part 24

110 10 0
                                    

*_NERNER AYSHER_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........24

Goggo sabira ta tattaro kan yaranta zubaida,harun,dayyaba suka taho nan gidan can bangaren masu aiki suka wuce suka gyara wanu spare daki akwai katifa da fanka sai wadrop ta cikin bango,mami ta kawo masu bed shirt da filo sai bargo da zasu rufa dashi.
Ta kuma kawo masu maganin sauro suka kunna,hawaye sosai goggo keyi saboda dai tasan ta cuci kanta da rayuwarta.
Mutanen da ta cutar gasunan sune suke taimakonta lokacin da ta rasa kowa da komi,meyakai wanan takaici tayi imanin inda sune suka shiga wannan halin suka nemi taimakonsu ba zasu taimaka masu ba,amman gashi sun suturta ta da yaranta marayun Allah.
Babbar yarta zubaida yar shekara goma sha takwas tace "mama kingani ko,sun saka mana da alkairi bacin sharrin da muke binsu dashi kullin,shiyasa nake gaya maki mama ki sassauta kiyayyarki da hasadarki akansu don wataran sune gatanmu,ki duba kiga baba kamilu shine ya dace ace ya dauke mu yayi bakin kokarinsa wajen ganin mun samu wurin zama,amman shine yafara korar mu ya wofi tar damu akofar gida kowa yana kallo,mama don Allah yanxu bakijin kunyarsu."
Kuka kawai goggon keyi tana sharben majina tace "wallahi zubaida inaji ina matukar jin kunyarsu abubuwan da nayi basu da kyau,jinake kamar na mutu na huta."
Zubaidar tace "karkiyi fatan mutuwa yanxu mama Allah ya raya kine don kituba,don haka saiki dage da istigfari shi ai gafururrahim ne mai yawan gafara."
Rungume diyar tata tayi tana kwalla daker suka hkr da koke koken sukaci abinci suka kwanta,daman duk yunwa sukeji duk yinin yau basu saka komi cikin cikinsu ba...........

💐💐💐💐💐💐

           *ABUJA*
*MAITAMA ESTATE*

Wata irin tsawa ya daka mata yayin da idanunsa suka yi fitinennen jaa kansa duk jijiyoyi sun fito b'aro b'aro wata damk'a ya kaima hannunta yai mugun murd'awa har saida yayi k'ara jikinsa yana tsuma yace cikin kakkausar murya.

"Lubabatu ki gaya mun gaskiya ina d'ana yake,bazan tab'a yarda dake ba zuciyata ta kasa yarda dake kin riga kin fallasa kanki,don haka ki gaggauta sanar mun inda d'ana yake domin kece kike da alhakin masaniyar yadda ya salwanta,wallahi tallahi billahil'azim kinji ratsuwar musulmi muddin kwanaki dana d'ibar maki suka cika baki zo mun da wani gamsashshen bayani ba wallahi bazan rantsuwar banza ba saikin kare rayuwarki agidan kurkuku,kin sanni  kinsan halina kinsan abunda zan iya don haka shawara ta rage gareki,kuma zan zuba maki ido cikin gidan nan koda bani nan baki isa ki taka k'afarki awaje ba dani kike bayani,zai kiyi dana sanin sani na ni *SULAIMAN MUSTAPHA JAJI* ya wanca kalar da ita gefe ya wuce upstairs amugun zafafe.
Fad'uwa tayi gefe tana shashsheka tana dafe da kirjinta,dan danan wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska jikinta yahau tsuma yana kerma,sai kurin ta fashe da wani gigitaccen kuka tana cewa.

"Nashiga uku na lalace ni lubah,shikenan asirina ya tonu,shikenan tawa ta kare wlh Fafah bazai kyaleni ba wlh saina shiga ukun da bantab'a tsammani ba,kaicona kaicona da bin son xuciyata wlh nayi dana sani banyi tunanin irin wannan ranar ba,ko kadan ban tab'a kawo cewar fafah zai wulakantani irin haka ba,nashiga uku ina zan saka raina tawa ta sameni..........ta sake rushewa da kuka sosai tana shashsheka teema ce take saukowa daga dayan upstars d'in dake gefen dama kasan cewar benen kashi biyu ne akwai na gefen dama dana hagu,ita na hagun take saukowa agaggauce hango mammah su tana kuka mai cike da tashin hankali.
Durk'usawa tayi agabanta tana jijjigata cikin damuwa da tashin hankali tace "mamma!mamma!!meyafaru?kuka fa kike don Allah kiyi shiru ki gaya mani abunda yake faruwa na dade ban ganki cikin wannan tashin hankalin ba,don Allah mamma kiyi shiru kiyi mun bayan."
Ta karashe tana kukan itama don iyakar saninta bata tab'a ganin kwalla idon mammah su ba,cikin kukan tace mata "fatima fafah ne,fafan ku ne silar shigata wannan tashin hankalin."
Da sauri tace "mammah fafah kuma?mekika masa haka?fafah dake gudun dukkan bacin ranki yake neman duk abunda zai saki farin ciki?mamma kiyi mun bayanin dazan iya dauka fafah bazai saki kuka da gangan ba kinyi masa wani mummunan abunne."
Dagowa tayi tana kallon yar tata don ta fad'i gaskiya don ko makaho ya zauna cikinsu zai shaida irin kauna da soyayyar da fafah yake mata,da irin tattali da ji da ita da yake amman yau an wayi gari ta jawo silar da ya wulakanta ta darajarta da martabarta suka zube kasa wanwar,share shawayen take wasu suna fitowa tace "fatima labarin yana da tsayi,idan na samu natsuwa zan sanar daku komi amman sai kun taru kuduka keda yayyunki."
Teema tai shiru tana sauraren mammah tace "mammah akwai wani labari da bamu san dashi ba atattare dake."
Jinjina kai tayi tace "tabbas akwai labarin da nake b'oyewa babu wanda ya sanshi dagani sai wata qawata *RASHIDA* sai Allah daya halicce mu,ahalin yanxu ban san inda rashida take ba tun bayan aurenta don haka shiyasa labarin bai fallasa ba har yanxu."
Jinjina kai teema tayi tace "mammah na k'osa naji wane labari ne wannan,mezai hana na kirasu Anty rumanah duk mu had'u yau ki sanar damu."
Girgiza kai tayi tace "bana cikin natsuwa fatima,don haka kubari na samu lokaci tukun,tashi kije ki shirya table nasan fafah ku bazai ci wani abuba daren yau saboda yashiga halin da ya dade rabon da yashigesa tsawon shekaru."
Tashi teema tayi tana wucewa hanyar kitchen don aikata abunda aka sata amman zuciyarta cike da d'okin jin wane labarine mammah take son sanar dasu,wanda tun kafin kajisa kasan akwai sark'ak'k'iya acikinsa.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now