*NERNER AYSHER*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3561🅿️..........8&9
Afusace na turesa da iyakar d'an karfin daya rage mun,ina cewa "dallah can cikani,ina ruwanka da fad'uwata kabarni na fad'in mana jikinka ko nawa,"
Naja dogon tsaki nace "sai tsami kake zaka had'a jikinka da nawa."
Idanun sa kawai ya zuba mata yana kallonta,azahiri bazaka ga b'acin ransa afili ba amman a zuciyarsa shikadai yasan yadda yake jin ransa,shine yake tsamin kenan?lallai zai koya ma yarinyar nan hankali soon.
Jiri na d'ibata na d'an zauna bakin gadon har sofy ta shigo ta kama ni muka fito yana biye abayan mu.
Tuni hamid ya tafi mota guda ce wadda sunnah gay ke jan Abbu da ita inzasu fita cikin gari,Nabla da ni da Abdul muka zauna baya sofy ta shiga gaba shikuma ya jamu muka bar asibitin.Har muka je gida ba wanda yayi magana,tunda aka bude get din muka kutsa kai cikin gidan namu moments dinmu da Abbu suka fara dawo mun cikin kaina,hankalina ya fara tashi kaina ya fara juyawa.
Muna tsaya wa duk kowa ya fito ni na kasa dukar da kaina nayi na fara kuka ba kama hannun yaro,ba karamin kuka ba.
Duk hankalin su ya tashi sosai Abdul ya dawo shida sofy da nabla suna aikin lallashi,amman kukan nake.
Sofy itama tana hawaye tace "yaya nanah idan kina kukan nan kamar kina jayayya da lamarin ubangiji ne,kiyi hkr ki fawwalama Allah kowa fa dole saiya koma inhar yazo duniya,wannan kukan baya maido Abbu saima matsala da zai jamasa.inhar kina son Abbu ba ta haka zaki nuna soyayyarki dashi ba."
Mus'ab na gefe yana kallonsu yanajin duk abunda sofy ke fad'a lumshe ido yayi yana jin jina kaifin tunaninta da tawakkalinta,yarinyar tana matukar burgesa hakinta ya masa inama ita aka bashi da bazai wani damu ba.Abdul yace "Abunda sofy ta fad'a gaskiya ne yaya nanah,kuma muma duk muna jin irin ciwon da rad'ad'in da kikeji bamu da yadda zamuyi face Addua da neman Allah ya sama na dangana."
Nabla ke share mun hawaye nace cikin shak'ak'k'ar murya "baxan iya shiga gidan ba tsoro nakeji,gani nake kamar zan gansa ku mai dani asibiti naita zama acan hankalina bazai iya kwanciya ba wlh."
Dafe kai sofy tayi saboda dai bata san kuma me zata ce mata ba,Abdul yakamo hannuna yana kokarin fiddoni daga motar na tokare "ka sakeni bazan iya shiga ba don Allah Abdul ka sakeni bazan iya ba,ku maidani asibitin na zauna acan."
Takowa yayi har inda suke yace "sofiyya,Abdul kuje cikin gida saketa kuwuce."
Duk kallonsa sukai yajin jina masu kai yace "kuje zata shigo yanxun"
Nabla tace "kana ganin yadda take gardama,duba fa kaga ta koma cikin motar."
Yace "na gani jeki kema yanxu zata shigo insha Allahu."
Rausayar dakai tayi sukai gaba sofy na waigowa murmushi yayi mata,wanda taji har cikin ranta.
Saida yaga shigarsu sannan ya bud'e k'ofar inda take zaune yatsaya yana kallonta,ta dunkule waje guda ta tattare duk kafafunta ta saka kanta aciki tana kuka.
Lumshe idonsa yayi ya bud'e kafin ya bude baki yace "Aysher"Cak natsaya da kukan saboda fitar muryarsa da fitar sautin sunan sunyi matukar yin tasiri cikin kaina,jin tayi shiru yasa ya sake cewa "Aysher d'ago kanki don Allah"
Mamaki nake da yadda ya ke furta kalaminsa wanda yake sakani jin bazan iya masa musu ba.
Ahankula nake d'ago kaina har na d'ago sa baki d'aya.
Amman ban kallesa ba kirjina yaketa d'agawa saboda shashshekar kukan da nake,ina sauke ajiyar zucoya.Sake sassauta murya yayi yace "kallan ni"
K'iya wa nayi saida ya sake cewa "ki jiyo ki kalleni nace"
Idona jajir na d'ago dasu na sauke akansa cikin ransa yace "tubarkallah masha Allah."
Cikin lallami da natsuwa yace "kinyi imani da Allah da manxon sa?"
Lumshe idona nayi yayin da sauran hawayen da suka rage cikin suka silalo mun kafin na jinjina kaina alamun eh.Ya sake cewa "kinyi imani da ranar tashin alk'iyama."?
D'aga kaina nayi ina share hawayena yace "to inhar duk kinyi dasu kisani cewar babu wanda ya isa ya dawo maki da mahaifinki domin wanda ya tafi baya dawowa,inhar kinyi imani dasu kiyi hkr kiyi masa Addua domin mamaci baya son kuka,kije kiyita sallah kina masa Addua shine abunda zai saka yayi alfahari dake,inhar kikai gardama kika cigaba da kuka Abbunki baxai tab'a alfahari dake ba,shin kina son ayiwa mahaifinki azaba.?"
Girgiza kai nayi ina hawaye yace "to wad'anan hawayen kidaina su,sannan kije kiyita masa addua,tashi muje cikin gida mami na jiranki."
Jikina rawa yake sosai ganin haka sai ya mik'a hannunsa alamun na kama,banyi masa musu ba nasaka hannuna cikin nasa.
Bazan iya kwatanta taushi cikin hannunsa ba amman yafi auduga taushi,har na fito yana rik'e dani ya rufe motar bai saki hannuna ba sannan ya nufo hanyar cikin gidan.
Har sannan hannunsa cikin nawa duk suna falon zaune muka shiga da sallama bakinsa,duk binmu da kallo sukai bai direni ko ina ba sai gaban Mami.
Kasa na zube wajen kafafunta na dora kaina bisa cinyarta na rufe idona kawai,mamin tace "sannu mus'ab Allah yayi maka Albarka."
Ya risina yace "nagode hajiya."
Ya juya ya fita daga falon.
Kaina take shafawa sai ajiyar zuciya naketa saukewa,cikin lallami da taushin kalami tace "kiyi hkr Nanah ki anshi rayuwa ayadda tazo maki,haka Allah ya kaddara mana kinjiko."
Shiru nayi kawai ajikinta don nikad'ai nasan hali da zuciyata take ciki.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...