part 47

144 15 0
                                    

*_NANAH AYSHA_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........47

Saurin tashi nayi daga jikinsa ina waige waige ko wani yana ganin mu narke murya nayi ina shagwab'e fuska nace "wayyo Allah na wlh bazan iya binka ba kaya kuri"
Idonsa sun kankance ya rik'o hannuna kamar zai kuka yace "wlh babu abunda zan maki kiyarda dani kawai dai ina son na kad'aice dake ne"
Muryata da sanyi nace "yanxu ma fa saida mami tace in sauri indawo don Allah yaya kaya kuri jibine fah"
Sakin hannuna yayi ransa yai masa ba dadi muryarsa ta d'an dishi yace "cutie kardai kice mun tsorona kikeji?wlh bazan cutar dake ba amman tunda baki yarda ba muje to na rakaki d'aki"
Tausayinsa naji ya mugun kamani kamar zan kuka nace "wallahi yaya mami fad'a zatai mun kaya kuri"
Jawoni yayi jikinsa yana shafa kaina yace "shikenan karkiyi kuka muje"
Yana rik'e da hannuna muka shigo main falon yadidi da mami sai fadila da sofy duk suna falon,goggo sabira ma tazo har sai an gama hidima zasu koma ita da yaran,zulaiha na gefen sofy suna wani abu cikin waya sallama yayi duk suka jiyo kanmu kowa idonsa kanmu,nai sauri sadda kaina ina kokarin anshe hannuna amman ya rik'esa gam yadidi tace "iyyye daga ina kuke?ke ban maki kashedin fita ba"
Kafin ma nace wani abu ya rigani yace "yadidi wai sai kuyita kulleta d'aki kowa yana shan iskansa ita tana can k'umshe,don Allah nidai kubarta ta sha iska haka nan"
Ai sai kowa ya hangame baki yadidi ta tsuru tana kallonsa mami murmushi kawai take tana danna wayarta goggo sabira ma dariya take ita dasu sofy.
Yadidin tace "Au Allah!to ai shikenan sai tazo mu zauna tunda baka son ana kulleta d'aki"
Yana murmushi yace "yadidi saboda Allah fa"
Jinjina kai kawai take bata san rashin ta idonsa yakai haka ba,da tana yabonsa sallah ashe dai shima gwanine.
Had'a ido mukai da ita nai saurin soke kai tace "d'ago kai ki kalleni yarinya bar wani soke kai."
Kamar zan kuka nace "yadidi awaje fa muka had'u wlh,ga kuma sofy da fadila nan ki tambayesu nabla naje rakawa sai gashi awurin"
Tab'e baki tayi tace "oho maku inkunyi hkr dai jibine in Allah ya kaimu tana fadar haka tatashi tayi ciki."
Ai sai naji kunya tayi kamar ta kasheni ina dira k'afafu na sai na saka kuka,me zasuyi mun ba dariya ba mami tace "ban son sakarci zaku b'ace mun da gani ko sai ranku ya b'aci marasa kunyar banza"
Mus'ab yana yar dariya yace "mami yanxu nan miye na rashin kuny........zaku wuce kokuwa?"
Yana ta kunshe dariyarsa su sofy na yi mana na dalla masu harara najiya jani kurin bai direni ko ina ba sai d'akina na haye gadon ina kukan shagwab'a.

Rungume hannunsa yayi ga kirji yana kallonta saboda dai gaba ki d'aya ta rikita masa lissafinsa,kwata kwata ji yake kamar notikansa suna kuncewa.
Wai har yaushe cutien sa ta koma haka?duk acikin sati guda kenan?lallai ko wacece wannan gwanace
(08065662450 masu buk'atar gyaran jiki suna iya tuntub'ar wannan no d'in gwanace ta kowane fanni,don da salonta nake amfani wajen gyaran jikin nanah,ina mai tabbatar muku da cewar inhar kika siyi kayanta na gyara saikin saka mata albarka,akwai mayuka na shafawa akwai sabulai na tsarki dana wanka,akwai humrori kai inhar ma kina bukatar ki sameta aimiki gyaran jiki cike da waje wlh ina mai tabbatar miki zaki sha mamakin kanki,tana nan akano zaku iya samunta in kukai contacting dinta ga no dinta nan gamai buk'ata 08065662450)

Sadda yaji fatarta ta had'u da tashi dan danan tsikar jikinsa ta mik'e abunda ma yafi saurin d'imautashi bai wuce masifaffen k'amshin da take ba,har bakinta idan ta bud'e tana magana wani sassanyen k'amshi ne yake fitowa,mafarin yace suje d'akinsa ko yaya ya d'an rage zafi amman yasan inhar ya tab'ata awannan karon kuwa baxai iya hkr ba,komi zai iya faruwa shiyasa ya hkr ai jibine shikenan kuma.

Numfashi yaja ahankali ya zauna bakin gadon yana cewa ca k'asan mak'oshinsa "Cutie wannan kukan da kike yana dagulamun lissafi fa,in kika cigaba dayi ina saurare bazan iya rik'e kaina ba"
Ai jinayi nayi d'ib kukan ya tsaya ina zare ido da kaina yake cikin guiwowina,murmushi yayi yace silently"Cutie bazan iya kwatanta miki irin kyan da kikai ba wlh,duk yadda zan fasalta miki bazai kai maki yadda nake gani ba,ko wacece wannan mai gyaran dole zan sake mata wani biyan na musamman"
Shiru nayi ina saurarensa yadda yake canza salon muryarsa kadai yake fixgata sosai muryarsa take ratsa kunnuwana tana haifar mun da wani sabon yanayi marar misaltuwa,jinsa nai kusadani sosai bakinsa wurin kunnena yace da wata kalar murya mai rikita duk wadda ake mawa.
"Plsss Cutie karki haukatani don Allah,wlh yanxu haka jina nake ba daidai ba."
Da sauri na d'ago ina kallonsa idonmu ya shiga cikin na juna,wani irin feelings suka taso mun kewarsa naji tana ratsa dukkan gangar jikina,kamar na fad'a jikinsa na rungumesa yana yin da nakejina ahalin yanxu bazai kwatantu ba,saboda ni kaina nasan na gyaru kuma akan guiwa nake
Shiyasa nake tsoron mu kad'aice.
Hure mun ido yayi na lumshe su na bude na sake sauke su akanshi,murmushi mai tsananin kyau yayi mun yace "Pls my princess ina neman alfarmarki."
Sake lumshe idona nayi saboda ji nake murarsa kamar yana reramun wata sarewa cikin kunnena daker na iya cewa "uhmm inajinka to"
Goga mun hancinsa yayi yace "Don Allah Cutie karki mun rowar jikinki karki hanani morar ni'imarki,inkika mun haka raina bazai dadi ba,zuciyata zata k'untata gara na gaya maki don kar zuciyarki ta sak'a miki yin hakan,kin san dai I LOVE U ko?"
Na k'asa da kaina na d'aga kai ya sake cewa "to son da nake maki bazai bari na cutar dake ba nai miki alk'awarin haka"
Shiru nai saboda jin yadda gabana yake fad'uwa tsakani da Allah atsorace nake da lamarin yah musab,duk da yadda jikina yake tsananin son kasancewa dashi amman can kasa akwai tsoro.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now