part 31

133 17 12
                                    

*_NANAH AYSHA_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........31

Hannunsa kawai ya ke cusawa cikin gashin kansa jiyake kamar zai haukace,yarinyar nan ajinta yayi yawa ya tabbata inhar ba shi ya fara magana ba to bazata ce masa uffan ba,har mamakin kansa yake yadda duk ya susuce akanta.
Gyara kwanciya yayi yana sassauta muryarsa yace "Aysha"
Lumshe idona nayi can kasa na sauke ajiyar zuciya ba tare dana bude bakina ba nace "uhmm"
Wani marayan numfashi ya sake saukewa yace "how are u"
Sake dunk'ulewa nai guri guda nace "I'm fine"
Murmushi ya saki ba tare daya shirya ba yadda tai maganar cike da shagwab'a baya tunanin ma tasan tayi,sai yace "Are u sure u are ok"
Na d'aga kaina kamar gana gabana yasake cewa "kinji yar gidan mami"
Dan murmushi nayi ina cewa "uhm I'm ok"
Mirginawa yayi yana jin kamar yana shawagi ya sake sassauta muryarsa yace "kinyi kewata kuwa?"
Saurin bud'e idona nayi nace "miye kewa?"
Yace "i mean are u missing me"
Hararar wayar nayi nace "oho I don't know"
Murmushi ya sauke yace "bazaki iya gane kinyi kewata ko bakiyi ba."
Nace "eh bazan iya ganewa ba,kuma ma akan me zanyi kewarka ai nadauka mutun yana kewar wanda ya damu dashine?"
Sauke numfashi yayi yana sake sanyaya muryarsa yace "kinsan yadda na damu dake kuwa."
Wani abu naji har cikin raina na runtse idona nak'i cewa komi,ya sake cewa "nikuma kinga duk da baki damu dani ba nayi kewar abubuwa da yawa daga gareki."
Jinai kamar zan narke asaman gadon,nace "like?"
Yace "kina son ji ne?"
Na bata fuska nace "in kaji kana iya fad'a ka fad'a mun."
Murmushi kawai yake yana imagining yadda bakinta yake yi idan tana magana,taita motsashi kamar na yan yara.
Yace "I miss ur eyes yadda kike harararta."
Na zaro idona nace "nice ma nake hararar taka?"
Yace "yes ke mana,ki rantse baki hararata in muna tare."
Na turo baki kawai nai shiru jiyake kamar zai fasa ihun dadi maganar nan da take masa cike da shagwab'a,shikadai yasan yadda jikinsa yake tsuma.
Yace "naji baki hararata abar wannan,kinji dai ina kewar idanunki ko."
Nace "uhm naji sai me"
Yace yana dan murmushi mai sauti "wannan bakin da kike turosa in zakiyi rashin kunya I miss it"
Bansan sadda nace "laaaaa nice ma nake rashin kunyar,wlh ni ba haka ba."
Dariya yayi da baisan sadda ya tafito ba saurin tashi zaune nayi na jingina da gadon ina tattare kafafuna na dora kaina bisa guiwata sanyin Ac yana ratsani dariyarsa ba karamin dadi tai mun ba,ina ma zaiyi ta in muna tare.
Jinai ya sake cewa "ki rantse baki rashin kunya,"
Nai shiru nak'i cewa komi nai lamo ina saurarensa yace "dake nake nace ki rantse"
Na turo bakina nace "aida adane ko."
Ya girgiza kai yace "aidai kinyi kuma nine zan shaida hakan,don ansha yi mun buhu buhu."
Cike da shagwab'a nace masa "nidai kadaina maganar nan to ba ya wuce ba ehy"
Lumshe idonsa yayi saboda wannan abun da take yana bashi wani yana yi dake tsumasa,can kasa yace "ok na daina,intsaya haka ko incigaba da lissafa maki."
Nace "uhm ni bana so ka daina."
Yace "shikenan kin yarda nayi kewarki"
Ina girgiza kai nace "Aa"
Yace "meyasa baki yarda ba."
Na silale zan kwanta saboda duk na kasa natsuwa sai motse motse nakeyi,yace "menene"
Na narke murya nace "sanyi fa nakeji."
Runtse idonsa ya sake yi yace "ki rufa mana."
Nace "uhmm basai na kashe ba."

"Daman ba sanyin kike ji ba"

Nace "Allah ko inaji"

"To ki rufa ko ki kashe AC"

Remote d'in Ac na lalubo na rage gudunta na ajiye nace "na rage dai"
Yace "ok fad'a mun."
Na b'ata fuska nace "me zan fad'a ma"
"Kibani kabarin sch,da gidan yadidi me dame yafaru"
Nai lamo nak'i magana don nagaji da surutun haka nan,yace "ina jinki fah"
Nace "nifa nagaji da magana bacci ma nake ka kirani."
Shafa kanshi yayi yace "wannan yar maganar ce kingaji,kawai dai kice baki son jina shikenan bari na kira hafsat daman tunda na dawo take kirana."
Jinai gabana ya fad'i zuciyata ta cigaba da bugawa akai akai muryata tai sanyi sosai nace "wacece hafsat?"
Yace "wadda na dauko ranar da zaki dawo kd,tace ma na gaida ki."
Sai naji numfashina ya fara canzawa nace "gidansu kaje zance kenan?"
Duk da yaji canjin murya daga gareta sai ya kasa yardar ma kanshi abunda yake zargi,sai yace "eh naje hira wurinta har mukai magana da babanta yace ya bani duk sadda na shirya sai ayi mgnar aure,koya kika ce gara na fara gaya maki inji shawarar da zaki bani."
Tsikar jikinace tatashi sai kawai naji ruwan hawaye sun silalo mani wani abu ya tsaya mun ga mak'oshina yak'i wucewa,hannu na saka na rufe bakina saboda shashshekata zata iya fitowa yaji.
Jin shirunta yasa gabansa ya fad'i yace "Aysha"
Soke kaina nai kan filo ina kuka can ciki saboda dai nasan nice nake wahalar banza da wofi,taya zan cigaba da dakon wannan wahalar bacin wanda nake donshi yana can wurin wata,gashinan har yana shirin aurenta.
Duk inda hankalinsa yake yai masifar tashi don in har ya natsu sosai kamar kuka take,numfashinta kadai daya saurara ya tabbatar masa da kuka take.
Cikin rawar murya yace "Aysha are u ok?.............afusace nace "pls don't call my name again,sannan karka sake kirana."
Na kashe wayar jikina har tsuma yake na k'udun dune cikin bargon ina kuka son raina,don abunda nakeji a xuciyata inba kukan nayi ba bazan samu sassauci ba,gaskiya wannan ba so bane ni ba haka nayi saba sadda ina tare da hamid,bai tab'a sani kuka ba kullin nidashi cikin farin ciki da annashuwa duk sadda na tuna dashi bana sanin nayi murmushi,amman wannan ko tuna sa nai zuciyata ce take bugawa akai akai idan hangosa nayi gabana zai ta fad'uwa,koda muryarsa najiyo kuwa hakan ce zata faruwa bacin ba haka nakeji akan hamid ba to wai me yake faruwa dani ne...............

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now