*NERNER AYSHER*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3561🅿️..........14
Saida nai kwana uku bana fitowa koda falone abinci kansa sai dai su biyoni dashi,daga sofyn har mamin na fice daga sabgoginsa to balle shi karan kad'a miya.
Ko abincin suka kawo mun sai naji yunwa kamar xata kasheni zanci,na bar kwanonin awajen insunga dama suxo su d'auke ko in mai gyara mun d'aki tazo ta dauke.
Na yanke shawarar koma wa sch gobe kuma ban sanar da kowa ba,har zuwa lokacin na kasa sanar da hamid abunda yake faruwa kuma na kasa daina waya dashi,don inhar banjisa ba yini nake kamar wata marar lafiy,nariga na yardar ma kaina cewar hamid shine mutumen da zai iya kawo farinciki cikin rayuwata,hamid shine yasan duk wani kalar mood d'ina dazai sani cikin walwala,shin taya zan mallaki cikon burina?shin idan hamid yasan Akwai auren wani akaina ya zaiyyi.......dole ne nasan hanyar dazanbi don ya sakeni wlh bazan iya zaman aure dashi ba.Akwatina na sauko na fara shirya kayana kasancewar duk agoge suke zuba wa kawai nakeyi,duk abunda ya dace na saka na sa.
On ready ina da sauran kaya can d'akin su nabla,da jakun kunana da takalmomina duk suna can so yanxu kayan sawa kawai na dauka..........kiran hamid ne ya tsineke ni daga gajeren tunanin yadda zan yanke alak'ata da wannan d'an rainin hankalin,ajiyar zuciya nayi ina picking call d'in."Partner kamar kasan kana raina."
Murmushi yayi mun yace "I know I'm in ur mind partner,nasan dai dai da second zuciyarki bazata buga ba tare dani ba."
Sai naji gabana ya fad'i nai murmushi kawai nace "I really miss u partner and I need to see u."
Yace "Inaji kamar nafi son na ganki akan wanda keke mun,idanuna har sun ka ga ganin suffarki jikin wata saboda tsananin kewarki da sukeyi,dana kalli wata sai inga kece nake gani baki ganin ya dace relationship d'inmu ya k'ara matsawa gaba."
Lumshe idona nayi nace cikin sanyin murya "kayakuri partner nima inason hakan,amman dole sai nayi magana agida idan zasu yarda muyi auren kafin na kammala tunda gaka sauran mu five months."
Kamar zai kuka yace "I swear partner nasoma fuskantar barazana daga bangarori da dama,dady ya kaiga fusata akan lamarina,sannan momy tace muddin watan nan yakai karshe ba wata doguwar magana ta rigata zab'ar mun mata,wadda nafi tsana aduniya don Allah kiyi ma mami mgn nasan bazata k'i tsakanin mu ba."
Jinai kwalla sun cika idona muryata da rawa nace "partner kayakuri kasan nima bani da wani buri daya wuce kasancewa dakai arayuwata,tun da na rasa Abbu rayuwata ta juye gabaki d'aya,Abubuwa suka dagule mun hamid ina fuskantar abubuwa agidan nan wanda xuciyata bazata iya cigaba da d'auka ba,shiyasa muddin ban sameka ba inajin guduwa zan............jinai na daskare inda nake yayin da naji tsayuwar mutun bayana,wani turare da ko bacci nake najisa zan gane kowaye awajen.
Dan danan zuciyata ta fara halbawa tsoro fargaba da shakka suka rufeni,nai saurin cire wayar daga kunnena na kashe ina turata cikin rigata ta saman kirjina.
Ras ras kawai gabana yakeyi,amman don karna kama kaina yasa nai dauriya na dake na mik'e ina daure fuskata na jiyo ina cewa "waye xai shigo mun ba sallam.........idanunsa nai karo dasu sunyi tsir akaina yana kare ma fuskata kallo,inzan iya fadar wani abu dangane dashi to kuwa zan iya cewa idanunsa sun iya kerewa mutun kallo idanunsa kamar bana mutane ba in yana kallonka,saboda dai duk yadda ka kai ga gaskiyarka dole ka rikice idan ya tsiro maka su,to balle baka da ita.
Saurin kawar da kaina nayi jikina tsuma yake kawai,nai saurin durk'usawa ina rufe akwatin hannuna rawa yake kawai.
Bakin cikin yadda ya samun tsoronsa kawai nake araina,aduniyata babu wanda na tab'ajin tsoro irin haka ni bana tsoron mutun saidai ni aji nawa,ni Abbu kawai nake shakka shima shakkar b'ata masa rai nake ba irin wannan tsoron da jikina zai ringa kerma ba.
Amman yau gashi nice nake rawar jiki akan wani k'azami driver d'an sunna kawai,na rufe akwatin na tadashi na aje can gefe na rasa abunyi sai kame kame nake,computer na na dauko ina sata jikin bag d'inta.
Kawai saina nufi toilet wanda ina cewa idan na shige wlh ban fitowa har sai yabar d'akin,tunda bana ubansa bane.
Ina aza hannuna saman handle d'in k'ofar bayin naji muryarsa cike da bada umurni tayi so silent yace "come here"
Ras ras gabana keyi kawai ina jawo numfashina daker daker saboda fargaba,amman ban fasa murd'a hannun k'ofar ba.
Wannan karon adake yace "Nace kixo nan karki sake ki shiga toilet d'in nan inba so kike ranki ya b'aci ba."
Kasa shigar nayi na jiyo na dawo can jikin mirrow na tsaya ina kakkauda kai ni ala dole karna had'a ido dashi,daga inda yake yace "bani wayarki"
Afirgice na jiyo ina kallonsa ina yamutsa fuska nace "ban gane inbaka wayata ba?me zakai da wayata"
Kallona kawai yake da idonsa kamar an xuba mai aciki sai shining suke bana son wannan tsinannen kallon ko kad'an.
Yace "karki bari na sake magana mik'o mun wayarki nace."
Hankalina fa ya fara tashi nace "wai......wai don Allah mezakai da ita kaga ni banma san inda takeba."
Guntun murmushi yayi wanda ya fidda sihirtaccen kyawun da Allah yai masa kamar karya daina murmushi saboda yadda yayi ma fuskar tasa ainahin kyau,amman cikin yan seconds ya daure tamau yace "karki raina mun hankali bani wayarki nace karki bari na k'araso inda kike ba dadi zakiji ba."
Matsawa na fara yi hankalina in yayi dubu yai mugun tashi,idan ya raba ni da wayata na shiga uku na lalace.
Ganin bata masa lokaci kawai take yasa yafara takowa xuwa inda take,ai jinai kamar na kurma ihu na ringa matsawa bakina yana rawa nace "kaga miye haka wai,don.....don Allah karka matsoni zan baka."
Tsayawa yayi sannan yace "bani"
Bakina rawa kawai yake da jikina hannuna har karkarwa yake na matsa can har na kai karshe wajen gado nace kamar zan rushe da kuka "ka.......kaga kay......kayi.....hakuri"
Hawaye suka silalo mun saboda dai wannan ne karon na biyu da na bude bakina na bashi hkr,wani d'aci ne yake taso mun daga cikin cikina yana sauka saman halshena.........hawayena kawai ke xuba ni kadai nasan ciwon da nakeji.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...