*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........30
Mus'ab ne zaune kasa saman kafet cikin falon baban su hafsat wanda falon yaketa k'amshin turaren wuta,tun kafin yazo aka share falon k'al k'al aka kakkab'e kujeru da wata drower da yake jera litattafan adininsa,aka goge d'an tv stand din dake falon wanda wata jibgegiyar tv da tajima da lalacewa take akai.
Maman su ta canza labule ta cire tsaffin nasa da sukai daud'a ta saka mashi nata da aka wanke jiya,ba yadda batai da baban hafsa ba akan asaukeshi falonta zaifi kyau amman ya nace dole nashi za'a saukesa.
Kanen hafsat d'in duk ankorasu isilamiyar dare duk da cewar yau malamin su bazai zo ba haka mama ta tirasu tace su shiga wani ajin,karsu ishe bak'o da hayaniya.
Tun marece daman aka soya masa zabgegiyar kasa dank'waleliya aka siyo lemu kala biyu coca cola da lacasera,sannan mamar ta tura kanwar hafsat gidan yayarsu dake kasan layinsu ta anso kula da plate da cup harda spoos,don shinkafa da miya ce akai yau gidan matsayin abincin dare harda naman sanuwa baba ya siyo kasuwa.
Fasail dariya kawai yake ganin yadda duk suka rud'e da zuwan mus'ab d'in matsayin sirikinsu,bacin on ready da matarsa shidai yayi shiru yabarsu suji daga bakinsa,duk da yana farin cikin ace mus'ab ya auri hafsat amman yana son alakarsa da nanah ta gyaru.
Haka aka shirya masa wannan k'warya k'waryar liyafar duk shi kad'ai,aka wanke gida aka goge saboda broken tayils ne tsakar gidan yafi shekara ba'a wanke ba sai wannan ranar.Sadda ya kira hafsat cewar yana hanya mama ta sata d'aka suka hau zab'en kayan da zata saka,idan kaga yadda daga uwar har d'iyar suka gigice saika ci dariya har cikin ka yayi ciwo,don dauka zakai sarkin kano ne zaizo wurin hafsat d'in suka rud'e haka.
Kayanta na wannan sallar wata atamfa mai kyau mamar tace ta saka riga da siket ne akai mata,dinkin yai kyau sosai kuma yahau jikinta ainun,da yake ba kushe hafsat mai kyai ce gata da dirin jiki masha Allah duk da dai irin matan nan ne masu manyan breast hakan bai munan tata ba gaskiya.
Duk wani turare da mama take dashi ta fiddo ta bata tace ta saka don ta kara k'amshi yasan cewar tana da tsafta sosai,har take ce mata.
"Kinsan maza irinsu suna bala'in son k'amshi da tsafta don haka sai ki dage."
Murmushi hafsat d'in tayi tace "mama wlh na yarda saboda shi kanshi kullin cikin kamshi yake."
Mamar tace "kin gani ko,ai gara kema yaji kina k'amshin yadda zaiji k'warin guiwar auren naki."Sadda ya iso faisal ne ya shigo dashi yana tsokanarsa yana dariya kawai,mama ce ta fito bakin k'ofar d'akinta ta tsaya tana washe dukkan hak'oranta cikin farin ciki suka gaisa.
Tace "ka shiga dashi faisal kafin baban naku ya dawo sallah."
Tare suka shiga mafarin zaman nasa kenan yana jiran baban ya dawo,faisal ne yake d'an taya sa fira suna tattaunawa akan bude restaurant d'in da za'ai kwanan nan saboda an riga an gama komi,har mus'ab d'in yace zasu saka rana su fara tantance ma'aikatan da zasu d'auka.Hafsat ce tai sallama cikin siririyar muryarta tana dauke da tire mai kyau da suka aro gidan yayarta fa'iza,fuskarta dauke da murmushi mai kyau.
Had'a ido sukai dashi sai ya sakar mata murmushin shima yana tashi ya anshi tire d'in ya ajiye kasa ta zauna gefensa tana gaidasa."Anya ma zan ansa gaisuwarki My haf"
Soke kai tayi cike da kunya tace "kaya kuri yaya mus'ab laifin me nayi."
Yace "Aa bazan fad'a gaban d'an sa ido ba yayi mana dariya."
Murmushi tayi tana wasa da hannunta bayan ta gama zuzzuba masa duk abuda ke wurin.
faisal yace "oho ka gama gulmar taka yanxu dai na zama sirikinka don haka dole ka ringa bani girma."
Saurin tashi tayi zata fita yace "ina kuma zaki."
Tace "zan baka wuri ka ci abinci inkun gama kafin katafi zan dawo."
Ta juya ta fice cike da tsantsar farin ciki marar misaltuwa.
Sauke idonsa yayi kan garar da aka shirya masa yace "faisal wai duk ni akai ma wannan garar?meyasa baka hana su ba aini ba bako bane d'an gidane."
Yace "to yazanyi dasu danai kokarin dakatar dasu ma mama fad'a ta kamayi dole na kyalesu."
Shiru yayi yana tunanin yadda zasu kwashe da baban,don gaskiya duk da yana ra'ayin hafsat bai shirya kara aure yanxu ba,yana da bukatar suyi magana da Aysha yaji ambition d'inta akan Aurensu komi zai yanke daga baya sai ya yanke amman not now gaskiya.
Faisal ya katsesa da cewar "mus'ab meyasa ba zaka hkr ku daidaita da Aysha ba kafin wannan maganar?"
Shafa kanshi yayi yana jin yadda take yawo acikin zuciyarsa,ya k'osa yaje gida ya kirata ko zai samu sukuni.
Yace "faisal naso hakan kwarai,saidai Aysha tak'i bani dama kullin rigima da fad'a tsakanin mu wanda bana jin dadinsa ko kadan,bazan boye ma ba wlh nagaji da zaman tazurancin nan mace nake buk'ata kusa dani."
Dariya faisal yayi yace "banga laifinka ba at ur age ai kakai ka bukaci haka,amman karkayi garaje kayo tunani mai kyau azahirin gaskiya zanso ka da hafsat don ba yabon kai ba duk gidan nan ba mai halinta mai kyau da hkr ga addini,saidai kuma yadda alakarka take da mahaifin Aysha da yadda auren ku yazo bazan so ace ko tare wa bakuyi ba ka sake rakito wani auren,sai nake ganin kamar sha'awar da kake da ita ne take damunka yasa kake son kara auren,saboda mai kamar Aysha bana jin zai nemi kari nan kusa kusa Kayi tunani sosai."
Jinjina kai yayi yace "uhmm faisal kenan na yarda da maganarka nima nasan Aysha babbar macece mai aji ta iya tafiyar da rayuwarta kan tsari,haka kyakkyawace sosai ba namijin da zai sameta yakasa afkawa kaunarta,saidai kuma tana da wasu kalubale da ni awajena babban kalubalene da zasu dankwarar da alakarmu,bacin haka banga alamar tana sona ba ta fad'a ta sake nanatawa bata kaunata bazata tab'a sona ba wannan abun shine yake sace mun guiwa amman zahirin gaskiya wlh *I'm in love for her too much* wlh don Allah kabani shawara."
Jinjina kai faisal yayi yace "zan baka shawara amman kaje ka saurari zuciyarka acikin Aysha da hafsat wacce kake so wacce kake sha'awar yaranka su biyo ta jikinta,saboda nai maka wata fahimta wanda ba lallai ka yarda da hakan ba."
Mus'ab yace "ban gane mekake nufi ba?ba yanxu na gama gaya maka ina son Aysha ba kuma ina son Auren hafsat itama kuma ina sonta."
Girgiza kai yayi yace "na yarda sosai kana son aysha,amman ina kokwonto akan cewar kana son hafsat,abunda yaja hankalinka ga hafsat shine halayenta da kuma addininta saboda nasanka sosai kana bala'in son mace mai addini saboda zata haifa maka yara masu tarbiyya da addini kuma zata kula dasu yadda addini ya tanadar,wannan dalilin yasa kake son auren hafsat don haka abunda zaka cema baba shine ka sanar dashi aurenka da Aysha,harma da yadda auren yaxo sannan kace kana bukatar lokaci don ka daidaita da ta gida kafin kasan matsayar da zaka tsaya.inba haka ba baba zai cika maka ido ka kasa fadar abunda ya kamata."
Shiru yayi yana sauraren faisal yana auna maganganunsa duk da haka shi yana jin yana son hafsat,saboda kafin ma asan za'a had'asa da Aysha ya had'u da ita suke tare.............sallamar baban ce ta tsinke masa dogon tunanin daya lula faisal ya tashi yace "inkun gama ina waje ban key d'in motar"
Mus'ab ya fiddo daga cikin aljihu ya bashi yafice.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...