part 2

178 10 0
                                    

*NERNER AYSHER*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3561

🅿️............2

Tafiya suke zuwa shopping nernerh ta had'e gabas da yamma kudu da arewa babu burbushin murmushi ko fara'a akan fuskarta,sau tari inhar tana tare da wani kaskantacce acewarta to sakin fuska ko dariya ko doguwar magana gaban talata zai kawo raini tsakani.
Ita da sofy ne bayan motar sai driver shikadai agaba ya maida duk hankalinsa kan titin,sofy tace "Yaya nanah har banson gobe tayi saboda zamuyi kewarki wlh"
Hannunta tarik'e cikin nata kafin ta d'an yi mata murmushi tace "don't worry my love ai zamuna video call time to time,nima badan inason karatun ba ai da bazan tafi ba."
Kwantar da kanta tayi gefen kafadar yayar tata tace "Amman zanso ace........shiiiiiiit banson duguwar magana sofy."
Dole taja bakinta tayi shiru,suka cigaba da tafiya ta maida kanta tana danna hadaddiyar wayarta iphone 11 pro ansaka mata pink cover anyi mata adon stones ga kuma zenen heart ajikinta.
Daka ga wayar kasan ta mace ce macen ma mai aji irin nanah Aysher,chat take da friends dinta wadanda suka rigata komawa suna tattauna hira lectures da akai bata nan,tana cewa gobe early morning Abbunta zai rakota...........wani wawan burki taji antaka har kanta yana buhar gaban sit din mai zaman banz,kallon gabansu tayi taga wani mai napep ne yashigo hannunsu............sauke glass *mus'ab* yayi mai napep din yana bashi hkr kai kawai yajin jina masa kafin yafara kokarin cigaba da tafiya,cikin masifa da bala'i tace masa "kai!!kana hauka ne?ina hankalinka yatafi har kake niyyar kashemu?..........kinga ba laifi bane karki mun fad'a"
Ya katse ta da fadar hakan zaro ido tayi tace "iyyeee,au nikake cema karna maka fad'a?kai din wai kaidin banza da wofi,tsayar da motar nan nace dakai nake ka tsayar da motar nan."
Wani uban cin burki yayi da zai nuna maka ya fara hasala,sofy tace "yaya nanah pls.........kinga yimun shiru kafin na sab'a maki"
Ta maida hankalinta kansa cike da tijara ta cigaba da cewa "kai har kana da bakin fadar cewar kar na maka fad'a har ka isa,kaidin banza da wofi.to wlh kashiga taitayin ka don ni nan ba kanwar lasa bace,ka tambayi mani driver sharuddan tuk'ani don shine driver na don haka next time ka kiyayeni."
Uffan bai tofa mata ba harta karaci masifarta saida yaji tayi shiru sannan ya cigaba da tafiya,amman kallo daya zaka masa kasan ransa yayi masifar b'aci.
Tsaki taita ja har suka isa wani babban mall din da akeji dashi cikin garin,watau *K.LULU* kayansu sun hadu ga kyau ga karko.
Wajen parking yaje ya samu waje ya parka yafito yaxo ya bude mata,saida ta fito sannan ya rufe ya zaga don budema sofy amman ta riga ta fito saiya rufe marfin.
Tana tsaye batare data jiyo ba tace masa "kabiyo mu don daukar mana kaya."
Taja hannun sofy sukai ciki,sofy tai ta waigensa ganin bai taho ba yadai bisu da kallo.
Arayuwa mus'ab yana bata tausayi tun sadda Abbu ya daukesa aiki ita dai hakanan takejin tausayinsa,gashi mutun ne marar magana.
Kwata kwata kalamansa basada yawa wanda yake mayar da magana kansu,daga to yallabai,sai insha Allahu,sai ina kwana,to gasunan dai gajajjerun kalamai sune maganarsa.
Ko fitowa sukai sun rako Abbu zaije wajen aiki idan ta gaidasa zai ansa da sakin fuska yace "lafiya lau" bata tunanin ma yasan sunanta..........."wakike waige ne wai."
Sofy tai saurin jiyowa tana rairai da fuska tace "yaya nanah kiringa sassauci don Allah"
Harararta tayi tace "kenan na barsu su rainani,nai daidai dasune aikinsan ruwa ba sa'an kwando bane."
Shiru sofy tayi bata sake cewa komi ba,saboda dai tasan halin yayarsun bazata canza ba.
Dan dakata wa sukai ta juya ta hangi bayansu,hangoshi tayi yana biye dasu taja tsaki kafin ta nuna masa babban basket tace "take it and follow me"
Bai musa ba kuma baice komi na ya d'auka yana biye dasu,duk abunda take so wanda taga yakai high class take dauka har basket din yacika.tace ya sake dauko wani sofy tai saurin cewa "yaya nanah bari naje na dauko"
Kafin tace komi harta tafi nan suka jirata harta dawo suka cigaba da zagawa suna daukar duk abunda suke so,atakaice saida suka cika basket hud'u.
Sukaje sukai paying akai masi parking dinsu sannan ya dauka yana kaiwa mota,sofy ta ringa tayasa duk hararar da yayar ke maka mata.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now