part 36

118 15 1
                                    

*_NANAH AYSHA_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........36

"Bismillah Dr zauna mana"
Ummi da duk jikinta yayi sanyi taja kujerar ahankali tana ajiye bag d'inta saman table d'insa zare glass d'insa yayi yana murmushi yace "kwantar da hankalinki ba tsohuwar maganarmu zan tado ba,saboda yanxu na hak'ura don dole saboda ance fad'an da fik'arfinka ka maida sa wasa koba haka ba?"
Ya gad'a da murmushi kan fuskarsa ummi tai ajiyar zuciya tace "Ai koba kafad'a ba yallab'ai aikafi k'arfina kuma kasan kome zakai bazan iya aurenka ba"
Yana shafa kanshi yace "naji nayarda ada dai nace saina ga abunda ya turewa buzu nad'i amman na sauko yanxu,watai Raihana wani mutume ne mai daraja da kima yai mun maganarki babban mutum ne sosai agarin nan,shine ya ganki ya rasa hanyar da zai yi miki magana shine fa ya biyo ta wajena yace don Allah na ansar mashi address d'inki inkin bashi dama zaizo har gida kuyi mgn."
Yai shiru yana kallona kamar yadda take kallonsa zuwa can ta sauke kai k'asa tana nazarin maganarsa kafin tace "MD waye wannan?"
Murmushi yayi yace "Aa zanso ace shine zai gabatar maki da kansa don haka nidai inhar kin amunce na bashi address d'in naki ki amsa mun?idan yazo sai kiji komi daga bakinsa ance wak'a bakin mai ita tafi dadi koba haka ba?"
Shirun ta sakeyi tana tunani aranta,tabbas ya kamata ta bude xuciyarta zuwa yanxu kodan ta samu tabar gidan Abbyn anwar,Amman babu abunda take tsoro arayuwarta da ya wuce zama da kishiya,ta dcan d'ana bataji da zak'i ba ko kad'an.
Don haka in yazo zataji idan yana da mata inhar yana da mata zata bashi hkr su rabu lafiya don tab'on da kishiya tai mata bazata tab'ajin ya goge daga zuciyarta ba.
Taji yace "kinyi shiru dr Raihana?kice wani abu mana"
Ajiyar zuciya tayi tace "MD ka bashi address d'in zanga idan ya dace da rayuwata."
Washe baki yayi sosai yace "kai kai kai wlh abun yayi armashi sosai,ai nasan ma zai maki dari bisa d'ari"
Murmushi kawai tayi sannan suka cigaba da maganar yadda meeting d'in zai kasance na gobe,yai mata alert din kudin da za'ai siyi duk abunda ya dace da bak'i zasu ci su sha.
Saida suka gama sannan tatashi ta wuce office d'inta tasan files nacan na jiranta da patient............
Bayan fitarta ya daka tsallen murna saboda yasan zai samu kaso mai tsoka sosai wajen *MINISTER S MUSTAPHA JAJI* wanda yake rik'e da kujerar minister of finance ma'ana minister kudi na Nigeria baki d'aya,saurin fiddo wayarsa yayi ya soma kiran sa cike da zumud'i yana jin yayi picking yace "yallab'ai barka da yamma"
Fafa yana cikin office yana juyi cikin kujerarsa yana rik'e da biro hannunsa takaddune gabansa yake rubutu akai yace "daman cewa nayi biyar da rabi na cika zan kiraka naji ya ake ciki sai gashi ka kira fatan andace"
Yana dariya yace "yallab'ai ai bata wani ja sosai ba saboda ban gaya mata kowaye ba,nace in kaje zakai mata bayani."
Fafa yayi murmushi yace"amman ka kyauta sosai inda hali baka komi kazo ka sameni office yanxu"
Cike da jin dadi yace "angama rankayadad'e"
Ya har had'a abunda zai buk'ata daga can gida xai wuce ya fice daga asibitin.

******

Ina zaune saman abun salla na gama sallar magriba na jingina da bago ko hijab d'in ban cire ba wuri guda na tsura ma ido bazan ce ga abunda nake kallo ba,bakina ahankali yana ambatar Astagfirullah ina k'irgawa da gab'ob'in yatsuna.
Sofy da mami ne suka shigo d'akin tare sofy da plate hannunta mami kuma da cup sai robar faro swan inda nake suka karaso mamin ta zauna bakin gado sofy ta zauna gabana tana bude plate d'in tace "yaya nanah ga farfesun na gama koshi kici don Allah."
Lumshe idona nayi na bude ina kallon zallar naman kazar da sofy ta dafa mun saboda tunda muka dawo ban saka komi acikina ba sai ruwa,mami ce ta mik'o cup d'in hannunta tace "shanye sa yanxu kiban cup d'in."
B'ata rai nayi nace "mami kinsan bana son tafiyoka ko"
Had'e rai tayi tace "ba ita bane shanye sa maza zai maki maganin yunwa"
Sofy tana dariya k'asa k'asa na dalla mata harara mamin tace "ko idonki zai fad'o sai kin shanye sannan ki cinye naman,sai muyi magana."
Ansa nayi ina kalon abunda yake cikin cup d'in wani abune kamar tafiyoka had'e da peak milk sai aka zuba madarar L&Z aciki sai rab'a cup d'in yake alamun sanyi,jinai miyauna har ya tsinke inason naji test dinsa.
Spoon d'in dake hannuna na saka na d'ebo romon naman na sha sannan na fara shan abunda yake cikin cup d'in naji wani masifeffen gard'i da zak'i yana kai min har k'walwata.
Dariya sofy ta kama yi mamin na murmushi sofyn tace "yaya nanah anji dad'i,to wai meyasa ni bazan sha ba mami"ta fad'a cikin shagwab'a dungere mata kai tayi tace "tashi kifice zanyi magana da yayarki"
Tana turo baki tace "don Allah nidai kibarni yau ma anan zan kwana."
Mami ba ta sake bi ta kan sofyn ba taita lallab'ani har na cinye naman da yake ba yawa garai ba sosai,ga kuma yar banzar yunwar dake cina aciki.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now