*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........32
Tun bayan tafiyarta cikin d'akin ya zube cikin kujera yana sauke numfashi akai akai duka hannuwansa ya tura cikin gashinsa yana ya mutsawa,duk inda gashi yake cikin jikinsa ya mik'e tsikar jikin sa ce take tashi.
Har yanxu jinta yake cikin jikinta jiyake kamar zai haukace idonsa ya runtse yana furzar da iska a bakinsa,wata irin kasala ta sauko masa bazai iya k'irga iyakar adadin mintyn daya kwashe awurin kwance ba,shida yaji anata kiran azahar kuma ba bacci ne ya dauke sa ba.
Daker ya iya bud'e idonsa yana kallon agogo karfe d'aya na rana tashi yayi yana sauke ajiyar zuciya ya jima kansa soke ak'asa kafin ya fita daga cikin falon,can wurin mai gadi yaje ya shiga toilet d'insa ya fito ya d'aura alwalla suka fita zuwa masallaci.Ahankali nake bude idona ina mik'a nai salallami ina jingina bayana ga gadon ina k'urama wuri guda ido babu abunda yake dawo mani arai illa abunda yafafu few awas ago,lumshe idona nayi na bude ina tunanin ko ya tafi?ko yana nan?yaci abinci kuwa?
Wannan tunanin da nayi yasa nai saurin tashi na nufo falon bude kofar nayi na lek'a wayarsa na gani da key d'in motarsa,sai ledar daya shigo da ita tun d'axun.
Sai naji nayi ajiyar zuciya na koma d'akin na shiga toilet d'in wanka nayi tare da Alwalla na fito jallabiya kawai nasa na kabbaara sallar.Shigowa falon yayi bayan ya dawo daga masallacin direct kofar bedroom din ya nufa ya tura kofar ya tsaya daga bakin k'ofa yana kallonta tana zaman tahiya,karema d'akin kallo yayi yana yabawa sa kyansa yana ayyana yadda zai yi dadin bacci falo ya koma ya zauna yana xuba ruwa acup ya k'urb'a yana ajiyar zuciya,sallame sallar nayi na cire hijab d'in da jallabiyar na daura towel na fara shafa cike da kasala,har bana son na tuna abunda ya faru d'axun ban jima ba na gama na hau feshin turare saida yayi mani son raina sannan na ajiye na bude inda kaya suke a Wadrop still doguwar rigar na sake daukowa amman abaya ce bak'a mai zallar stone tai kyau sosai da sosai.
Na saka ina daura veil dinta red color na tsaya ina kallon kaina a madubi,tabbas nayi kyau sosai murmushi nayi dumfuls dina suka fito da suka sake fidda kyawuna.
Sai naji nauyin fita nakeji da wane ido zan kallesa bacin kukan da nasha ajikinsa,tuna wa danai baci abinci ba don tiren dana kawo banga alamun ya tab'a shi ba.
Plat shoe d'ina red na saka ina bude kofar ahankali cikin sand'a kafin na fito ina takawa cikin falon,duk na duburce na ma rasa ta inda zan kama sai nai tsaye daga gefen kujera ina fidgeting ya tsuna kaina k'asa.Kamshinta kad'ai ya isa ya tabbatar masa da fitowarta,idonsa suka tai loooo zasu lumshe yai saurin budesu ya sauke akanta jiyai kamar ya saceta tai masa kyau ainun guntun murmushi yayi yana jan iska yace "u look so cute kin yi kyau sosai."
Kasa kallonsa nayi sai motsa d'an bakina nake inason nayi magana na kasa ya sake cewa "kiyi maganarki mana."
Yatsuna naketa murza kafin naji nace "kaya kuri na barka da yunwa,bari naje na kawo maka abinci."
Wani smile ne mai tsada yake fitar wa yace "gaskiya ni ban hkr ba."
Saurin kallonsa nayi daman kuma haka yake so yawani narke fuska yana mutsa baki yana kwai kwayata yadda bakina yake,ganin haka yasa nasan dani yake sai na turo baki na ina daina kallonsa nace "bacci ne ya d'auke ni ban sani ba."
Iska ya shak'a yace "ya mun daidai wannan baccin,any way jeki kawo mun abincin yunwa nakeji ko nayi na kama hanya."
Na fito daga bayan kujerar muryata can kasa nakejin ta nace "baka ci naman ba har yayi sanyi,naje dashi saina saka maka oven yayi zafi?"
Yadda take maganar kamar wata yar yarinya sai soke kai take ta kasa kallonsa,hakan ba karamin dadi yayi masa ba ya shafa kanshi yace "eh zoki d'auka"
Na tako na iso inda tire d'in yake na dauki bowl din na juya zan fita naji yace "nazo na tayaki."
Jiyowa nai na kallesa na girgiza kai sannan na fice daga d'akin.Kitchen na nufa na samu masu aikin har sun gama abincin,nace "karima me kuka dafa nayi bak'o zan kai masa.?"
Tace "Ai yau kala daya akai saboda hajiya da Alhaji basa zaune shinkafa da miyace akai da coleslaw sai fefersun yan ciki amman cikin miyar ma ansaka naman rago."
Nace "ok don Allah fara had'a masa ina xuwa,amman kin san yadda ake shirya tire ko?"
Murmushi tayi tace "na sani hajiya za'ai yadda ya dace."
Nai murmushi nace "ga wannan naman ki sake d'uma ma shi saiki had'o dashi,basai kin saka naman miyar ba."
Tace "to yar gidan hajiya"
Murmushi nayi na juya na koma can falon na samesa yana waya idonsa akan tv,ina shigowa ya maido idonsa kaina tsura mun ido yayi ya daina maganar da yake na yan seconds kafin ya lumshe idonsa yana cewa "kai ni nama daina fahimtar me kake cewa."
Hannu ya mik'o mani alamar inxo na mak'ale kafad'a murmushi yana sake mik'o hannunsa,har alamun rok'o yana cewa awayar "wai kai ina ruwanka haka nan bazan zo ganinta ba sai da dalili,okk to gata nan bari na bata ku gaisa daman baku tab'a gaisawa ba."
Yana cire wayar daga kunnensa yace kasa kasa "don Allah kixo faisal ne abokina yake son ku gaisa."
Sai sannan na isa inda yake kamar jira kau yake in isa ya cafkeni ya jawoni gefensa ya zaunar,harararsa nayi ina anshe hannuna wayar ya samun ga kunne yana mun alamar nayi magana.
Cikin siririyar muryata nace "ina wuni."
Duka idonsa ya zuba masa komi tayi kara burgesa take,duk motsin da zatai jiyake son da yake mata yana hauhawa.
Faisal yace "lafiya lau amaryar mu ya kd d'in?"
Ahankali nake amsa masa ina jujjuya yatsuna nace "Alhamdulillah lfya lau."
Yace "shine kika azzira masa saida ya baro aikinsa ya taho wurinki ko?"
Na turo baki nace "nifa banma san zaizo ba bani na kirasa ba Allah."
Dariya faisal yayi shi kanshi yana yin yarinyar yana burgesa akwai natsuwa dai ga class
Yace "anya kuwa zan yarda? saboda naga alamar kin rikita mun abokina da yawa,to adai kula mun dashi har yadawo saboda inaji dashi sosai"
Nace "uhm shikenan ngd agaida mama"
Yaji dadin maganarta yace "zataji insha Allah"
Na zare kunnena ina kallonsa murmushi yake idonsa akaina yake cewa "karka sake kirana ina busy yanxu"
Dariya yayi yana kashe wayar daidai anyi knocking k'ofar na tashi naje na bud'e karima ce da abincin da ta shiryo,kuma ya tsaru sosai ina mata murmushi nace "nagode sosai karima"
Tace "ba komi ai aikina ne"
Saida na shigo da tiren na ajiye sannan na dauko wanda na fara kawo masa na mik'a mata nace "ki canzo lemun wannan sun huce."
Cikin girmamawa ta ansa
Ta juya ta koma na tura k'ofar sannan na iso na ajiye k'asa ina d'agowa yace "sannun ki"
Kai na d'aga masa na nufi hanyar bedroom dina cikin sauri yace "ina kuma zaki?"
Na b'ata fuska nace "kaci abincin don Allah"
Narkewa yayi yana wani bina da kallo na juya idanuna na dauke kai yace"ki dawo fira zamuyi plzzz"
Yadda yayi maganar kad'ai ya isa ya kashe mun jiki,na sadda kaina ina wasa da gefen veil dina bance komi ba ya sake cewa "kinji AYSHER"
naturo baki na ban kallesa ba nace "zan dauko phone d'ina aciki ne"
Lumshe ido yayi ni kuma na shige jingina bayana nai da k'ofaf inajin yadda zuciyata take beating,meye haka?
Na tambayi kaina ina shafa fuskata na ja iska nace "wai duk wannan abun da yake duk na miye wlh ni nakasa d'auka"
Na fad'a kamar zan kuka wurin mirror na isa na dauki wayar ina kallon kaina idona duk ya wani lumshe kamar ina jin bacci,na jima sosai kafin na samu na fito daga d'akin.
Na tadda har ya xuba yafara ci na zaga daga can gefe na zauna cikin one seater ina satar kallonsa,dana ga zamu had'a ido sai in d'auke kaina.
Shiru duk mukai ba ruwansa abincinsa yake ci cikin natsuwa yana yi yana duba wayarsa yana dannata,jinai yace mun ba tare daya kallan ba.
"Zaki iya zuba mun ruwa a cup pls"
Na aje wayar na sauko na dauki ruwan da karima ta kawo da lemu na zuba masa sannan nace "lemun fah"
Ya dan saci kallona wani kalar kallo yai mun kafin yace "saina gama zan sha,ke baki cin abincin banga kinci wani abu ba tunda nazo."
Ina rufe jarkar ruwan nace "ni bana cin abincin rana"
Zaro ido yayi yace "bcos?"
Na koma mazauni na nace "ra'ayina ne haka,sai bayan magrib zanci daga nan sai safe kuma."
Yajin jina kai kafin ya d'an kallan sama da k'asa yace "kuma kike k'iba abunki"
Kallon kaina nayi nace "nice ma nake k'ibar?bacin duk karatu ya ramar dani."
Na fad'a ina turo baki murmushi yayi yace "janki nake kiyi rama amman ba da yawa ba,duk da nayarda karatun zai iya ramar dake amman deep down akwai wani abu ko?"
Na d'an hararesa kadan nace "Aa bakomi karatunne kawai"
Ruwan yasha yace "inkika sake hararata zaki sani."
Nad'an murgud'a baki gefe ina duba wayata naga miss call din wasila tun d'axun ta kirani,naji yace "me faisal ya gaya maki daxun"
Nace "oho na manta ka tambayesa mana."
Murmushi yayi yace "baki manta ba baki dai gaya mun ne kawai,kuma naji komi daya fad'a."
Nai masa wani kallo nace "meyace to?"
Ajiye plate d'in yayi da yaci rabin abincin yana zuba lemun da kanshi yace "ba cewa yayi kin rikitani ba kuma ki kula masa dani saboda yana ji dani,koba haka yace ba"
Zaro ido nayi nace "ashe kasa kunne kayi kana jin meyake fad'a"
Yace "to ai banji kince masa zaki kula dani d'in ba"
Na dauke ina cewa "gashinan na baka abinci kana ci."
Murmushi yayi yana koma wa cikin kujera ya jingina yai mun k'uri kafin yace "wannan yayi kad'an gaskiya"
Na b'ata fuska nace "to me zanyi maka? kazo nai maka sannu da zuwa na tarbeka da abun sha sannan na kawo maka abinci gashi nan ma ina maka fira."
Dariya yayi kadan yace "haka ne kuma,daman Annbi yace ka fara tarbar bak'onka da abunsha kafin komi,ngd sosai Allah yai maki albarka."
Na sadda kai guntun murmushi yana son fitowa afuskata kasa kasa nace "Ameen"
Duk sai mukai shiru ina jujjuya wayata yayin da nakejin kaifin idonsa akaina wad'anda suke sani jin duk a d'aure nake,gajiya nayi na b'ata fuska ina kallonsa nace"don Allah ka daina wlh ni takura nake in ana kallona"
Murmushi ya saki mai dan karen kyau daya daki zuciyata,na kasa kauda idona akansa lumshe idonsa yayi yana kallon agogon dake d'aure tsintsiyar hannunsa ta kamfanin swiss brown color yace"saidai kiyi hkr ba laifi na bane"
Nace "kamar ya ba laifinka bane?ba idanuwan ka bane kuma ajikinka suke"
Ya shafa kanshi yana murmushin yace "to ai bana sanin suna kallon naki,kiyi masu kashedi kila su daina."
Na turo baki ina murgud'ashi ya zaro idonsa yace "hararata kike?"
Kamar zan kuka nace "to bakai bane ba"
Wani yammm yaji cikin kansa ya daure yana d'an shan mur yace "zonan"
Idona duk na fiddo waje nace "to ka ya kuri nidai kabarni nan don Allah."
Ya sake d'aurw fuskarsa amman cikin ransa wani irin nishad'i da farin ciki yake jinsa aciki yace "ohh kinfi so ni inzo kenan?"
Hannuna na yarfe ina nuk'u nuk'u fuskata kamar zan kuka sai motse motse nake a kujerar nace "Aa basai kazo ba,don Allah ka ya kuri na daina"
Ganin zai taso yasa nai saurin mik'ewa na dawo gefensa cikin two seater na rab'e can gefe ina kun kunin kuka,saboda wannan salon nan da yake mun rikitani yake har inda bana zato yana yin kaimin yake.
Sassauta fuskarsa yayi yace "tsorona kike."
Na girgiza kai "to motse motsen me kike kin mak'ale jikin kujera."
Muryata da sanyi qalau nace "Ni dai kabarni na koma wurina anan bana jin dadi."
Idonsa sun wani juye yana jefarta da wani irin shu'umin kallo da shi kanshi baisan yana yi ba saurin daina kallonsa nayi na turo baki jinai yace "naga alamar dai so kike na sha wannan bakin"
Zabura nai ina saurin toshe bakina idona duk awaje tsoronsa ma ni ya kamani,nai saurin tashi har sannan hannuna saman bakina.
Dariyarsa yake dannewa yace "dawo nan karki sake ki fita."
Idona yayi rau rau da kwallah nace "don Allah ka ya kuri wlh niba haka nake nufi ba,abun ne yabi mun jiki amma zan daina bazan sake ba."
Ganin ba zata dawo ba yasa ya tashi ya nufoni jikina wani irin tsuma yake kafafuna sunyi sanyi sosai daf dani ya tsaya naji ya kamo hannuna muka dawo muka zauna,ya matsoni sosai har zuciyata tana bugawa basan wane irin so wabane wannan mai wahalarwa,ba haka na saba yinsa ba wannan yana matukar gajiyar dani yana sani jin kamar zan zare.
Muryarsa tai sanyi sosai har saida na lumshe idona saboda yadda take ratsani yace "Aysha na"
Shagwab'e fuska nayi nak'i amsawa wani gauron numfashi ya sauke yana tallabo hab'ata ya sake cewa "kallani nan meyasa kike guduna?"
Jinai zan narke a wurin na sunkuyar da kaina ina girgiza kai alamun ba komi,ajiyar zuciya yaja yace "in tambayeki?"
Nan ma d'aga kan nayi ban sake kallonsa ba ya cigaba da cewa "yanxu kin hakura zaki rayu dani matsayin abokin rayuwarki?ko kina ganin har yanxu kina kan ba kanki na cewar ba kya sona kuma bazaki zauna dani ba."
Kamar saukar aradu haka naji maganar ta daki zuciyata da kunnuwana,ahankali nake d'ago idona ina kallonsa ya wani lumshe idonsa ya bude yana kallona.
Kasa magana nayi saboda ban san abunda zance masa ba yace "kinji abunda nace kuwa?"
Na d'aga kai hannuna ya kamo cikin nasa yana kallon hannuwan namu ahankali ya d'an matsa shi na kallesa ya daga mun gira,har zan turo baki sainai saurin fasawa.
Murmushi kawai yayi yace "ina jinki kice wani abu."
D'an juya wa gefe nayi ina anshe hannuna sai murzar yatsuna nake nace"saboda kana son kara aure yasa kake mun wannan tambayar?"
Saurin girgiza kai yayi yace "wlh ba dan haka bane kawai naga lokaci yayi daya dace mu fahimci juna,mu yadda maka man mu."
Nace "uhm ya batun auren ka da kai mun magana jiya."
Yace "sai naji daga gareki idan kin hkr zaki rayu dani."
Na rausayar dakai nace "nasani ada ina adawa da Auren mu bama kad'an ba,saboda Abbu ya riga ya yi mun shigar sauri bayan ina da wan nake so,to amman bakin alkalami ya riga ya bushe an daura kuma ni ban isa na warware ba,haka zalika bazan iya bujirewa umurnin Abbu ba saboda ya mun komi arayuwata duk abunda nake so yayi mun to mexai hana saud'aya dai bazan yarda da shi abunda yake son ba,shiyasa kawai na hkr nayi biyayya da fatan hakan zai sashi cikin farin ciki,don haka ni tuni na hkr zan zauna dakai Aman saida sharad'i guda"
Tunda ta fara magana yake kallon d'an bakin ta miyau kawai yake had'iya ba tun yau yakejin sha'awar shansa ba.
Saida yaji takai aya yaja iska yana jinjina kai yace "zaki zauna dani duk da baki sona?sannan wane sharad'ine kike son fad'a?"
Nai yar ajiyar nace "ba kaina aka fara aure babu so ba,don haka zan zauna dakai ahakan sanan sharad'in shine matukar har zaka k'ara aure bazan zauna dakai ba"
Murmushi yayi amma sai yai saurin kawar dashi cikin serious tongue yace "ban gane ba?kina nufin bazan auri wata ba kenan?"
Na jiyo ina kallonsa nace tabbatarwa "eh haka nake nufi."
Ya shafa kanshi yana jujjuyasa kafin yace "Ai na d'auka yin aurena bazai dameki ba,bama d'aya ba ko nawa xan aura na zata hakan bazai dameki ba tunda zaki zauna dani don dole tunda baki sona,amman inhar kika ce bazan auri wata ba ai kamar kina........"
Saurin kallonsa nai idona waje da fargaban me zai idasa fad'a nace "ina me?kaga bafa zanji kishin ba ne yasa nace haka kawai dai bana sone."
Kunshe dariyarsa yayi yana cewa "naji wannan zanyi tunani akai,amman kukan me kikai jiya muna waya daga nace maki naje zance wurin hafsat."
Wani kallo na wurga masa na tashi kawai zan barsa anan saurin rikoni yayi saidai naji ya zaunar dani samaj cinyarsa,cike da firgice nai saurin yunkurawa zan tashi ya sake zaunar dani,duk na rikice nace "don Allah kabarni miye haka,to shikenan zan zauna na fasa tafiyar amman ka barni na tashi ana...........hucin numfashinsa naji ga fuskata da yasa maganar ta mak'ale ban san na runtse idona ba jikina yana wata irin tsuma,har sannan numfashinsa kawai nakejin yana sauka akan fuskata na daskare a wurin tsikar jikina wani tsammm take tashi,hankalina ya mugun tashi har wata yar kerma nake.
Wani mugun miyau yake had'iya so yake yai control d'in kansa ya kasa so yake ya daina jin abunda yake fizgarsa zuwa ga bakinta amman abun ya faskara,shima bai sani ba bai aune ba yaji kawai bakinsa da nata sun had'e wuri guda..........
Su duka saida suka wani dogon numfashi sai naji na kasa janyewa,jikina yai wata mahaukaciyar mutuwa ko hannuna na kasa d'agawa,d'an light kiss ya sakar ma bakina muuaaah sannan ya had'e hancin mu guri guda muna musayar iska sai naji nawa kamar mai asthma yana fita da sauri da sauri.
Hannuwansa yasa yana zagaye k'ugana dasu dagani harshi idonmu a rufe yake muryarsa dan danan ta dishe naji yaki ra sunana "Aysha"
Kamar na kurma ihu nakeji saboda abunda nakeji kamar zai hallakani,ban san meyasa naji ina shashshekar kukan karya ba wanda babu hawaye,kuma kamar kukan shagwab'a haka naji yana fitowa ban san abunyi ba haka ban san nayi ba.
Jinai ya idasa rungumeni jikinsa dan danan nahau wata kerma ta rashin makama,shashshekata kuma tana karuwa na kank'ame jikina jinai ya sake sakar mun wani kiss din wannan karon da zafi zafinsa,sai kawai na ida kwanciya jikinsa na saka kukan da babu hawaye.
Yadda naji ya rikice abun ya bani mamaki magana yake son yayi mun ya kasa,nima kuma banda kukan bansan me zanyi ba,abune sabo wurina da yazo mun ga gab so bansan ya zanyi ba.
Hannunsa ya saka ya tallabo fuskata gefe da gefen bakinsa kusa da nawa yace murya na yar rawa "Menene"
Wani kukan na sake sakar masa wannan karon harda hawaye ban san meyasa ba,sake rikicewa yayi yace "plzzz tell me menene?kina so nima nayi kukan"
Nai saurin girgiza kai yace "ok stop it"
Sai lokacin na iya fiddo maganar muryar na rawa jikina tsuma yake sosai nace "ni......n....ban....bansan.....yazan ya daina ba ai."
Sai kurin naji sassanyen halshensa yana bin kuma tuna yana lashe ruwan hawayen,cikin wani irin salo da yasa ni jin kama zan sume.
Saida ya gama lashe su tasa can kasa yace "in suka sake fitowa irin haka zan masu."
Nai tsit ko tari na kasa yi d'agoni yayi jinai kamar zan mutu don kunya,azabure na tashi zan ruga d'aki yace "kina guduwa zan biyoki"
Na daskare awurin sai shashsheka nake yace "tafiya zanyi yanxu la'asar tataho."
Saurin jiyowa nayi nace "yanxu kuma?baku gaisa da yadidi ba don Allah ka bari ku gaisa zuwa magarib zata dawo"
Yace yana fiddo ido yace "so kike ai mun dukan tsiya a hanya?"
Na bata fuska nace "sai ka kwana da safe saika juya."
Hannunsa yasa cikin aljihu yana mun wani makirin kallo,na turo baki ina kauda kai yace "kina son k'ari kenan"
Nace "meke nan?"
Bakin sa ya nuna sai kawai na ruga nabarsa nan tsaye dariya ya sanya cike da tsananin nishad'i zubewa yayi kan kujera yana saki iska tare da murmushi,bakinsa yake shafawa cike da kwad'aituwa kari yake so koma fiye da haka amman not now akwai lokaci sai ya sata ta susuce sannan,saiya nuna mata bata da wayau anan wurin duk wata wayewarta zai nuna mata ta banza ce asannan zai iya gabatar da soyayyarsa lokacin da yasan bata iya guje masa bata iya kauracema soyayyarsa,yanxu yasan wahalar dashi zatai muddin ya furta mata amman zai bita ahakan yaga darasin zai matukar lallasata cikin ruwan sanyi,mik'ewa yayi cikin kujerar yana lumshe idonsa yana ciki tunanin bacci ya sacesa mai cike da nishad'i.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...