*NERNER AYSHER*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3561🅿️............3
Karfe takwas daidai ta gama duk wani shiri da yadace tayi,tayi wanka ta zuba kwalliya tubarkallah masha Allah duk hassadarka saika yaba ma nanah,bata kwalliyar fuska ko kad'an don ko kwalli bata sakawa.
Daga powder sai lipstick kawai take anfani a fuskarta,amman sai kaga tayi kyau kamar wata aljana.
Abaya ce ta saka cikin wadanda suka siyo jiya,Golding color da tsasha adon duwatsu sai ta yane kanta da gyalen abayar.
Ta daure kashinta yayi tudun acuci,kamar kaita daukarta hoto don kyan da tayi.
Break suke jiran Abbu ya fito suyi,Sofy sai bata rai take saboda yau dai dole za'a rabu da yaya nanah.
Kusada ita nanah ta zauna tana dafa kafad'arta tace "wai miye ne tunda kika tashi kike bakin rai?" Haba sai kwallah sharrrrrr zaro ido nanah tayi tana kallon mamin cikin mamaki tace "mekikai mata take kuka."
Murmushi tayi tace "mexan yi mafa fa da farar safiyar nan?tafiyarki ce bata so"
Jawota jikinta tayi ta rungume tana bubbuga bayanta cikin sigar lallashi tana mata magana a hankula cikin natsuwa da taushin murya.
"Inkina kuka taya zanji dadin tafiya har naje nagane wani abu,in bakison natai yau kifad'i ranar dakikeso saina bari sai ranar."
Girgiza kai tayi tana cewa cikin kuka "aa yaya nanah gara kitai zan hkr danaga baki nan."
Murmushi tayi kawai tana daukar cup din tea dinta tana bata ga baki,daidai sadda Abbun hake fitowa daga part d'insa.
Mami taje ta anshi jikkarsa tana rissinawa kallonta yayi cikin fara'a yace "sannu Rashida,Allah yayi albarka ita kuma wannan yau shagwab'arce ta motsa kome?"
Yar dariya mami tai tana ja masa kujera ya zauna ta fara had'a masa abunda zai ci tana cewa "wai nan lallashi ake tayi,kukan rabuwane akeyi."
Dariya yayi shima yana cewa "to ranar da zan aurar daku kuma sai ayi yaya sofy."
Ai saita sake fashewa da kuka ta dora kanta jikin kafadar nanah.
Bata fuska nanah tayi tana kallon Abbun tace "fisabilillah Abbu meyasa zaka sake sakata kuka,bayan na samu tayi shiru."
Had'e hannayensa yayi alamun ban hkr yana murmushi,daker sofy tai shiru nanah tai ta bata break ga baki harta koshi.
Sannan ta fara yin nata cikin yanga da salo,Abbun ya d'ago yace "sofyna jeki shirya dake zan tafi rakiyar beauty."
Ai kan yarufe baki ta ruga aguje cikin bangarensu,me zasuyi mata ba dariya ba.
Nanah saidai tai murmushi bata san wanda yafi son dan uwansa ba ita da sofy,suna son junansu matuk'a.
Abbu ya kalli mami yace "kira mun asabe"
Ta d'an kwala mata kira daga can sashen da suke saigata ta taho cikin sassarfa ta durkusa tana gaida Abbun,kafin ta gaida nanah wadda ta ansa cikin gatsali "lafiya" ta cigaba da cin palanten dinta da pork ga ferfesun yan ciki nan sai tashin kamshi yake.
Abbun yace "jeki kira mun mus'ab"
Tatashi cikin hanzari tatafi dagowa nanah tai tana kallon Abbun wanda shi sai ya nuna kamar bai ganta ba,don yasan me zatace.
Ganin yaki kallaonta yasa ta ajiye pork din tace cikin yar shagwab'a "Abbu badai wannan kazamin zai tukamu ba?gaskiya Abbu ka kyalesa kasaka mani kawai."
Bai bata ansa ba saiga asabe da mus'ab sun shigo,ta dage iyakar iyawarta ta daure fuska tamau tana cin magani.
Gaida mami yayi cikin girmamawa ta ansa masa da kulawa,tace "ka gama karyawar ne?"
Yace "eh hajiya"
Abbu yace masa "ka gama goge motar dana saka?"
Yace "eh yallabai"
"Ok kaje ka shirya zamuje kaduna mukai beauty makaranta."
Ya risina tare da cewa "to yallabai
Wani wawan tsaki taja wanda awajen babu wanda baiji ta ba,amman ba wanda ya kulata shidai mus'ab tuni ya bar falon."Dota na bana son kalar abunda kikeyi,hakan ba kyau kinjiko."
Fad'an ma kansa cikin lallama da kalami mai dadi yake mata shi,saboda kar ranta yab'aci tayi kuka.
Baki taturo tace "haba Abbu wai taya ma kake tunanin zan iya had'a hanya da wancen mai shegen girman kan tsiyar,kasan jiya soyayi ya kashemu nida sweety."
Murmushi yayi yace "yazo ya gaya mun jiya bayan na dawo yace nayi hkr tsotsai yasa ya kusan yin accident daku,hakan ya nuna tsananin hankalinsa da gudun aikata laifi,ina tausayin mus'ab duk cikin ma'aikatana ba wanda nakejin tausayinsa da sonsa irin sa,saboda shidin yasha banban da duk sauran.
Ina rokonki akan abu nafarko dana tab'a rokarki kidaina masa kalar wadannan abubuwan cikin mutane."
Sadda kanta tayi tana jin haushin kalamin Abbun,komiye abun tausayi ga wancen munafukin mutumen.
Bata ce komi ba suka cigaba da break d'insu wajen yayi tsit,mami tunanin maganar Abbu kawai take da abunda nanah tayi.
Tabbas rayuwar mus'ab abun tausayi ce don itace ma tasaka Abbun ya nema masa aikinyi acikin gidan,shikuma ya duba natsuwarsa da hankalinsa ya daukesa matsayin drivern sa.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...