*_NERNER AYSHER_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461🅿️........16
Washe gari nanah kadai ce bata tashi da wuri ba tun asuba da mamin ta tadata sukai salla ta koma ta cigaba da bacci,sofy kuwa daman tana da lecture tun eight so bakwai da rabi mus'ab ya fita da ita don shima yana son yaje akwai wani aiki da yake nema ance yazo yau.
Bayan an gama had'a breakfast zainabu tabi ta share gabaki d'aya gidan tun daga falo har waje kitchen ma asabe ta nuna mata yadda zatai mopping tana yi tana gyara mata,tayi ta tisa har saida asaben tace yayi haka nan.
Sannan tazo ta goge falukan guda biyun shima kuma tayi da kyau,indai aikine to zainabu bata da ragganci inhar ka nuna mata aiki to zata yi maka ita dai barta da wauta da sakarci sai kauyancin ta bacin haka zainabu bata da wata matsala.
Mami mamaki tai tayi ganin aikin da tayi tasaka aka kirata mamin na zaune dining tana break suka shigo ita da lantana.Zubewa k'asa tayi tana cewa "hajiya ina kwana."
Mamin tace "tashi ba haka ake gaida mutane ba,inkika tsaya ma atsayen ya wadatar naga aikin da kikai waya nuna maki."
Washe hakora tayi da yasa mami saurin kawar da kai gefe saurin rufe bakin tayi tace "ai hajiya asabe ce ta nuna mani yayi kyau kuwa?na iya hajiya."
Jinjina kai mamin tayi tace "anshi nan"
Ta bata sabon brush da marclearn tace "lantana dake zan had'ata sau uku arana zata ringa goge baki,ta ringayi gabanki don Allah duk jinin da yake fita karki sake tace zata daina,ki kula sosai."
Wangale baki kawai zainabu keyi tace "hajiya buruhi zan ringayi nima,kice xan zama yar burni nima"
Mamin tace "abunda zance dake zainab,kinga yadda kikai aikin nan to haka nakeson ki ringayi koda yaushe cikin natsuwa,sannan zan ansar maki makullin dakin mus'ab daga yau ki ringa gyara masa lantana ki ringa binta kina saka ido."
Tace "an gama hajiya insha Allahu."
Zainabu jin ance zata ringa gyara dakin mus'ab tahau dariya "nagode hajiya Allah ya tsindumaki aljanna."
Murmushi kawai mamin tai sannan ta sallame suNaji dadin kwanan d'akin mami sai nakejin wani bangare na zuciyata yana bata matsayin mahaifiya,duk da irin abubuwan dana ringa yi mata bai saka ta wofintar dani ba,duk sadda nake bukatar kulawa tsaye take akai kuma bata takura mun akan abubuwa da yawa.
Ta silar sofy yasa nafara rage yimata wasu abubuwan,da mami bata isa tace mun banyi daidai ba yanxu zan rufeta da masifa amman ahankali sai nafara hankalta har nakejin zan iya kallonta matsayin mahaifiyata.
Jiya dana kwana ajikinta ban tab'a samun natsuwa irin ta lokacin ba,sai naji kamar kar safiya tayi.
Mik'a nai ina salati wasai na kejina wani irin nishad'i na tashi dashi don haka na sauko na fito karo mukai da mamin zata shigo,murmushi nai mata mai sanyi ina dora kaina gefen kafad'arta na shagwab'e murya nace "mami ina kwana."
Mamakin da mamin tai bai hana tashafa fuskarta ba tace "yaya nana sarkin kuka tatashi bacci."
Dariya na kyalkyala wadda ta fiddo mun da duk wani boyayyen kyau na da nake dashi,tace "da ace kullin haka kike da kuwa kyawunki ya ta fitowa,saboda dariya tana maki kyau."
Dariyar na kara yi nace "mami yunwa nakeji."
Shafa kaina tayi tace "to wankan zaki fara ko cin kala cin."
Nace "banyi brush ba fah."
Dod'e baki mamin tayi tana tureni "wai wai shiyasa ma naji hamami ko?"
B'ata fuska nai "wayyo Allah mami wlh bana warin baki."
Dariya ta saka mun nima na kama yi tace "to kije ki shirya kafin ki fito na shirya maki break d'in zan kai maki can falon Abbunki,yau ki wuni acan kiyita masa Addua."
Murmushi nai nace "to bari naje."
D'akina na wuce cikin nishad'i bana kaunar duk abunda zai kawar mun da wannan jin dadin na yau,rabon da naji xuciyata haka tun kafin raduwar Abbu.
Shiyasa duk yadda zuciyata take son sanyo mun hamid na katange ko ina na hanata don komi zai iya wargaje mun.
Kananun kaya yau na saka wanda na mance rabon dana saka su,wandone black sai yellow din riga mai dogon hannu tsawonta sai kawo guiwata,akwai tsaga gefe da gefen rigar wadda tsagar zata kawi daidai k'uguna ana ganin hips d'ina kamar zasuyi mgana,haka daga sama tadan kamani breast d'in sun fito masha Allah tubarkallah.
Farar powder kawai na saka na fesa turare ko kwalli ban saka ba,mamakin kyawun da nayi nake don ni najima ban kalli kaina jikin madubi ba,araina nace "inama hamid zai gan........saurin dakatar da maganar nayi ina lumshe idona,.
"Allah ka bani hkr rashin wannan masoyin nawa,ka samun salama akan wannan kaddararren auren ka kawo mun karshensa.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...