part12

97 13 0
                                    

*NERNER AYSHER*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3561

🅿️..........12

Mami ce ta karaso inda nake tana kamoni jikinta na fixge ina shashsheka raina yai matukar mugun b'aci ina rawar murya nace.

“ki kyaleni ba ruwanki dani,agaban ki yake mun duk cin mutuncin daya gadama,har yana maganar shine mijina auren zobe ne babu saki gidan ubanshi ya auran d'in,don takamarsa Abbu yace yabashi ni bashi zai saka na aurai ba,wlh tallahi bazan tab'a aurensa ba saidai duk abunda zaiyyi yayi."

Mami tace "mus'ab d'in kike zagi nanah?kinsan kuwa girman darajarsa awajenki yanxu har kike bud'e baki kina zaginsa,da nace bazan sanar dake ba saboda ki kara samun natsuwar da zaki fuskanci abunda yake gabanki,amman tunda naga abun naki harda rashin hankali bari kiji abunda baki sani ba,mus'ab d'in dakika raina kike ganin shi bakomi ba,kike masa kallon makaskanci ayau bakida wani wanda yakaisa *Domin kuwa Andaura Aurenki da shi wata biyu kenan*."

D'ifff naji kukan nawa ya tsaya na bud'e dukan idanuna ina kallonta kamar yau nafara ganinta,taci gaba da cewa cikin fad'a saboda yau nanah ta kaita karshe.

"Don haka kisan abunda kikeyi duk duniya babu wanda yafiye maki shi ayanxu,kuma Aljannarki atafin kafarsa take idan kinyi Abun da yadace kishiga inkinyi hauka gaki can Wuta Allah ya kyauta,don Haka ni iyakata dake na nusar dake tare da yimaki nasiha,idan kinyi daidai daba daidai."

Wani irin numfashi naja a mugun gigice nace "Aa.....wallahi ba gaskiya bane,banyarda ba bazan tab'a yarda ba wlh tallahi nafi karfin aurensa,da ajina da komi bazan kare ga drivern gidanmu,narantse da Allah bazan yarda ba bazai yuwu waye wani mus'ab zaku ma fadan gaskiya."

Sofy ce ta fito idonta alamun bacci take hayaniyar tatasheta,tace "mami lfy?meke faruwa?yaya nanah meyafaru don Allah."
Mami tazo ta wuce ciki tabarsu nan saboda ranta yab'aci ainun,sofy ta karasa wajenta tana rungumota saboda kukan da take.

"Yaya nanah menene don Allah."

Cikin kukan nace mata "sofy wai don Allah an daura mun aure da mus'ab?don Allah kice mun karya ne ba gaskiya ba,karki gaya mun an daura mun aure dashi zan iya mutuwa wlh,saboda bana son sa bana kaunar ganinsa.............
Na cigaba da kukan kaina yana bisan kafad'arta,shiru sofy tayi tanajin bugun zuciyarta mamaki na cika mata zuciya.
Yah mus'ab d'in yaya nana ke kuka an daura mata aure dashi?kukan bakin ciki take bana farin ciki ba,innalillahi inama nice na samu wannan damar inama auren nan zai dawo kaina bana jin akwai wadda ta sa'a kamata.
Jinjina kai tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "kiyi hkr yaya nanah tabbas yaya mus'ab ya zama mijinki wanda shariar muslunci ta dora dukkan sharrudan aure akanki.........."
Da karfi na turata ina mik'ewa hawaye jage jage nace "karya kuke yi,meyasa ni Abbun bai gaya mun ba sai ku?wallahi karya ne hakan bazai tab'a yuwu wa ba............na wuce fuuuu natai dakina kamar xan kifa saboda d'imaucewa dajin wannan sabon labarin mai gigita kwalwata.

Sofy ta bita kallo cike da mamakinta da ganin sakaci da wauta,jinjina kai tayi tace "yaya nanah kina wasa da damarki,Amman nasan tabbas nan gaba zakiyi dana sani ba kad'an ba."

*****
Misalin karfe d'aya da rabi na dare suka samu hanyar shigowa gidan,ta bango suka fasa suka shigo saboda ta ko ina gidan akwai tsaro,saman katangun duk wayace mai shocking.
Tunda aka fara bugun bangon ya farka daman lokacin tashinsa ne yayi nayin nafilfilunsa,wannan bugun duk ya tada masa hankali matuk'a kafin ya gama tantance ainahin abunda yake faruwa mai gadi ya rugu adari da hamsin yana shashsheka da huttai yabanka d'akinsa yace "mus'ab barayi mun shiga uku wlh gasu can sune suke dukan bango zasu shigo,nikam cikina ya katsa ya zamuyi"

" innalillahi wa inna ilaihir raju'un."

Abunda mus'ab yake fad'a yana nanata wa kenan,jikin shazali mai gadi rawa kawai sai kar karwa yake yaje jikin bango ya lafe.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now