*NERNER AYSHER*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3561🅿️..........11
"Nanah har sai yaushe kike ganin ya dace ki koma makaranta?baki tunanin shekara da kikai zata roshe?"
Ina kwance cikin doguwar kujera ina chat da hamid yana sanar dani zaizo gobe,hankalina na kan wayar nace mata "Mami nifa tunanin da nake zan ajiye karatun nan ne kawai."
Cike da mamaki mamin ke kallonta tace "ban gane zaki ajiye karatu ba,wai ko kin mance sauranki wata biyar ne gabad'aya."
Na b'ata fuska ina juya mata baya nace "Mami inajin Aure zanyi,saboda hamid ya sanar dani gidansu an matsa yafitar da mata,shiyasa kawai naga yadace muyi auren saina koma baya."
Wani irin fad'uwar gaba mami taji tabbas akwai matsala akwai rikici inhar nanah tasan da auren nana,shiyasa rannan ta matsanta akan akirata asanar da ita amman mus'ab yace aa ba yanxu ba,gashinan tana so ta d'auko wata babbar magana.Cikin damuwa mamin tace "Amman Nanah kinsan da cewar Abbunki ya fitar maki da miji,nai tunanin zuwa yanxu zaki hakura da hamid d'in naki domin cika wasiyyar mahaifinki."
Saurin tashi nai zaune raina b'ace gabana yana fad'uwa shaf ni nama mance da wata magana makamanciyar wannan,kamar zan kuka nace "mami wallahi ni nama manta da wannan maganar,saboda bana jin zan iya hkr da hamid,mami hamid shine buri na shine type d'ina taya kike tunanin xan iya hkr dashi na iya rayuwa da wani gaja k'azami.............daidai shigowarsa kenan yakejin munanan kalaman da take fad'a akansa.
Had'a ido mukai dashi yana tsaye bakin k'ofa ya rungume hannunsa ga kirji yana kallona ido cikin ido,wani irin fad'uwar gaba naji nai saurin daina kallonsa ina yan motse motse.
Mami ta juya tana kallosa daga yana yin fuskarsa zaka tabbatar da yaji abunda Nanah ta fad'a,kuma ransa ya b'aci ainun.
Sofy ce ta shigo da sallama yajuya yana ansa mata sallamar,kallonsa tai cikin tashin walwala tace "yaya ina wuni."
Asanyaye ya ansa mata inba dan tana kusada shi ba bazata ji bama.
Shigowa falon tayi tana ajiye jakarta gefen mami,sanan ta matso jikinta cikin shagwab'a tace "Mami yunwa nakeji wlh yau fa tunda muka shiga lecture tun 1 sai yanxu hud'u na yamma"
Tace "tashi kije kiyi wanka sai ki fito kici abincin sannu safiyya, Amman fara zuboma yayanku kafin kiwuce.”
Tashi tai ta nufi kitchen d'in ba tare data kalli yayar tata ba,don duk sadda ta kalleta wani zafin kishi takeji akanta.Karasowa yayi cikin falon yana zama tare da mik'a ma momy wasu takaddu muryarsa ba walwala yace "gashinan mun samu babban filin da zai wada ayi ginin,insha Allah cikin satin nan za'a fara in akai sa'a ma kiga angama sa cikin wata guda."
Ansa tai tana dubawa tace "Masha Allah sannu mus'ab Allah yayi maka Albarka ya saka maka da alkairi."
Yana jingina da kujerar ya d'an lumshe idonsa kadan sannan yace "Ameen Mami."
Sofy ce ta karaso da tirw d'in abincin ta ajiye gabansa,sannan ta xuba masa had'ad'd'ar shinkaface fried rice ce tasha nama zuk'u zuk'u aciki da veges aciki,sai coleslaw da juice na coconut.
Kalon juna sukai ya sakar mata murmushi ta b'ata fuska tana turo baki sannan ta juya tabar falon.Saurin tashi nima nai zan bar wajen don nakasa sukuni da kallon da gake jifata dashi............"dawo nan"
Naji muryarsa da kaushi ta katseni rass gabana ya sake fad'uwa juyowa nai ba tare dana dawo ba na b'ata rai nace "mezan maka in nadawo inada abunyi aciki."
D'aure fuskarsa yayi tamau cikin bada umurni yace "nace ki dawo nan kafin ranki yayi mummunan b'aci."
Ina huci na dawo afusace na zauna ina b'ata rai.Abincinsa ya fara ci cikin natsuwa suna magana da mami akan yadda aikin ginin restaurant d'in zai kasance,da yake bayan komi ya lafa da rabon gadon suka zauna shida mami suka yanke shawarar bude restaurant babba yadda at least dai akwai ta inda kud'i zasu ringa shigowa,tunda company nanah baya aiki yanzu sai ansake uploading d'insa
Yana da burin ya cigaba da aiki amman sai nan gaba saboda yana bukatar kudade masu yawan gaske.Raina tafasa kawai yake ganin kamar baisan ma da zama na awajen ba,hirarsu kawai suke da mami na kasa hkr kuma atunxure nake komi zan iya fad'a,saidai abunda kawai yake mun cikas inhar na tuna kalaman Abbu akaina da alkawarin danai masa,amman wannan bashi zai saka nasa masa ido yaringa juyani kamar waina masa ba,bazai yuwu ba.
Cikin fushi da b'acin rai nace "malam ya zaka zaunar dani ka banzatar dani bacin na ce maka inada abunyi."
Wani irin d'ago idanunsa yayi ya zuba mani su saida zuciyata ta buga,nai saurin dauke idona ina cewa araina "dalla can daina kallona da wad'anan mayun idanun naka."(lol😂)Ruwa yasha ya ajiye kafin yace "kishirya zaki koma makaranta gobe insha Allahu."
Cikin mamaki da maganarsa nake masa wani irin kallo ina zaro idanuna nace "makaranta kace?uhmm to ni bazan koma makaranta ba mami ki masa bayani."
Murmushi mamin tayi tace "Aa badani ba nanah wak'a bakin mai ita tafi dadi."
Huci na fesar ina kauda kai gefe ina jin yadda raina ke suya,wai me guy d'in nan yake nufi dani ne.
Kafarsa d'aya ya dora kan d'aya yana tsareni da wadannan idanun yace "baki da dalilin dayasa baxaki koma sch ba Aysher,tunda har kika fara to insha Allahu saikin karashe da Amman inhar akwai uxirin da zai hana ki koma wa inajinki."
Motsa baki nake amman na rasa abunda zance sai fidda hucin bacin rai nake,gutun tsaki yaja yace "bakida dalilin kenan don haka kishirya gobe insha Allah zan kaiki makaranta don yanxu haka kuna gaf da exams,dole kije ki gyara abubuwan da kika rasa na one month."
Ya tashi zai fita muryata kiris nai kuka saboda dai raina amugun b'ace yake,nima tashin nai afusace nace "kai nifa nagaji da wannan ikon da kake akain tunda ba haihuwata kai ba,karatu ai nice dai keyi ko to nace bazan ba *Aure zanyi.*"
Cak ya tsaya da tafiyar da yake kafin yayi wani irin u turn yana dire idanuwansa akaina,duk da yadda gabana yake dukan uku uku har ina wata yar kerma saboda shakkarsa da tsoron sa da nakeji.
Fuskarsa tamau yace "mekikace? maimaita inji?"
Duk na rikice amman ina kokarin karfafa kaina da niyyar nuna masa cewar bai isa ya ringa juyani ba.
Ina rawar baki na ce"na.....nac...nace ni baz....bazan koma makaranta ba Au...aure zanyi,hamid zan aure don shine wanda ya dace da rayuwata."Mami dai kallonsu take bata son saka baki so take ya koya mata hankali tunda har yau ita batasan Annabi yafaku ba.
Takowa yake yana dawowa cikin falon,direct inda nake yake nufowa ai dan danan na rikice na rud'e ina rawar d'ari,ja baya na farayi ina zazzaro idani cike da tsoro.
Biyonin yai tayi fuskarsa ta canza saboda b'acin rai saida ya direni jikin bango ya matsoni sosai yadda har takai munajin numfashin juna,zuciyata babu Abunda take sai dokawa.
Idonsa cikin nawa cikin dakakkar murya yace "badai zaki koma makaranta ba right?hakan yayi Amman ki sani bake babu wani Aure daga nan har iyakar karshen rayuwarki *SABODA NINE MIJINKI,KUMA AURENA DAKE AUREN ZOBE NE BABU SAKI DON HAKA KI GAGGAUTA SALLAMAR WANNAN GUY D'IN KAFIN KI FUSKANCI MUMMUNAN B'ACIN RAINA*Ya dalla mun wata muguwar harara kafin ya nufi k'ofar ficewa daga falon cikin mazan taka,kafin kice me harya fice saidai sassanyen k'amshinsa da zakaji..............
Silalewa kasa nai na saka wani irin kuka wanda naketa dannewa azuciyata,sosai nake kukan saboda bazan iya kwatanta halin da zuciyata take ciki ba.
*zuwa anjima zan sake wani posting din insha Allah.*
Mom muhseen ✍🏻
09034722970 its my no.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...