part 6

101 6 0
                                    

*NERNER AYSHER*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3561

🅿️............6

"Bazan ji dad'i ba kice ruwa kawai zaki sha."
Rausayar dakai nayi nace "sorry shikad'ai ya isan"
Ya kalli fadila yace "sorry friend dinmu kefah what do u want"
Murmushi tayi tana masa wata lank'wasa.
Tace "Aa nima bana buk'atar komi bayan ruwan."
Swan mai sanyi aka kawo masu ya xuba mani da kansa ya mik'o mun yana mun smile,dan kurba nayi na ajiye nace "i hope dai lafiya ka kirani"
Kallon fadila yayi yace "friend ko zaki ara mana few minutes pls"
Ta mik'e tana cewa "oky no problem"
Nabita da kallo don naga kamar abun ya bata haushi,jinai yace "ni zaki kalla ba ita ba."
Sauke masa idanuna nayi masu ban sha'awa ina dan guntun murmshi.
"Ina jinka whats happening hamid"
Lumshe idonsa yayi cikin wani salo yana murmushi kamar bakinsa zai yage.
"I like that name wlh,ban sama haka sunana yake da dadi ba sai idan kin ambaceshi,pls lolly said it again"
Kawar da fuska nayi ina murmushin da ya kubce mun,na sauke kaina kasa ina wasa da yatsuna da suka sha jan lalle,da wuya kaga yatsuna babu lalle ajiki ko na kafafuna,ban cika k'ushi ba ina dadewa ban ba amman su bana barinsu haka nan gaskiya,don yana kara masu kyau.
"Pls mana lolly"
Dagowa nayi nace cikin sanyin murya "oh hamid pls hamid tell me what happen"
K'ura mun ido yayi yana rage sautin maganarsa kamar baya son wani yaji.
Yace "I calling u here because I want tell u something."
nanata kalmar sa ta karshe nayi nace "something?"
Jinjina mun kansa yayi nai ajiyar zuciya nace "ok I'm hear u"
Wani d'an akwati ya fiddo daga cikin aljihun sa ya bud'e sa,wani kaya taccen zobe ne sai daukar ido yake silver color ne da d'an light pink Stone akai,wlh yayi masifar had'uwa.
Hannu ya mik'o mun da na bashi nawa,ban masa musu ba na bashi.
Yatsata ta kusada d'an karamin ya saka mun,sai kuma yashige ba yawa ba kad'an.
Kallon juna mukai idonsa har wani love color yake fitarwa muryarsa da sanyi tana ratsani yace "I love u❤ lolly,my heart is beating because of you,I will be ur mine ever and ever pls lolly are u love and will u marry me??"
Anshe hannuna nayi da yaketa lailaya gaba d'aya soyayyarsa datake dan k'are acikin jikina take mun yawo ajiki.
Hamid ya iya bayyana soyayya,bana jin zan samu namiji kamarsa da ya iya sarrafa love d'insa.
Kasa magana nayi saboda bakina yayi nauyi,kuma ba aji bane daga anfurta maki so ki wani ansa.
Makale kafad'a ta nayi nace "ni bazan aureka ba"
Zaro idonsa yayi masu rud'ani yace "pls lolly don't say that idan kina fadar haka zuciyaya zata iya fitowa waje."
Dariya nayi masa nace "haba saika ce ba namiji ba."
Murmushi yayi yana ajiyar zuciya yace "akanki ai bana gane nid'in ko waye lolly kice kina sona don Allah."
Girgiza kai nayi nace "sai nayi tunani"
Kamar zai kuka "for how long lolly pls karki saka na kasa aikata komi idan nakoma wajen aiki."
Dariya nake masa nace "its just 2 to 3 weeks."
Dafe kirjinsa yayi yace "wlh lokacin kila ina gadon asibiti."
Dariya yabani saboda yadda yake acting d'in kamar ciwon lokacine ya kamasa.
Ba yadda baiba akan na rage kwanakin,daker na barshi a one week.
Bamu bar wajen ba sai akai la'asar,kamar bazamu rabu ba ahaka ya wuce abuja muka yo makaranta.
Muna isa sofy ta kirani awaya ina ganin kiran naji gabana ya yanke ya fad'i jikina yayi mugun sanyi na d'aga kiran "sweeety.........kukanta ya katse mun maganar dake bakina.
"Yaya nanah muna cikin tashin hankali!,yaya nanah Abbu yana kwance asibiti rai hannun Allah,yaya nanah kitaho kigansa tsoro nakeji kar mu rasa Abbu!"
Ai ban san sadda nima kukan ya kubce mun ba ban samu damar mayar mata da ansa ba,na kashe wayar na zauna darshen bakin block din mu ina kuka bilhakki da gaskiya,hankalina yayi kololuwar tashi nai zunbur na mik'e jikina wata irin rawa yake,na fizgi jakata fadila ta biyoni cikin damuwa.
"Ina zaki nanah, ki tsaya meya faru don Allah ki tsaya kimun."
Nabla ta fito class ta hango abunda yake faruwa,binyoni tai aguje ta rik'eni tana sani cikin jikinta saboda yadda taga ina kerma.
"Innalillahi nanah whats wrong with u,kimana bayani kibar kuka."
Ina shashsheka ina cewa "nab...nabla Ab.....Abbunah....Abbu nah ne zai mutu!!bashi da lafiya,yan.....yanxu sweety ta kirani.bazan iya zama ba kano zan tafi,nabla kano zan tafi".......na sake rushewa da kuka.
Fadila tace "tafiyarki kano yanxu ke d'aya akwai matsala nanah,nabla in zaki kishirya sai mu kaita ya kikace."
Tace "haka ne fadila rik'eta bari naje na dauko mana kaya ko kala uku ne."
Zama mukai da fadila nan inda motata take,nabila tatafi hostel don dauko masu kaya.......

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now