part 19

107 9 0
                                    

*_NERNER AYSHER_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

🅿️........19

Duk yadda nake hana kwayar idona kallonsa abun ya faskara na tsinci idon nawa cikin nasa muna kallon juna,directly idona cikin nasa shima haka nasa cikin nawa,na gaza gane wane irin kallo ne muke yawan yima juna,wanda har mukan mance a inda muke sofy ta k'ushe dariyarta tayi gyaran murya tana cewa "uhmmm yaya yaushe zamu tafine."
Gaba d'ayan mu saurin dawowa hayyacin mu mukai,duk jinai na kunyata sai soke soken kai nake saurin yin hanyar waje nai don na rasa abunyi.
Sofy na dariya kasa kasa tana sunne kai,rankwashi yakai mata ga kai yace "dariyar me kike magulmaciya"
Kyalkyalewa da dariyar tayi tana tashi daga zaunen tana sosa kanta,tace "nifa badaku nake ba."
Murmushi kawai yayi yace "muje."
Gaba yayi ta bisa abaya saida ta rufe gidan ta saka key d'in ga jikka sannan ta samesu can bakin get d'in gidan,da yake titine akofar gidan kana fitowa zaka samu taxi.
Ina rungume da hannuna ga kirji na gansu,ban sake kallon gefensu ba don har sannan inajin bugun xuciyata,mai taxi d'in ya tsayar na shiga gaba su suka shiga baya kasancewar nice na san sch d'in sai nai masa bayanin makarantar yace ya gane sannan muka tafi,hirarsu suke can yaka junansu ni kuma ina danna wayata zuwa can na tuna bamu kira mami ba batare dana waiga ba nace "sofy have u call mami"
Tace "wallahi ba layina yak'i tafiya bansan ya akai ba."
Nace "ni kuma na kira ban samu ba ko miye matsalar."
Har dai muka isa nidashi bamuyi magana ba,ya sallamesa muka nufi cikin makarantar,haduwa kenan don billahi inkai bakauyeni saika zuba kauyanci,to gadai sofy nan tana ta sabbatu mus'ab na mata dariya.
Kiran Abdul d'in sukai suka gaya masa ga inda suke yace yana zuwa,suka samu wuri suka zauna nidai ban sake yarda na kallesa ba wayata nake danna wa kawai.
Kamar daga sama saiga Abdul ya bayyana shida wani friend d'insa dan nigeria shima.
" wai wai wai masha Allah Abdulrahman haka ka koma zabgi kenan,wannan ai ka kamoni akomi ma ko."
Inji mus'ab rungume juna sukai shida Abdul d'in yana dariya yace "kai yaya wane ni na kamoka."
Yace "haba ai ko makaho ya shafa zai fad'i gaskiya."
Sofy tace "wlh bro ka kara girma sosai garin nan ya amsheka ga kyau ka kara."
Ya rungume sofyn yayi cikin farin ciki har da yar kwallarsa dariya suke masa kawai,yaje ya rungume yayarsu yana cewa "nai matukar kewarku yaya nanah,nai farin cikin zuwanku."
Shafa kanshi nai nace "muma haka bro ya karatu ina maka murna Allah yasa albarka."
Sai ya kama kuka wanda duk jikin mu yayi sanyi yace "yaya nanah duk sadda na tuna Abbu bazaiga wannan rana ba sai naji hankalina yana tashi,naso ace dashi zamuyi wannan murnan amman sai gashi hakan bata samu ba."
Mu duka sai muka kama kuka muka rungume juna mu ukun,ba wanda yace mana komi har muka yi iyakar iyawarmu sannan muka hkr.
Yace "kuxo muje gidanmu ai zaku kwana acan ko."
Mus'ab yace "muje mu zauna maka zuwa karfe goma sai mu koma gida, kafin goben saboda mun riga mun kama gida,kuma kaga bakai kadai bane."
Haka muka shiga motar su Abdul d'in nida sofy da bro baya sai mus'ab da abokin Bro agaba,hira sosai muka ringayi dashi daka gansa kasan yana cikin matsanancin farin ciki.

Agidansu Abdul muka sallar magariba har da isha'i mazan suka fita masallaci kasancewar unguwar akwai masjid,mu kuma mukai agida.
Sofy ta shiga kitchen ta shirya lafiyayyar indomi da kwai daga k'amshinta kawai zakaji kana son kaci,abunda ban iya ba kenan ni idan ka ganni kitchen to abu nazo d'auka ban tab'a attempting yin wata sanwa ba,suna shigowa ta zuba masu tasu takai masu bro da abokinsa sai mus'ab nashi daban.
Sannan ta sanyo mana tare muka zauna falon anata fira amman saika dade bakaji bakin mus'ab ba.
Nid'inma ba sosai nake saka baki ba donma sun sanni ba gwanar magana bace yasa basu damu ba,saidai nai murmushi kawai.
Muna cin idomin naji yar wayarsa tana vibrating kallon juna makai karo na farko tunda muka fito gida daxun,harararsa nai kadan ya zari ido irin ni kike harara d'in nan,na murgud'a baki na cigaba da tsakurar noodle din da fork.
Saka wayar yayi ga kunne bro yace "wai yaya har yau baka canza waya ba,don Allah ka canza waya haka nan ba girman ka bane."
Murmushi yayi kawai yana cewa "soon insha Allah."
Sannan ya maida hankali kan wayar tashi yana d'an murmushi,duk ina satar kallonsa lokaci zuwa kokaci,kasancewar ba nisa yayi da inda muke da sofy ba yasa nakanji abunda yake fad'a.
Naji yace "taliyar yan yarace in zakici."
Tsai nai da idona ina kallonsa hakan ya tabbatar mun da mace yake waya,sai naji nak'oshi da noodle d'in duk da dan karen dadin da tayi mun.
Lemu na kurb'a na ajiye fork d'in,jinai ya sake cewa "me zaki ce mata idan na bata gaya mun first sannan."
Tashi nai daga inda nake zaune nayi hanyar waje sofy yace "ina kuma zaki yaya nanah."
Nace "zan d'an ga waje ne kafin ku gama."
Bro yace "karfa ki b'ace yah nanah".hararar wasa nai masa nace "ko kai baka gaya mun malaysia yaro."
Dariya sukai shida abokin nashi wucewa nai zuwa farfajiyar gidan wurin wani lambu da yai kyau sosai,akwai matakaka da zata saka ka hango waje na tattaka na hau saman,iska mai dadi yake kad'awa na rungume hannuna ina jikin wasu karafa da aka katange wajen dasu,ina kokowar hana zuciyata shiga wani tunani na daban,wurin tarr yake da hasken kwayaye different colors gwanin sha'awa.
Inayi ina duba agogon dake daure hannuna,sai naji wayata tayi kara no d'in mami ce ina ta samu layina na malaysia??
Dauka nayi muryata ta zama so cool ban san dalili ba.
Cikin sanyi nace "mami in wuni,inata son kiranki hakan ta gagara."
Tace "layin nawa network ya dauke,amman ai munyi waya sa mus'ab tun da kuka sauka."
Nai shiru ina tuna sadda nake ma sofy maganar ashe ya kirata shine yai kamar baisan me kuke fad'a akai ba.
Nace "Amman mami yana ji muna maganar rashin samunki yai banza damu wannan ba daidai bane "
Tace "ya isa haka mus'ab ba mai hayaniya bane haka yake karki dauki hakan da zafi,to ya Abdul d'in."
Nace "akai masa wayar ne."
Tace "ke kina ina ne to?"
Nace "ganinan ina shan iska su suna ciki."
Tace "kyalesa to zan kirasa don Allah nanah kar kija yayanku da fad'a kinjiko,duk abunda zai saka ya maki fad'a ki kiyaye."
Jinai kwalla ta ciko idona daker nace mata "uhm"
Sauke wayar nai ina share hawayena,naji anyi gyaran murya bayana nai saurin ida goge kwallar na d'an juya na gansa tsaye bayana hannunsa duk sanye cikin aljuhun wandonsa.
Kawar da kai nayi ina cigaba da kallon waje motoci na wucewa da mutane,gefena yazo ya tsaya yana dafa karfen dake wurin ya d'an sunkuya yana kalon wajen shima.
Uffan ban ce masa ba kusan minty biyar sannan yace "meyasa kika fito daga cikin mutane."
Nace cikin rashin kuzari "haka nan."

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now