part 15

117 9 2
                                    

*NERNER AYSHER*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3561

🅿️..........15

Da sallama suka shiga falon idonsa akansu dan danan ya d'aure fuskarsa tamau kace bai tab'a sanin yadda ake dariya ko murmushi ba,Ai Abule na ganin sa ta saurin mik'ewa hakoran nan kamar tasha d'orowa sunyi sharr ba kyan gani ta washesu tace "laaa mus'abu kaine ka zama haka."
Sake d'aure fuskarsa yayi har ya idasa shigo yana zama sannan ya gaida mamin,tace "tunda ka dawo ban sake ganin ka ba."
Shafa kansa yayi yace "bacci ne ya daukan wlh"
Tace "ga bak'inka nan mamanka da kanen babanka."
Kallonsu yayi yace "Mami ni bani da mama marik'iyata ce matarsa ce."
Soke kai baban yayi yana y'an kame kame yace "Au...eh...haka ne marik'iyarsa ce ai shi tun yana yaro iyayen nasa suka rasu,ahannuna yataso."
Girgiza kai kawai mami tayi ba tace komi ba,mus'ab d'in yace"meke tafe daku,bance kar wanda ya tako kafarsa inda nake ba?akan me zaku zo kuna da wani sauran business danine?"
Matar baban ta lauyar dakai tace "Aa d'an nan karka manta da cewar yarinyar nan Abule tun da aka haifeta mahaifinta ya baka ita,kuma kaima mahaifinka ya ansar maka auren kawai za'ai kuma abule na sonka koba haka ba Abulen babaah."
Ta washe baki da wadannan hakora ba kyan gani tace "ehy inna aradu inason Mus'abu."
Wani banxan kallo ya watsa mata cike da haushi yace "dalla zauna."
Saurin zaman tayi tana rakub'ewa bayan innar tana turo baki,kallon baban mus'ab yayi yace "nasan kasan ina da wata matar ai ko?"
Baban yace "ehy....ehy na sani d'annan Ai hakan bazai hana ka kara ba,ai addini bai haramta ba."
Girgiza kai yayi yace "idan ina ra'ayi ba kune zaku kawo mun ita ba nine zan biyoku har kauye na aurota na taho da ita nan,don haka koma wa xakuyi da ita don bakuda hujjar da zaku kawo mun ita nan tunda ba gidana bane,kuma ba Aure tsakaninmu akan me"
Innar ta fara had'a hannuwa tana rausayar dakai zatai magana yace "karki ce komi inna ku koma da Zainabu idan ina ra'ayinta xanzo har cibiyayi na aureta."
Ai sai Abule ta rushe da kuka, kuka ba na wasa ba tana shure shuren kafafu.
"Alqur'an babu inda zani,aradun Allah ni inanan bazan koma ba saika aureni,aini ina sonka kuma kaima ai kana sona,me matar taka zata nuna mun nafita kyau na fita girma alqur'an bazan je ba."
Sofy me zatai ba dariya ba harda rik'e ciki mami kanta saida tayi murmushi,wai wannan kucakar ke had'a kanta da nanah tabdijam,lallai karma Alah yasa ta fito ta gansu don wlh anbani.

Mik'ewa mus'ab yayi yana duba agogo yace "yanxu bakwai tayi idan kuka taso na kaiku tasha zaku samu lafiyayyar mota daga nan har can,don wlh kunji na rantse bazata zauna anan ba na gama magana,naje sallah."
Ya fice daga falon kuka kawai Abule take rusawa sai lallashinta inna keyi,mami tace "kuyi salla kafin ya dawo ko"
Abule ta kalli mamin tace "yanxu ke fisabilillah bazaki saka baki na zauna ba,wallahi tun dana shigo zuciyata ta kwad'aitu da son zama anan ni wlh ko shara da wanke wanke ne saina ringa yi maki kafin sadda zai sauko muyi auren."
Murmushi mami tayi tace "to zan masa magana ku tashi kuyi sallah,kai baba kaje wajen maigadi sai kai alwallah akwai masallaci awaje."
Ya tashi yana godiya asabe mami ta kwala ma kira ta iso tana durkusawa ciki girmamawa tace "kwashe kwanonin nan agyara wajen,sai ki kaisu can b'an garenku suyi sallah."
Tace "to hajiya"
Ai tun kafin ma asabe ta kashe kwanonin abule ta kwashesu tas,sannan tace "ina ne madafar taku."
Murmushi kawai mami keyi tace "kuje zata nuna maki."
Bin bayan asabe sukai mami ta bisu da kallo sofy tace "mami me kike nufi?badai cewa xakiyi ya auretan na,?Allah ya sawak'e yaya nana tayi kishi da wannan kazamar,don Allah karki soma yin haka mami"
Girgiza kai mami tayi tace "ba cewa xanyi ya aureta ba,idan yana da niyyar hakan kuma bazan hana sa ba,zance ya barta ta zauna damu saita ringa taya asabe da lantana aiki,bayan haka kuma akwai wani dalilin nan gaba zaki gane."
Ta wuce bangarenta tabar sofy da rikon baki,wannan kucakar ai kokusa bata jin yayanta zai iya dating da ita balle har akai ga aure.,wuce wa tayi itama dakinta duk da ba salla zatai ba.

Rabon da nayi bacci mai yawan wannan na manta saboda rashin natsuwa da kwanciyar hankali,sadda na tashi naji masassarar ta sauka saidai ciwon kai shima harda kukan da nasha sosai,saukowa nayi na shiga toilet wanka nayi da ruwa mai d'umi sanan nayo Alwallah nazo nayi salla sanan nashafa mai da turaruka na saka doguwar riga marar nauyi na sagala kallabinta kawai,yunwa nakeji sosai dole na fito daga d'akin babban falon babu kowa haka ma karamin,dining na wuce ina duba abunda akai na dinner naji anbude kofar shigowa wani irin bugawa zuciyata tayi,ta fara dokawa da sauri da sauri.
Saurin rufe kular miyar nayi ina jan kujera na zauna na rasa abunyi,can falon najiyo maganarsa alamun dai ba shikad'ai bane,ban dai juyana kallesu ba inanan zaune mami suka fito ita da sofy naji tace "kun dawo mus'ab."
Yace "eh mami ina suke suxo muje na sauke su."
Mamin tace "sofy jeki kice sufito."
Ta wuce tana kara sawa cikin falon tace "mus'ab inson kabar zainabu anan,koba komi zata ringa yimana wasu aikace aikacen."
Kallon mamin yayi cikin mamaki yace "mami waccen kazamar zakice tazauna idan ma itace ta saki fad'ar haka to duk abunta saita koma kauye."
Baban yace "Aa mus'ab karkayi haka don Allah kabari ta zauna d'in."
Sofy ce da su zainabu suka shigo,kallon mus'ab tayi ta washe hakora tace "mus'abu kaji hajiya tace bazan koma kauye ba anan zan zauna na riga yi mata shara da wanke wanke harma da gyaran d'aki."
Ta fada tana wangale baki yamutsa fuska yayi yace "mami me wannan zatai maki anan kibari don Allah sutai wlh wauta ne da ita."
Mamin tace "nidai inason zamanta anan don haka kabari ta zauna in lokaci yayi kaga zaka iya auren nata ba shikenan ba,inma baka iyawa akwai maza agari zata samu wani amman ka barta anan."
Ai inna da baba kamar suyi me don dadi,ba yadda ya iya da mami bazai iya musu da ita ba yace "shikenan mami.............ban san sadda na taso daga dining na iso falon ina toshe hancina da bakina ba,ina masu wani dakikin kallo na aje idona akan wadda ake kirarin zata zauna agidan dannan a masifance nace "mami wai waye zai zauna nan d'in,karkice mun wannan kazamar?wallahi tallahi ba dai nan gidan ba aiba gidan ubanta bane,bamu had'a komi da ita ba akanme?na rantse da Allah bazata zauna anan ba sokike mukwashi diseases,haba mami don Allah kalleta dubi fa kiyi ma Allah ki barta tatafi wa ina ma akasamo su."
Tuni Abule ta boye bayan inna tana hawaye,saboda dai duk mai mata bakin cikin zaman wannan aljannar duniyar jitake kamar tayi me,mami tace "Nanah yan uwan mus'ab ne fah,kuma matarda zai aure ce dole zata zauna anan kafin lokacin yayi..........ai bansan dariya ta kubce mun ba wadda bazance ga lokacin da nayita ba,na d'ago ina sake nunata nace "matar da zai aura uhm lallai ai sai itan,to yakaita can part d'insa mana nikam wlh bazan zauna da wannan daud'ar ba."
Sofy tace "kiyi hkr yaya nana da man bafa cikin nan zata xauna ba can b'angaren masu aiki zata zauna."
Na koma dining ina cewa "da dai yafi kam gaskiya."
Ajiyar zuciya Abule tayi tana goge hawayenta,ta jawo bakkonta da kullin kayanta tace "inna saduwar alkairi yanxu sai bikin namu yazo zakuzo da jummai ko?"
Innar ta washe baki tace "sosai ma abulen kaka."
Mus'ab dai yayi gaba sannan suka biyosa bayan sunyi sallama da mami tare da yi mata godiyar wannan alfarma.
Mami tace zainabu ta dauki jakarta ta kai can dakin su asabe da safe sai suyi magana,cike da jin dadi kuwa ta wuce tana suburbuda mata godiya.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now