*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........35
Tafiyar tamu ta kasance so silent saidai time to time yake ɗan yimin fira sama sama,zuciyata tama son tambayarsa ya batun Auren da yace zai yi,amma na barsa zuwa wani lokaci don ina nan kan bakana wlh bazan zauna da wata tare dashi ba.
har lokacin karatun ƙur'anin ne take tashi acikin motar hakan sai ya saka mani natsuwa sosai har ina sauke ajiyar zuwa,idona rufe munata zuba gudu duk da bana son gudu so baxan iya hanasa ba bansan dalili ba,kamar daga sama naji yaje fomin wata tambaya cewa.
"Naga alamar itama Nabila irin auren da akai mana ne xa'aimata ko?"
ya faɗa da alamun som ƙarin bayani daga garen,na bude idona ina kallonsa kaɗan nace "mekagani daya nuna maka hakan?"
murmushi yayi mun yace "daga yanayin da ta nuna sadda nace ta gaida mun angon ya tabbatar mun da ba sonsa take ba kamar yadda kema kikai"
wani kallo nayi masa nace "mena nuna niɗin?"
Shafa kansa yayi yace "wai da kika nuna baki sona ba wanda kika tsana sama dani,gashinan inata fama dakon soyayyarki na gaxa samun matsugunni cikim zuciyarki,koma tausayina ba kiji" taɓe bakina nayi nace "kaida zakai Aure mexa kai da kamata "
nafaɗi haka ne badan komi ba sai sonjin ina maganar ta kwana,amma sai bai kilani ba yace "Allah yasa ƙawarki ta faɗa son wannan innocent Guy ɗin"
zaro idona nayi cike da mamakin abunda yace ganin yadda nayi yasa shi ua kama dariya kaɗan ya hana bai buga ma wano mai mota ba,jinjina kai nayi nace "Amma ka iya fata marar kyau wlh,to ina ruwanka ma tukun."
Yana murmushi "aa ba ruwana kam inason zamansu yayi kyaune kinga ita fara sonsa bazata yi masa abun da ransa zai b'aci ba."
Nace "uhmmm"
Daga nan bamu sake magana ba yana ta sharara gudunsa ni kuma na koma na kwanta ina son bacci ya d'aukeni,saida mukazo kudal local government wani gari dake under dinta hunk'uy yace "zamu siya ma su mami wani abune?"
Ba tare dana bude idona ba nace "mai zai hana,tunda can Irish potetor yana tsada."
Wurin masu siyarwa yaje ya siyo kusan tiya goma yabiya sannan aka sa masa abut suka cigaba da tafiya.
Can naji yace mun "hixub d'inki nawa Aysha."
Ba tare dana ja da nisa ba nace "biyar"
Jinjina kai yayi yace "hadith kuma na nawa kike?"
Na turo baki nace "nifa ko haqqul mubin na biyu ban gama ba."
Yace "tauhidi fa kin tab'ayi?"
Nace "eh Abbu ne yake koya mun"
Yai mun tambaya cikin tauhidin na bashi amsa ya sake yi mun na sake bashi cikakkar amsa,ya jinjina kai yana sarrafa sikiyarin cikin kwarewa kafin yace "karato mun hadith na karshe da kika tsaya"
Shiru nayi saboda kai na manta shekarun da yawa kuma yai da gobe baka biya karatu fecewa yake yana barinka,asanyaye nace "gaskiya I can remember"
Yace "Akwai bukatar ki koma islamiyya kwanan nan!"
Zaro ido nayi nace "me?islamiyya kuma?da girmana don Allah"
Maida fuskarsa serious yayi yace "Ai shi ilimi ba'a girma dashi,sai kinje zakiga akwai wadda ta haifeki sau biyar ta dawo nema,don haka ki d'auka kin koma islamiyya kin gama."
Nai shiru kawai ban sake cewa komi ba,hakan ya nuna masa banji dadi ba sai ya sassauta murya yace "Aysha na"
Banza nai masa ya sake cewa "cutie na"
Na lub ina rufe idona ganin bazan amsa ba yace "meyasa baki tambayeni dalilin da zan matsa saikin koma islamiyya ba?"
Ba tare dana bud'e idona ba nace "Saboda ka cika alkawarin Abbu"
Yace "daya kenan,sai kuma me"
Nace "shikenan abunda zan iya fada akai"
Ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa "da na bari in munje gida mun natsa sai muyi magana,sai naga kuma yanxu ma damace da zamuyi nidake."
Yai d'an shiru sannan ya cigaba "Na had'u da hafsat tun kafin ma Abbu yace ya xab'a mun matar Aure,hafsat mutuniyar kirkice kuma mai hankali da hkr sannan yarinya ce mai ilimin addini,abunda yafi jan ra'ayina akanta kenan,saboda aduniya banda wani buri daya wuce auren mata mai ilimin addini sosai saboda nasan inhar na sameta nayi dace,yarana basu da sauran wata matsala haka zalika gidana zai zauna lafiya komi zai tafi cikin tsari na islama."
"To hakan yasa dan danan sabo da shak'uwa ya shiga tsakanina da ita,har nakejin ina sonta kuma ashirye nake dana aureta da fari itace ta fara kamuwa da soyayyata,amman kunya da kawaici irin nata sai ta kasa fad'a amman ni na gane haka mukaita Alk'armu har amunce ina sonta nima,sai kuma ga maganar aurena dake data fad'o kamar daga sama alokacin da mukeji ni dake kowa baya kaunar kowa,azahiri ada ban tab'a kawo cewar xan iya jin sonki ba Aysha,saboda kullin Allah wadai nake da halayenki ina ayyana taya ma za'ace wannan ce matata,bacin ni ba haka naso ba.
To shi Allah ba ruwansa yana tsara lamurransa alokacin da yaso kuma yaga dama,sai kawai gani cikin kaunarki dumu dumu har nakan kasa bacci nakan ji kishi idan na tuna da wannan saurayin naki,ban tab'a zaton soyayyarki zata kamani har haka ba Amman da yake ba ni nakeda iko da zuciyata ba bana iya hanata,abaya nayiwa hafsat alk'awarin Aure bayan na fara sonki babanta ya nemi ganina yazo da maganar yabani hafsat duk sadda na shirya nazo asa mana rana,alokacin faisal ya bani shawara cewar na sanar da babansu cewar akwai auren ki akaina,tunanin zai janye maganar aurena da hafsat!Amman sai yace hakan ba matsala bace inhar inaso shikuma zai bani,inje duk sadda na daidaita dake na kuma shirya sai na dawo ayi magana."
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...