darene jikin nasa ya rikice,bana son ganin hawayenki rad'ad'in da nakeji araina karuwa yake don Allah kiyi hkr."
Kamar wata status haka ta tsaya da idonta tana kallonsa,wannan wace irin ranace agareta mai matukar dad'i da d'aci,da ace Abbun ta lafiyarsa lau hakika farin cikin da zata nuna batasan yawan sa ba,saidai ciwon Abbu ya wuce gaban tayi dariya.
Sauke idonta tayi k'asa saboda yadda yake kallon nata idon,kujera ya nuna mata cikin kulawa yace "ki zauna pls"
Ba musu ta zauna kusada shi wanda shi yakai awa guda tsaye ko gajiya bayayi,kamar wani tsohon soja.
Abdulrahman ne ya karaso inda yake ya bashi hannu suka gaisa,kowa fuskarsa babu kyan gani saboda damuwa.
Yace "yaya yajikin Abbun,kana ganin zai tashi kuwa."
Ya fad' muryarsa da rauni sosai har kwalla na taruwa cikin idonsa.
Rungumo kafad'arda yayi yace "karka tsorata muyita masa Addua,dukkan tsanani yana tare da sauk'i Allah zai tashi kafad'arsa"
Ya karashe cikin wani yana yi marar dad'i,don gaskiya kwarin guiwarsa na cewar Abbu zan tashi ya kare,shikadai yaga tashin hankalin cikin dare,don inka Abbu awannan lokacin bama zaka ce zai kawo safiya ba.
Tunda nazo wajen nai ma kaina masauki kasa na tsugunna kusada mami ina soka kaina cikin tafin hannuna ina kuka har lokacin,hakan bai hana ni jin duk abunda suke wakana tsakaninsu ba.
Amman rabin hankalina yana cikin d'akin da ake duba Abbuna,kukan da nake yasa na fara wani uban tari tun inayi ahankula har ya tsorata wad'anda ke wajen.
Mami cikin tashin hankali tace "nanah meyafaru,kin kwareni sannu mus'ab ku nemo ruwa don Allah,Abdulrahman bishi ku samo ruwa."
Duk ta rud'e baiwar Allah dora kaina nayi bisa cinyarta ina tarin,sofy banda kuka babu abunda take.
Cikin minty biyu mus'ab ya samo ruwan har sannan tarin nake,afirgice ya d'ago kaina yana shafa mun ruwan ga fuska,kafin ya kanga mun bakin robar ga bakina nasha sau d'aya tarin yasa na fiddoshi ruwan ya wanke masa rigarsa.
Bai damuwa ba ya ringa jera mun sannu,mami da Abdulrahman ma sannun suke mun.
Kara bani ruwan yayi ahankula na sha na kara sha cikin ikon Allah ya lafa,kowa saida yayi ajiyar zuciya.
Na maida kaina bisa cinyar mami ina sauke numfashi naji yace "sannu."
Banza nai masa duk da taimakon da yayi mun ni ba wani burgeni yayi ba,munafuki kawai.
Mami tace "sannu nanah,garin yaya kika kware."
Muryata tai wani irin sanyi,bama kajinta sosai saika matso da kunnenka saboda tarin ba d'an karami nai ba,nace mata "ban sani ba mami,naji dai kawai inayi."
Ta shafa kaina cikin kulawa tace "kiyi hkr kinjiko Abbun ku zai samu sauk'i."
Mus'ab ya koma inda yake ya zauna kusada sofy,data buga tagumi.
Kallon juna sukai ya kakalo murmushi ya sakar mata,lumshe idonta kawai tayi bata jin zata iya dariya ko murmushi.
Muna nan zaune wani likita ya fito aiko duk muka mik'e na riga kowa tun kararsa ina kermar murya nace "dr ya jikin sa,dr bazai mutu ba ko?don Allah karku bari ya mutu..........hawaye suna bin kuncina.
Mami ta rik'oni jikinta yace "kuyi hkr muna kan dubasa kuyita masa addua,."
Ya wuce yabarmu anan muka dawo muka zauna zaman jiran marabbuka.
Bai dade ba likita ya dawo ya shiga dakin,muna nan zaune bayan kamar minty talatin wani ya lek'o yace "muna son ganin matarsa."
Cikin hanzari mami ta tashi ta nufi cikin d'akin wani irin rawa jikinta yake,suka shiga suka rufe k'ofar.
Tashi nai inata *safah da marwa* awajen na kasa samun natsuwa,mami ta dad'e sosai kafin ta fito da kuka,ban tab'a ganin ko hawayenta ba sai yau kuka take na gaske.
Ta zauna kasa darshen tana kukan,ai sai muka dauka muma.
Anrasa mai lallashin wani,koshi mus'ab d'in tsaye yayi ya kasa magana.
Sake lek'owa likitan yayi yace "ina mus'ab da nanah"
Jiki na b'ari natashi muka shiga d'akin tare,wasu irin na'urori ne aka huda cikinsa aka saka masa,babu riga jikinsa ga oxygen an saka masa toshe bakina nai kar kukan ya kubce mun so koroni,yana hangoni ya ringa mik'o mun hannu.
Aguje na karasa wajen ia gunjin kuka likitan yace "karki kuka kinjiko,karki tada masa hankali yana son magana daku shiyasa muka barku kuka shigo."
Mus'ab da hawaye ke bin fuskarsa yace "insha Allahu"
Tunda yake bai tab'a jin tsoron rasa wani abu ba irin Abbu,ko mahaifinsa daya rasu baiji irin wannan feeling d'in ba.
Durk'usawa duk mukai gabansa na kama hannunsa ina kuka kasa kasa.
Likitan ya zame masa oxygen d'in ya fara magana wadda daji kasan bakinsa ya karye,daker yake fiddo maganar amman kuma muna ji muna kuma fahimta.
"Ayshertu kiyi hkr kiyi hkr kinjiko,rayuwa duk yadda tazo ansarta ake ayima Allah godiya,naso ace zanyi tsawon rai domin na saki farin ciki marar iyaka,Allah kadai yasan kaunar da nake maki,Amman ga halin dana tsinci kaina bana tunanin zan kara kwanaki,ku yafe mun nikam bakuyi mani komi ba na yafe maku duniya da lahira.saidai Ayshertu na wane Alkawari zakiyi mun."
Dora kaina nai bisa hannunsa ina kuka maganar ma ta kasa fitowa sai jan majina nake,ina kermar murya nace "Abbu bazaka mutu ba,babu inda zakaje muna nan tare."
Lumshe idonsa yayi yace "tambayarki nai wane alkawari zakiyi mun,wanda bazaki karya ba."
Ina shashsheka nace "Abbu nai maka Alkawarin bazan aikata duk abunda baka so ba,zan zama Abun koyi wajen kannena."
Jinjina kai yayi cikin wahalar ciwo,yace "inaso koda bayan raina ki dauki mus'ab matsayin yayanki wanda zai sakaki abu kiyi,sannan ki dauki rashida matsayin mahaifiyarki,kizama y'a tagari da kowa xai alfahari dake."
Ina kukan nace "to Abbu zan zama,insha Allahu ma bazaka tafi kabarni ba Abbu karka tafi don Allah."
Hawaye suka silalo masa ta gefen ido,ya saki murmushi ya maido dubansa ga mus'ab yace "Allah yayi maka Albarka,Allah ya tayaka rik'o nauyin da na d'ora maka,nasan zakayi tabbas zaka tsare mun iyalina duk wuya duk rintsi.sannan ga nanah nan ka zama jajirtacce akanta,karka yi fushi kace zaka saka mata ido,Aa ka danne duk bacin ranka wataran zakayi dariya kamar yadda kaji rannan na fad'a maka cewar na zab'a maka matar aure,to ba kowa bace face *NERNERH AYSHER*"
atsananin firgice muke kallonsa tashin hankalina ya bayyana,kukana ya tsaya na rikice nafara girgiza kai nace "Aa Abbu bazan iya ba,bazan iya daukar wannan ba don Allah kace wasa kake,wlh tallahi bana sonsa bana kaunar sa.Abbu ba dashi nake tsara rayuwata ba Abbu ina da hamid shine burina,shine zan iya rayuwa dashi."
Lumshe idonsa yayi yace "kiyo hkr nanah bakin alkalami yariga ya bushe....."
Aguje nabar d'akin saboda tashin hankali,mus'ab zuciyarsa babu abunda take banda bugawa,inhar kana tsaye kusada shi to tabbas zaka iya jiyo sautin ta.
Ya kasa magana ya kasa cewa komi saboda maganar tai masa mugun bazata,Abbun yace "kayi hkr mus'ab hakan danai shine daidai,saboda ba kowane irin miji ne zai hkr da halin nanah ba,tsoro nakeji kar aringa sakota gidan miji ana kirga mata aure,shiyasa naga ya dace na baka ita matsayinmata.
Har sadaki na biya maka ranar da mukaje sallar juma'ata ta karshr aranar ne nasaka aka *D'AURA MAKU AURE.*"
Ai mus'ab jiyayi dakin yana zaga yawa dashi,juwa na d'aukarsa Aure?shi aka daura ma aure da *AYSHER* Innalillahi wa inna ilahir raju'un.
D'an tari Abbun yake yayi saurin dawo wa cikin hankalinsa,idonsa jajir yace "Abbu meyasa?kasan bata sona kasani ba kalar mijin da take so ba kenan,sannan nima agida an riga an zab'a mun mata,Abbu ya zanyi." Yafada kamar zai kuka.
Dafa shi yayi cikin numfarfashi yace "kayi hkr mus'ab,banyi haka ba saida nai magana da kanen babanka,ya kuma sanar dani cewar bakomi sai kayi ta biyu da ita duk sadda ka tashi,nai bincike sosai har na gano danginka na kuma yi masu abun arxiki,nasan kana cikin wani hali dasu karka damu kayi addua Allah ya shige maka gaba."
Shiru yayi don yama rasa abun cewa,lallai akwai dramer acikin rayuwarsu ta nan gaba ga *Aysher ga zainabu* tabdijam.
"Mus'ab"
Abbun ka tsesa d'agowa yayi yana kallonsa yaga idonsa yayi wani tsanwa,hankalinsa ya tashi yace "ina jinka Abbu"
Yace "duk tsanani karka sake kace akwai kudadena wajenka,karka yarda nasan sufyan jiran ranar mutuwata yake yahau kan duniyata,nabarsa da mai mana ruwa don nasan bazai bawa masu hakki ita ba,amman duk nai ma lawyer na bayanin komi kuma zai tsaya masu,mus'ab ka zab'a ma sofiyya miji nagartacce karka bari tayi kukan rashina"

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now