*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........45
Duk da yadda basu kwanta da wuri ba kiran salla akunnensa aka yishi,daker ya iya bud'e idonsa ya tashi ya shiga toilet yayi alwalla sannan yazo ya gyara mata kwanciya ya sun kuya yana kissing forehead d'inta,murmushi na kubce masa inya tuna daren jiya.
Ahankali ya bud'e kofar ya fita don har an tayar da sallar yau bai samu damar zuwa kiran sallar ba don har lokaci ya gota,yasan anjirasa anji shiru shiyasa wani ya kira.Kamar an tada ni daga baccin haka naji idona ya bud'e,sai yaji suke mun jina nayi tunb'ur ba rigata ba bra d'inta,idona a warwaje na soma lalubar inda akai fatali dasu kunya kamar tayi me dani,dan danan cikin sauri na maida abuna na diro na suri hijab d'ina na saka na xura takalmana na arce cikin gida,gabana yana fad'uwa kar mami ko yadidi su san ban kwana d'akina ba,saida na ganni cikin dakina sannan na sauke ajiyar zuciya addua nake Allah yasa ba wanda ya lura da rashin kwana na cikin gidan dana shiga uku bazan iya sake had'a ido dasu ba expect sofy.
Alwallah nayi nafito na zura doguwar riga nayi sallar,da har na d'auko na fara karatu sura biyu na iya karantawa adaddafe na rufe na rarrafa ma haye gadon,wayata ma na mantota can saboda shegen sauri kar aganeni.
Kan kace me bacci ya sake figata ina sauke ajiyar zuciya........******
*Agurguje*Tun daga wannan ranar ganina yayi wa yah mus'ab wuya saboda dai kullin ina d'aki saboda gyaran da aka fara yi mani sai anyi sati ana abu guda ko main falo bana fitowa iyakata bed room din mami da falonta,saidai muyi waya dashi kamar zai mun kuka wai wallahi in bai ganni ba bazai samu sukuni ba,ko wurin aiki ya fita baya gane komi.
Banda dariya babu abunda nake masa illa ince "kaya kuri *my prince* nima fa hkr nakeyi karka ce mun dai nafika dauriya"
Sai ya had'e fuska yace "kedai kawai kin daina ji dani,aida ko satar hanya kinyi kinxo na ganki ni wlh atakure nake."
Da haka zan shashantar dashi karshe yayi fushi ya kashe wayar,bai hana kuma anjima ya sake kirana,ita kanta mai yi mun gyaran rannan saida tace "gaskiya wannan angon fa ya matsa lamba baya baki tausayi"
Araina nace "ai nice abun tausan wannan da kike ganinsa ba wani tausaya mun zai ba."
Amman azahiri sai ince mata "rabu dashi fitina kawai yakeji."
Batun kyau da taushin fata da haske b'atama bakine don inaka ganni cikin kwana hud'un da aka d'auka ana gyaran cewa zakai tarwad'ace ni,har hak'orana ba abarsu abaya ba su kansu akwai abunda ake shafa masu suna k'ara kyalli da haske,ni kaina na yaba sosai da aikin matar kuma tana koya mun wasu abubuwan da zan ringayi idan naje gidana badole sainaje wurin gyaran jiki ba,kwata kwata bata da irin halin masu sana'a don zakiga wasu basa son su fad'i wani side d'in aikinsu don karka kashe masu kauwa,while wannan ba hujja bace ita kasuwa ai ta Allah ce kowa rabonsa yake ci.Batun HQ kuwa ba'a cewa komi don wani turarene nake tsugunni dashi idan ina yin turaren har lumshe ido nake saboda guminsa dake shigata ina jin dadinsa sosai,ga shegen k'amshi zaka d'auka ma na jiki ne aa na jiki daban shi ma inayi sau biyu arana safe da dare,b'angaren shaye shayen abubuwa kuwa bana shan wasu abubuwa da suka wuce tsumi sai fruits,haka yadidi zata yayyanka mun Apple,ayaba,kankana,cucumber ta zabga mun peak milk ta ruwa aciki saita juye mun gwangwani biyu ko biyu da rabi,kuma bata samun suger haka zan ta cinsu ina shan madarar wayyo Allah na,abunda yake fita daga jikina kamar madarar haka yake.
Gaskiya ni kaina na tabbatar na gyaru kuma akan guiwa nake,kunya ce da kawaici nakeyi bana nunawa,ita kuma yadidi sai tace "wai kuwa kinajin canji ajikin ki?"
Saidai ince "uhm inaji"
Sai tace "ban gane uhm inji ba,bayani zakiyi mun don insan ta inda zan kama in abunda ake bai wani aiki ai aikin banza akeyi."
Ni kuma na rasa yadda zan mata bayani saboda dai wlh kunya nakeji ince mata inajin sha'awata tana ninkuwa fiye da kima,kuma in ina magana da yah musab inajin abu yana fitar mun muryarsa kawai in naji zanji jikina ya canza,ba wai sai yayi mun wata magana da bedroom secret ba.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...