*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........ 49
Wani irin xazzab'ine ya rufeni da ciwon kai saboda tsabar kukan da nasha saboda tunda goggo sabira da momy hafsa suka shigo ɗakina suka sanar damu cewar motoci sungama hallara hankalina yai mugun tashi,na fara kuka wanda kowa yaji hankalinsa ya tashi,ni kaina banyi tunanin zanji ciwon rabuwa da gida har haka ba saboda nasan wanda zanje gidan nashi yai mun tanaji na musamman na kulawa da soyayya,amma duk da haka gida daɗi gareshi kuma wannan kukan ya zama kamar dole ne ga amarya saboda sabo da shaƙuwar da sukai da iyaye da ƴan uwanta,mutane da dama sun tausaya mana nida sofy ganin yadda muka maƙale juna daƙer da siɗin goshi aka rabamu akajani ina tirjewa muka fito,wurin mami aka kaini nan ma wani sabon kukanna dasa saboda na tun bayan rasuwar ABBU ba wanda nake kallo a madadinsa face ita,ta taka muhimmiyar rawa acikin rayuwata bazan taɓa mancewa da mami ba har abadan,kuma zan dawwama ina mata addua kamar yadda nakema iyayena.
DUk ƴan uwan su mamana da na Abbu suka taru ana mun nasiha da faɗa kowa da irin nashi tun ina fahimtahar nakai ga bana ganewa saboda kuka,ita kanta mamin hawaye take sharewa.
yadidi na rungume dani jikinta tana lallashi muka fito aka sani mota yadidin ta shiga ita da goggo sabira suka sani tsakiya sannan mani driver yaja mukai gaba sannan sauran motocin suka biyo miu abaya,kaina yana cikin mayafi bazan iyagane ya tsarin gidan yake ba,amman ayadda naji bakin su yadidi hakan ya tabbatar mun da cewar ba ƙaramin gida bane kowa bakinsa masha ALLAH yake faɗa,saida muka zo bakin ƙofar shigamain falon sannan yadidi ta umurceni nayi addua tana karanto mani ina amsawa sannan tace na shiga da ƙafar dama.
ahaka har aka sadani da ɗakina muna shiga wani sassanyen sanyi da ƙamshi ne suka baibayeni sanyin yana ratsa ni har cikin ƙashina,haka zalika ƙamshin kanshi mai daɗin gaskene.
zaunar dani yadidi tayi tace "Alhamdulillah Nanah kin iso gidanki lafiya ubangiji ALLAH ya zaunar daku lafiya,ya kawar da dukkan wata fitina da zata ratso tsakaninku,ki kauda kanki kiyi hƙr zaman aure sai an hƙr duk wanda kike gani zaune gidansa lafiya nanah wlh hƙr ne ya zaunar dashi haka,don haka inhar kinji nasihar da mukai miki zaki zauna lafiya kuma mijinki xaiyyi alfahari dake.............sai kawai na saka mata kuka momy cetaita lallashinaInaji ina gani suka sakai sukatafi suka barni dagani sai k'awayena da basu wuce biyarba,don wasu ana kawoni suka ce zasu tafi don dare yayi tara ta wuce sosai,kwance nayi saman lallausan gadon da aka zaunar dani na dunk'ule wuri guda ina shashsheka ina tariyo rayuwata ta baya,Ashe dai nan ne gidan Aurena ashe bani muda rabo da hamid,duk soyayyar da na nuna masa ta tafi sai gashi wanda na tsana nake nuna ma kyama shine na kasance k'ark'arshin ikonsa,lallai babu ta inda Allah baya ikonsa kaidai bawa in zakai k'ikayi saisa saisa haka inzakai so kayi shi saisa saisa sannan karmu ringa fidda tsananin kiyayyarmu ga mak'iyanmu saboda bakasan me gobe zata haifar ba,duk wanda kuka gani da irin baiwar da Allah yayi masa Allah yasa mudace.
Ina nan kwancr sofy ta dafani cikin tausayawa tace "yaya nanah kiyi hkr kitashi kiyi wanka kinji jikinki kuwa?"
Muryata ta dishe ga wani irin ciwon kai da nakejin kamar zai fasa mun kaina, daker nace "sofy sanyi nakeji kuma kaina ciwo yake"
Layla ce ta shigo ita da zulaihar goggo sabira sofyn tace "yaya layla kin samu yayan awaya,jikin nata taketa complain"
Wayar ta mik'o ma sofy tace "ya d'auka kiyi masa magana."
Saurin ansa sofyn tayi ni kuma na koma na kwanta ina rufe idona saboda yadda nakejin jikina,nasha kuka sosai dole zan jigata ga yunwa daman ba wani abinci nake ci ba.Sofy tace "yaya kana ina"
Mus'ab da suke cikin mota shida faisal da musbahu wani abokinsu sunata hira da raha suna tsokanarsa sun rakoshi,yace "ya akai ne an sofyn mami"
Tace "yaya ka kira dr yaya nana fa bata da lafiya kwance take wlh,bakaji jikinta ba"
Hankalinsa ya tashi yai saurin fitowa motar yana cewa "gani nan shigowa"
Ya kashe wayar faisal yace "lafiya?"
Yana danna wayarsa cikin damuwa yace "cutie ce bata da lfy bari na kira dr sha'aban"
Musbahu yace "rud'ewar ciwon cutie yasa ka manta da dr kake tare"
Dafe kai yayi yana murmushi yace "wlh musbahu na shafa'a hankalina ya tashi mu shiga to"
Faisal ya saka dariya yace "toda uban me zai dubata"
Kanshi yake shafawa duk ya rikice yace "sorry bana cikin natsuwata,yanxu ya xa'ai to."
Yace "bari muje da faisal clinic d'ina muna dawowa ka shiga ciki ka dubata"
Haka kuwa akai shida faisal suka ja motar suka bar kofar gidan shikuma jikinsa yana rawa ya shigo cikin kantamemen get d'in maigadi ne yake gaidasa sama sama ya ansa mashi yai ciki,da sallama ya shigo duk suka tashi daga zaunen da suke cikin lumtsatstsun kujerun dake falon,cikin damuwa sofy tace "yaya ka iso?tana d'akinta mun samu tayi wanka da ruwan d'umi ta kwanta."
Ledojin daya shigo dasu ya bata yace "kije kitchen ki juyesu,wannan na kune bari na dubata"
Layla da xulaiha suka gaidashi ya amsa da kulawa sannan ya nufi d'akin.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...