part 34

114 10 0
                                    

*_NANAH AYSHA_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........34

              *ABUJA*
     *MAI TAMA ESTATE*

Fafa ne acikin kasaitaccen falon sa dake upstairs cikin daya daga cikin lumtsastsar kujerunsa royel kirar Italian,jikinsa dank'areriyar shaddace gezner fara k'al mai dan banzan kud'i harda babbar riga jikinsa,idonsa sanye da farin glass kafafunsa sawu cikine bak'ak'e masu masifar kyau hannunsa da agogo kirar Gucci baka itama sai zabga k'amshi yake ya dora k'afarsa d'aya bisa d'aya yana kallon news.
Yayin da wani MD na babbar asibitin dake cikin garin Abujar suke magana yana saurarensa yace "yallab'ai sunan ta Rayhana Rufa'i likitar mata ce kwararriya ma tasan aikinta sosai yallab'ai."
Gutun murmushi fafa yayi yace "ina take zaune?"
Yace "yallab'ai tana lugbe agidan wani yayanta take zaune wanda suke ya'ay'an wa da k'ane,tana da 'yarta daya mace mai suna tasleem kuma a yanxu haka bata da aure tun da mijinta ya rasu baban yarta bata sake aure ba shekara bakwai kenan."
Jinjina kai fafa yayi yace "ka iya aikin da aka saka MD don haka godiya nake ga wannan ka k'ara mai idan ina buk'atar wani abun zan sake gayyatoka"
Ya rusuna yana murmushi da jin dadi ya anshi kud'in da fafan yake mik'a masa yace "Alah yak'ara girma yallab'ai"
Sukai sallama ya juya ya fice cike da jin dadin samu dubu d'ari uku akan d'an binciken da yayi masa.

Shigewa yayi cikin kujerar tasa yana murmushi tare da lumshe idonsa,at least bata da aure yanxu hakan na nufin zata sake zama tasa karo na biyu,to Amma ta yaya?zance zashi?awaya zai kirata?sawa zai a daukota?wanne ne yake daidai wane yadace yayi?..........sallamar da yaji yasa ya tashi yana bud'e idonsa ya sauke su akan teema,daga bakin k'ofar ta tsaya cikin tsoro da shakkar sa saboda kwata kwata yanxu fafa ya daina yiwa kowa dariya,duk irin farin cikin da yake ciki kau da yashigo gidan zai d'inke fuskarsa ya haye sama,yana da masu masa hidima acan kafin ma ya dawo anyi komi.
Namiji hake gyara masa bedroom dinsa da sauran dakunan da falukan,wadda ke masa abinci kafin ya dawo ta shirya taje ta jera masa mai serving d'insa na tsaye yana jiran isowarsa ya anshi jakarsa ya kai masa sannan ya dawo yajira fitowarsa ya zuba masa abinci yaci,ya dawo falo yana kallon news in akwai aiki gabansa ya wuce can study room dinsa yayi abunsa baya buk'atar koda kallon fuskar lubabatu.

Kallonta yake atsanake yayin da ta sunkuyar dakai tana risinawa tace "fafa barka da dare"
Kansa ya jinjina tace"daman su momy salma ne suka zo sunce nai maka magana zasu iya k'arasowa nan"
Baice komi ya jinjina kai kawai harta juya zata tafi yace "and u should call me mammah ku"
Ta sake risinawa tace "to fafa"
Ta idasa ficewa ya tashi ya wuce bedroom d'insa don yin wanka da shiryawa don dawowarsa kenan daga office tare suka taho da MD mujitafa.

"Momy salma yace ku isa can"
Sakina ta sauke ajiyar zuciya tace"wlh har naji sanyi,kunsan tunda tatafi gabana yake fad'uwa saboda gudun karya korota."
Salmar ta girgiza kai kawai tana ajiyar zuciya rumana tace "Ai kamar kin shiga zuciyata wlh nima a d'ar d'ar nake."
Mariya tace "ni tsorona karya zo ya fatattakemu don naha fafa kowama haushinsa yakeji."
Salmar dai ba tace komi ba sakina tace"ai ba kowa yaja duk wannan masifar ba banda mammah,inda tayi hkr tun wancen lokacin haka ta faru,gashinan ta jawo kanta muma ta ja mana Allah sarki d'an k'anena ko yana ina yanzu."
Sai yanxu salma tayi magana tace "tun ranar da ta bamu labarin wlh nake tunaninsa,sai naji ina kaunar haduwa dashi kusa kusa."
Teema tace "wlh nima momy haka nakeji araina zanso inga dawa yake kama nasan ba makawa sak fafa ne kuma inhar fafa ya biyo wlh ba k'aramin kyau zai ba"
Dariya Rumana da su mariya sukai salmar tace "yo ai ingaya maki mahaifiyarsa ma wlh karshece wurin kyau bafulatana ce ta usili ingaya maku,don babu abunda fafa zai nuna mata wlh"
Teema tace "kai wayyo Allah na Allah kasa ya bayyana inhar yana raye"
Sakina tace "ni wlh inaji ajikina yana raye saboda nasan Allah yama son nuna ma mammah kuskurenta tun aduniya shiyasa zai barsa da ransa."
Salma tace "kafin yayi zuciya ya fasa ganin mu kutashi muje"
Teema tace "wayyo na manta yace na tabbatar nakira mammah bari naje"
Ta ruga dayan upstairs d'in don kiranta.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now