*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)*Last page*
*Laifin dadi kare wa*Bayan mun gama duk abunda zamuyi da muka shigo,har abinci munci don bama abincin muka ci ba nama ne zallah sai ice cream da youghout sai fruit salad da yace sai na had'a mana,ina turo baki yajani muka je ya taya ni muka gama yasha zuma da uwar madara don shine ma ya matsanta saida aka zuba zumar mai yawa,cikina ya cika tatul ganin inata nishi yasa ya fara mun cakulkuli kan kace me mun haukata falon,dariya nake kamar zan shek'a ai ina samun hanyar guduwa na arce d'akina na rufe kofar inata sauke numfashi bubbuga kofar yake yana cewa "cutie ki bud'e k'ofar nan ko"
Ina shashsheka nace "Allah dear inhar zaka cigaba da mun bazan bud'e ba"
Dariya yake yace "shikenan bazan sake maki ba ki bud'e"
Na shagwab'e ina kukan shagwab'ar nace "nidai gaskiya ban yarda ka rantse ba zaka kara mun chakul kulin ba"
Dariyar yake gana dafe da k'ofar yace "Im very serious love"
Sai sannan na tako nazo na bud'e ina harararshi fixgoni yayi ya had'e da kofar ya jinginani yana tsuramun idonsa narke masa nayi zan silale ya matseni,
"Wayyo dear cikina zai fashe Allah kuwa"
Had'e fuskarmu yayi yana shinshina fuskar tawa murya slowly yace "no my love cikin ki bazai fashe ba,keda nake fatan ki haifa mun twins or three pul."
Zabura nai ina zaro idona nace da kuka kuka "laaaa gaskiya ni aa sunyi yawa ina laifin guda guda dai"
Ban ankare ba naji ya sab'eni yana kallona sai turo baki nake yace "muje part d'ina yau acan zamu kwana saiki lissafa mun yara nawa zaki haifa mun,harma da sunayensu"
Kuka na saka mashi ba hawaye ina cewa "nidai ban yarda ba wayau zaka mun Allah ko...........bakinsa da naji anawa yasa nai tsit ban sake mgn ba yana dariya muka fice daga dakin nawa,can part dinsa muka nufa dakin da naita santinsa ya direni gefen gado yace "bari na d'auko miki kayan bacci yau ni zan shirya ki my love"
Gabana ya fad'i na mak'ure wuri guda daman muna dawowa wanka duk muka fara yi sannan muka zauna cin naman,so yanxu kayan kawai zan canza tun kafin ya dawo zuciyata take zullo ba abunda nake tsoro da ya wuce abunda ya faru jiya,amman inda zai tsaya iyakar romance din to da sauk'i amman ba lallai bane duk na tsure bugawa kawai gabana yake don wlh naji jiki jiya bama kad'an ba,har yanxu inajin zogi awurin don ma yawan shiga ruwan zafi da nake ko agida saida na gasa jikina kusan sau biyu,yanxu ma da muka dawo na kulle toilet din na gasa wurin sosai.........shigowarsa yasa nai saurin kallonsa da kayan da ya d'auko ga hannu zaro ido nayi banma san nace "gaskiya bazan saka wannan rigar ba,wlh fa dear kamar mutum bai saka ba."
Dariya ma ya kamayi yana rungume hannunsa jikin kofa,saida na gama yace "to cutie inbaki saka mani nagani ba wa zaki saka mawa?ninefa mijinki prince dinki kenan ba zaki saka nagani naji dadi ba?lada fa zaki samu cutie na!plsss don Allah karki ce bazaki saka ba ni ita nake son nagani jikinki nasan zata haskaki sosai"
Baki na nake turowa kawai ina murje murje agadon ina motsa bakina alamun ni gaskiya Aa,sai ya langab'e kai yace "shikenan cutie bari na maida tunda bazaki saka ba"
Ya fad'a yana yin kalar tausayi sai naji ban kyauta ba na sadda kaina nace can ciki "ni karka maida zan saka"
Dariyarsa ya b'oye yace "Aa cutie kar in takuraki"Na turo baki ina harararsa sai ya nufoni yana dariya yace "sorry bbyna so nake ki saba dani nan gaba ma babu kaya zakina kwana"
Ai amugun kunyace na tashi zan ruga yai saurin damk'oni ya sa jikinsa yana kyalkyala dariya,daga nan zancen ya soma sauyawa da salo salo da d'aukar d'aukar hankali ya samu ya rabani da kayan jikina,zuwa lokacin ni kaina nasan nahau network sosai don sai shan yaji nake ina makalkaleshi,ga kunnena ya rad'a mun "sweet d'ina asa rigar ko abarshi"
B'oye fuskata nake jikinsa don kunya sosai ta kamani yadda na sakar masa jiki ina taimaka masa akan abunda yake,kasa cewa komi nayi ahankali ya ke samun rigar yana tafiyar dani wata duniya da take dauke hankalina nan take zanjini agajimare ina yawo..........
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...