*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️.........40
mun isa karfe sha ɗaya na safe da yake hanyar mai ƙyau ce ba wani gajiya tattare damu sosai,saida mani ya huta yaci abinci sannan ya juyo munyi waya da mami mun iso ta sake mana nasiha sosai sannan muka kashe,inason na kirasa wata zuciyar tana hanani kan dole yasa na hkr ban kirasa ban ba,muka shigar hidimar shirin bridek shower anyi anko ba laifi kuma ƙawayen mu duj sunxo wasila ma tazo nan muka had'u aka ringa ashiririta da tsokanar amarya,aiko me zatai ba kuka ba tun muna dariya har muka tsorata don kamar zata shiɗe haka takeyi,nan muka shiga lallashinta daker aka samu tayi shiru kafin aka fara shirin tafiya bridel ankon da tayi mani na saka doguwar riga munyi kyau sosai aka kira photographer ya ringa kashe mana kala sofy ma tayi kyau sosai mune bamu tashi ba sai ana kiran sallar magriba,wasu da zasu koma gida tuni sun koma wasu kuma anan zasu kwana sai jibi idan an daura aure a wuce kano kai amarya.
Muna d'akin Nabla munyi wanka muna fira ga cake nan da cin cin da nama sai meat pie harda samosa da spring rose sai wanda kake ra'ayin ci,cup d'in zallar madarar L&Z ce nake sha cike da nishad'i munata fira harda sofy ga wasila da wata husna Nabla tayi ta gumi ta tsurama wuri guda ido.
Anata dariya ita kamar bata wurin nice na ankare da ita na sauko gadon na isa wurinta nace "Nabla don Allah ki sawa rayuwarki ruwan sanyi,ki d'auka hakan shine mafi alkairinki duk abunda kika ga Allah yayi mai kyaune,mezai hana ba zaki dauki darasi akaina ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Nanah ba abunda kike tunani bane,mamaki ne nan yake cina kinsan jiya fadila tazo har gidan nan?"
Da mugun mamaki nake kallonta nace "fadila kikace!"
Ta jinjina kai tana cewa "in kika ga fadila sai kin kusa zubda mata hawaye,fadila ta fige ta lalace nake gaya maki tayi bak'i duk farin fadila wlh ta dahe da kuka ta rungumeni tana cewa na yafe mata nace aini batai mani komi ba,inma akwai wanda tayi ma laifi to kece shine tace bazata iya had'uwa dake ba nace ki yafe mata,wai ashe auren su hamid wata hud'u ya saketa yanxu haka kusan sati biyu kenan yayi wani auren,inkinji matsalar da fadila take ciki abun gwanin ban tausayi."
"Wlh Nanah na sare da duniyar nan,duk abunda kake kaji tsoron Allah shiyasa duk nasha jinin jikina,ba dan komi nayi wannan kukan ba d'axun sai don tuna irin wulakancin da nake wa jamil,da irin abunda nai tayi kan auren nan,ni duk tsoro ma ya kamani kar Allah ya kamani nan gaba na san bazanji dadi ba,wlh hankalina tashe yake."
Hannunta na kama muka dawo bakin gado na soma goge mata kwallarta nace "karki saka damuwa aranki ta yi maki illa,tunda har kinsan kiyi kuskure baya yanxu kuma kin gane kuskuren ki saiki gyara,fadila kuma ni tuni na ma mance da me ya had'amu wlh saboda sai yanxu nake ganin Allah gata yayi mani,yana sona da rahmarsa yasa ya had'ani da musab,kuma ina rok'on abunda nayi baya ya yafe mun.kedai kiyi zaman aurenki cikin lumana karkiyi abunda ransu mama da dady zai b'aci dake suyi fushi dake............duk muka had'u mukai ta mata nasiha da kwantar mata da hankali,sofy mamaki kamar ya kasheta wai yau yaya nanace ke yima wani fad'a da nasiha?lallai ta yarda ta natsu kuma ta gyaru.Anyi bikin Nabla cikin kwanciyar hankali amarya tasha kyau sosai amma kuma tasha kuka kamar ba gobe,nasiha tasha wurin dangin mama kamar kamarme ni da nakaita ni kaina nasha jinin jikina,yadda suke girmama kula da miji da hak'ok'insa da illar bijiremasa ta kowace fuska ai sai hankalina ya tashi,sai gani ina share kwallah bacin da ni nake sharewa amaryar.
Wannan fad'a ya shigeni ya ratsani ya dakusar da duk wasu makamai na dana d'auka,jikina yai bala'in saki haka aka fiddo Nabla don kaita gidan mijinta jamil,koda aka biya da ita wurin dady cewa yayi "ni duk abunda kikai mun Nabila na yafe maki amman ki sani muddin ki ka kashe auren nan wlh tallahi babuni babu ke,kiyi biyayya ga mijinki ki rik'e gidanki ki kula da shi ki kwantar da kanki garesa shine zai saka nayi alfahari dake,na kuma dawwama ina saka maki albarka,idan har shi namiji ya kauka kai ya jure wannan auren had'in ke da kike mace bazaki iya hkr ba?to ni kinji abunda zai saka nayi fushi dake in har zakije ki zauna lfy da mijinki da yan uwansa wlh hakan zaifi komi sani farin ciki,Allah yasa albarka a aurenku ya baku hkr da juna ya azurtaku da zuri'a d'ayyiba"
Kuka riris haka Nabla take duk fuskarta tayi ja karma ace idonta gurzar kuka kawai take haka aka sata mota,kanen dadynta da wasu yayyun mama da goggonsu yayar dady,
Motarsu ta fara yin gaba kafin ta saura ta bisu baya,duk bana cikin natsuwa sosai tunda muka zo na kashe wayata don nasan yaya musab dole zaita kirana ni kuma aganina ban gama wahalar dashi ba,muna cikin motar wani abokin jamil daga ni sai sofy da wasila zamu isa kanon na fiddo wayata na kunna gabana yana fad'uwa,saboda tuna wata magana da naji wata daga cikin yan uwan maman nabila ta fad'a da ana mata nasiha cewa.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...