part 48

148 14 4
                                    

*_NANAH AYSHA_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........48

*business aisa scent and spa empire company yayi  suna haka zalika yayi fice ta b'angaren sarrafa turaruka na kece raini,sabulai na gyaran jiki da zasu maida miki fatarki tamkar jariri sabon haihuwa,ina kuke manyan mata kai harma da k'ananan inhar kina son sabunta kanki ki saka zuciyar mijinki motsawa to kau kema sai kin motsa,don mace saida gyara yar uwa karki bari wannan garab'asa ta wuceki cikin sassauk'an farashi zaki samu dukkan kayan gyaran dakikeso da kudinki kalilan kisha mamaki,ni mom muhseen na shaida hakan so ina maku albishir da cewar  AISA SCENT AND SPA EMPIRE COMPANY sun shirya tsaf don tabbatar da gyaran kowace irin mace kama daga kan amarya uwar gida kai harma da wadda take fuskantar matsala da mijinta in akai mata wannan gyaran ina mai baku tabbacin zakusha mamaki,ku garzayo kar abarku abaya 08065662450 masu buk'ata ga contact d'in mu nan ga masu so sai suyi contacting d'inmu,sai mun jiku masoya kuma abokan kasuwa*

Sha biyun na bugawa kau naji vibrate d'in phone d'ina nai saurin tashi zaune dama idona kawai nake rabawa saboda duk damuwar halin da nabla ta shiga nake ciki,gabana yana fad'uwa dana tuna tace mun har d'inki aikai mata.
Jikina a kasalance na dauki kiran murya can k'asa nace "yah musab"
Murmushi yayi yana zama cikin kujerar dake dakinsa yana shan coffee mai zafi don ya jima dadawowa ya rage wasu aiyukan ne kurb'an tea din yayi yace "Cutie bakiyi bacci ba."
Na turo baki nace "bakaine kace karna yi ba na jiraka,shine kake wani tambayana"
Yar dariya yayi yace "Ayya my love sorry nai tunanin kin gaji da jira kinyi bacci,to taso kixo ganinan ina jiranki."
Zaro ido nayi nace "Aa nifa bazan sake zuwa d'akin tazuru ba ehe,ka gaya mun dai albishiri d'in da kace zaka gaya man"
Yace cikin sassanyar muryarsa "yanxu cutie nine tuzurun?"
Dariya na saka kasa kasa ina yin abuna saboda yadda yayi maganar kamar wani d'an yaro ten years yace "dariya kike yi ko?uhm yarinya zan kamaki badai gobe bane."
Dan danan naji dariyar ta tsaya ina zaro idanuna na had'iye miyau daker nace da muryar tausayi harda yan kwalla na "yaya kaifa kace bazaka cutar dani ba,shine kuma yanxu daga na jaka zakace haka."
Hawayen suka silalo mani saboda dai nasan ina cikin tasku,yadda naji muryar nabla tana kuka nasan ba karamin lamari bane wannan abun,dariyarsa ya danne yace "Aaha toni menace kuma zaki yi mun kuka?"
Ai sai kawai na saka mashi kukan bilhak'k'i da gaskiya,don wlh tsoro ya kamani ji nake inama ace an d'aga tarewar ba yanxu ba.
(Ni kau nace koma yaushe ne dai nanah ai zuwa ranar zatai,kuma wannan harka yinta za'a ba fashi😂😂😂🤭)
Dariya ta kubce masa don wlh sosai ta bashi dariya,saida yayi abunsa yaga dai bazan daina kukan ba sai ya daina ya shiga lallashina yace "wai miye ne na kuka Cutie?ni ne fa prince dinki kinsan kuma duk abunda zai saki kuka bana so,ki cire duk wani tsoro da wani tunani akaina bazan cutar dake ba I promise u"
Shashsheka kawai nake ina jan numfashi yayin da zuciyata take son yarda da kalamansa,saboda bai tab'a sab'a alk'awari ba inhar ya furta zaiyi abu ko bazaiyi ba,amman kuma wani shashe na zuciyata yana k'in yarda da cewar bazai bani wahala ba.
Muryarsa ta katseni yace "Cutie nah"
Can kasa na ansa nace "uhum"
Yaci gaba da cewa "inhar kin yarda ni prince dinki bazan cutar dake ba ki saki ranki ki cire duk wani tsoro da fargaba kiyi walwalarki kinjiko,nifa ba bakon tsanani bane wlh."
Nai shiru ina jinsa ya fesar da numfashi yace "yanxu dai zakixo d'in?kinga in kika zo albishir d'in zaifi dadi ina kallon cikin idonki masu kashe mun jiki "
Runtse idona nayi saboda wani abu daya tsarga mun,ya sake cewa "my love d'ina zaki zo ko?"
Narkewa nayi ina masa shagwab'a "uhm uhmm nidai gaskiya yaya Aa"
Wata irin kasala yaji tana baiba yesa dan danan yaji mik'a na zuwar masa daker yace "shikena saida safe sai muyi magana Good night cutie na"
Shiru nayi saboda jin canji daga garesa nace "fushi kayi kenan"
Muryarsa harta dishe yace "no ba fushi nayi ba,naga idan ma na matsa saikinzo nine awahale"
Gabana ya fad'i nace "to kaya kuri"
Murmushi yayi yana runtse idonsa yace "don't mind cutie"
Asanyaye nace "saida safe"
Yace "ok bby I love u❤"
Can k'asa na amsa da cewa "love u too my prince"
Nai saurin kife wayar ina dariya shima can dariyar yayi ya kwanta rigingine yana kallon silin tabbas in ma yace zai kyale cutie gobe wlh karya yake,don wannan abun da yakeji akanta mai wahalarwa tsaf zai iya kaishi lahira,amma dole zaibi komi ahankali har ya samu natsuwa da ita yasan dai akwai daru,don haka sai yayi amfani da salo salo na dubaru da daukar hankali kafin komi ya wakana..............
Tashi yayi ya d'auko computer da wayarsa yana duba wasu abubuwa gefe guda na zuciyarsa yana tuna masa abunda ya faru d'axun yana company d'in nanah.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now