*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️.........39
*Kano*
Ina gama sallar asuba na jawo wayata na kunna data na sauke app din karatun qur'ani na shuraim,sannan na kashe data na dauko qur'ani na bude sai na shiga app din danai downloading na kunna suratul jinn ina binsa ina kuma duba na cikin k'ur'anin har na gamata na shiga muzzamil itama na gama na shiga muddasir,haka nai tayi har saida na karanta sura ashirin cif na tsaya a ash shams na kalli agogo karfe takwas daidai na tashi da sauri ina rufe qu'anin na fice zuwa wurin mami don ban gaya mata zan koma kd yau ba,saboda shirye shiryen bikin Nabla.
Dakin sofy na fara shiga na sameta kwance tana waya na wani lumshe ido sai zabga murmushi take rik'e baki nayi da mamaki,don bazance ga ranar dana ga an sofyn mami na waya ba harda wani lumshe ido saboda kauna.
Dariya na saka ina cewa "tofa!sabon salo kenan"
Saurin tashi tayi zaune tana fiddo ido don mamakin ganina tana mun alamar nai shiru don Allah,tai saurin cewa "sorry lovely I'll call u later"
Tana sauke wayar ta turb'une fuska tace "kai yaya nanah don Allah."
Dariya nake sosai nace "to sweety kar nayi dariya saboda Allah?abunda ban tab'a gani bane dole zanyi mamaki ashe kina soyayya sweety."
Soke fuskarta tayi cikin filo tana dariya tace "don Allah ki daina wlh kunya kike bani"
Ina murmushi na zauna bakin gadon nace "don Allah kibar jin kunyar nan,gaya mun yaushe aka jone"
Tana dariya tace "yaya nanah kunya nakeji wlh"
Bata fuska nayi nace "tunda ba zaki gaya mun ba shikenan,"na mik'e zan fita tai saurin rik'o hannuna tace "zan gaya maki yaya nana karki tafi"
Na dawo na zauna ina kallonta sai murmushi take tace "lecture mune tun muna leve one ya nuna yana sona ni kuma lokacin bai mun ba,saboda kowa a sch d'in zakiji yana yabonsa kyakkyawane sosai yaya nanah,yan mata sonsa suke kamar hauka ni kuma duk abunda akai ma taron dangi bai burgeni,so yadda yaga ina basar dashi da nuna halin ko inkuka dashi yasa shikuma abun yake b'ata masa rai,don me ni bazan nuna damuwa akansa ba yadda saura keyi,rannan nai missing test dinsa da yace babu wanda zai ma make up amma da yaji harda ni sai yasa ma kowa ranar da xai mana,nice karshe acikinsu da nace banyi na hkr zanyi c.o din course d'in,sai su Ramlat sukace zasu zo har gida su sanar da yaya da mami dole yasa nashirya ranar wata juma'a naje office d'in nashi."
"Nai sallama yana ta aiki ya d'ago ya amsa ciki ciki,nai tsaye saida yaga dama sannan yace na zauna na samu wuri na zauna ya dauki wata jotter ya rubuto mun questions d'in"
Dariya ta saka tana rik'o hannuna tace "yaya nanah kinsan me ya rubuto mun a paper shit din kuwa?"
Ina murmushi na girgiza kai tace "ina ansa na tare da booklet zan soma karantawa kawai naga ya rubuta *Your full name.........*
*your phone no........*
*And your address.........* a firgice na d'ago ina kallonsa,sai ya sha mur kamar baisan kallonsa nake ba,ganin dagaske bazai ce komi ba yasa ni nace masa "sir what's this?"
Wani kallo yake jifata dashi yace cikin calmly voice dinsa "ur test mana"
Na b'ata rai nace "sir pls kai mun question din da kai ma saura don Allah ni kam bazan iya ansa wannan tambayoyin ba"
Ajiye biron sa yayi yana kallona yace "duk yadda kika yi daidai ne,ki amsa tambayoyi na saka miki mark dinki,ki k'i amsawa na saka miki absent"
"Kamar zan kuka dole na cike masa na dan farar da takaddar na fice ba tare dana jira abunda zaice mun ba,gab da zamu fara final exams ne abun ua faru tun daga ranar naita expecting kiransa ko zuwansa gidan mu amma babu ko guda,ganin har mun fata exams yasa na kwantar da hankalina muka fara exams cikin kwanciyar hankali,muna sauran kwana uku muyi graduation da dare aka kirani ina dauka naji muryarsa na ganesa,gaisawa mukai yake tambayata ya exams don shi bai samu zama ba ranar da akai tashi naji ance ko yana Germany oho dai,gaisawa kawai mukai ya kashe daga ranar kullin zai kirani safe rana da dare kuma only gaisuwa muke,yaya nanah kafin nayi aune mutumen nan yayi wuff da zuciyata yai mun kane kane acikin rai in fact ban san ma lokacin da soyayyarsa ta kamani har haka ba,kiji yadda akai muka jone da *ABDOUL_NASSER* (It's my favorite book😍)
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...