*NERNER AYSHER*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3561🅿️..........10
Kwance nake muna chat da hamid ba yau na samu kaina cikin nishad'i ba laifi saboda tun safe muke waya da hamid,muyi chat har ma da video call.
Ya sakani cikin farin ciki domin hamid gwanine wajen iya soyayya,ga kalamai masu kwantar da hankali shiyasa na wuni d'aki ko abinci saidai sofy ta kawo mun,ko sallah tara su nai sai da akai magriba nayi su baki d'aya shima kuma shaf shaf ko addua ban ba nadai ce *Allah ka gafarta ma Abbu ka haskaka kabarinsa* banda haka babu abunda nai,na tashi kenan ina cire hijab d'in sofy ya shigo tace "yaya nanah kifito ga Abba sufyan nan shida lawyer Abbu da wani malami sai goggo sabira inajin dai rabon gadone."
Dan danan na d'aure fuskata nace "muje tana wurgar da hijab d'in ta fito fuskarta murtik kamar an aiko mata da sak'on mutuwa.Mami,mus'ab da su Abban duk suna falo zazzaune ga kuma wani malami nan yana jan carbi da gani dai kasan malamin karyane,inhar kasan malamin kwarai.
Wani kidahumin kallo take binsu dashi d'aya bayan d'aya,kafin taja ta tsaya daga bayan kujerar mami babu ko gaisuwa balle wa magana mai dadi,Abban yace "ke baki iya gaida mutane ba,kinxo kin tsaya kina karewa mutane kallo kamar tsararrakin ki."
Wani jakin kallo ta masa tace "gaisuwata kaxo ka saurara kokuwa wani abunne nadaban,idan gaisuwata kake nema zaka iya juyawa don bazaka samu ba inkuma wani abunne ka fad'a kafin nagaji da tsayuwa nabarnan."
Goggo sabira tace "iyye sanni rasa kunya beran tanka,watau ke tatattar marar kunya uban naki kike gaya ma magana?!"
Dogon tsaki naja nace "waye uban nawa?badai wannan ba Allah ya sawak'a."
Cije baki Abban yayi yana jinjina kai yace "zakici ubank...........karka sake zagarmun uba,wlh tallahi ka sake zagin Abbu saina rama mas........"
Cikin tsawa da dakatarwa mus'ab yace "indan kika sake magana anan sai ranki yayi mummunam b'aci,akwai sa'anki anan ne.?"
Idona har wani maik'o bala'i yake da masifa nace "taya zai zagar mun uba kum...........I said keep quiet be for I slap u."
Jinai kawai bakina ya tsaya da maganar,ta mak'ale daidai mak'oshina bakin ciki kamar zai kasheni idona yayi jaja wur kuma duk sun fito waje.
Wani kullutu ne yaketa kaikawo ga mak'oshina ina had'iyesa yak'i wucewa.
Goggo sabira tace "gaskiya ne,watau munan duk munfi karfin mu fad'a kiji sai wani banzan driver ko........mus'ab ya runtse idonsa ya bud'e yana tausar zuciyarsa baice komi ba,Abban yace "samun wurine kawai bakomi ba,inbanda shi uban naki ya daure maki gindi har kin isa ina fad'a kina musu dani,da ban xubda maki hakoran gaba ba."
Mami ranta yafara b'aci tace "sufyanu inajin rabon gado ya kawoku nan,to don Allah ayishi atashi lfy ba neman fitina ba sannan kasan irin kalamim da zaka ringa furta wa mamaci fadar magana marar dadi ba daidai bane."
Wani kallo ya watsa mata sannan yace ma malamin "bismilla ya malam"Addua akai da salatin Annabi sannan aka shafa,Abban yadubi lawyern Abbu yace masa "barrister ka karanto mana dukkan abunda yake mallakin Alh kowa yaji da kunnensa kar suga ko akwai cuta aciki."
Dogon tsak'i naja nace cikin fushi "inbabu rami meya kawo ramin."
Mus'ab yace "wallahi kika sake magana anan kinji na rantse zaki bar wajen nan,ki kame bakin ki."
Kunbura kawai take tana sawa tana sauka,kukanta yana wuya kallonsa kawai take shikuma ya dalla mata harara.
Barrister yafara da cewa
"Alh Abbakar hakika ya tara dukiya mai yawan gaske,wanda duk wanda yasan sa yasanshi da dukiya da kadarori,tabbas nine shak'ik'insa wanda yake ba dukkan bayan kudinsa da kadararsa,dukkan wasu takaddu masu muhimmanci suna wajena,in banda wasu da ya ansa kafin rasuwarsa."
Yayi shiru yana dauko wani file yafara b'udewa ya fiddo wasu takaddu ya ajiye saman table,ya dauki d'aya yace "wannan takardar filinsa ce dake rijiyar zaki."
Ya mik'a ma Abba shikuma ya ajiye gaban malam.
Sannan ya sake d'auko wata yace "wannan kuma takardun gidajensa ne guda hud'u sune had'e anan waje guda,suna nasarawa yanxun haka."
Ya sake mik'ata ya dauko wasu yace "wannan kuma takardar wannan gidance" ya mik'a ta ya dauko wata yace "wannan kuma takaddar karamin company sa ne na auduga sabon da baifi shekara uku da bud'ewa ba,wad'anan sune takaddun da Alh yaban tun yana raye,sai tsabar kud'i dake cikin bankinsa biyu yana da tarin kud'i cikin asusunsa sun tasanma biliyan talatin,wadanan sune dukiyar da Alh ya bari sai fa motoci gasunan sunkai guda shida."
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...