*NERNER AYSHER*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3561🅿️..........13
Bazan iya cewa nai bacci ba saboda tunda na koma d'aki na makure can karshen gado ina rarraba idanu,amatukar mugun tsorace nake kuka nake sosai da sosai kunnuwana har sannan ji suke kamar ana harba bindigar,danaji d'an motsi konice nayisa saina zabura bantab'ajin tsoro matsanan ci ba irin wannan,dana kulle idanuna mugayen mutanen nake gani kewaye damu,sai dukan da aka ringa ma wannan d'an sunnah d'in yafi komi tayar mun da hankali nai zato kashesa zasuyi.
Ahaka naita kerma ina makurewa jikin bango,har aka kirayi sallar asuba.Sai lokacin wutar gidan ta dawo,wata gauruwar ajiyar zuciya na sauke ina saukowa na nufi bayin saboda wani fitinennen fitsari dake addabata.
Mami da sofy d'aki guda suka idasa kwana suka makale juna,har aka kira Asuba tare suka tashi kowa na sauke ajiyar zuciya,don gani suke zasu iya dawowa.
Koda sukai sallah mami bata koma ba sofy ce ta koma saboda baccin dake idonta,bayan ta kwanta kamar minty biyu ta tashi afirgice har taba mamin tsoro tace "lafiya miye haka."
Kwallah suka zubo mata sharrr tace "mami yaya..........sai kuka ya kubce mata ta soke kai tana ta rera shi.
Tasowa mamin tayi tazo saman gadon ta zauna tana jawota jikinta tana lallashi tace "ya isa haka insha Allahu babu abunda zai samesa, ki kwanta ki runtsa ko yaya ne kafin gari ya waye muje mudubasa."
Kwanta watai tana ta ajiyar zuciya mami taja mata bargo ta rufe mata jikinta,kasancewar ana sanyi ba laifi.Laximi mamin tai tayi har gari yayi haske sosai,sannan tatashi ta nufi kitchen wajen masu aiki don ganin yadda aikin yake,gaisheta sukai tare da jajantama juna abunda yafaru,da kanta take shiryama mus'ab abunda zai karya dashi saboda har cikin ranta mugun tausayinsa takeji,hankalinta yayi matukar tashi jiya bata zaci zai samu kwarin guiwar fuskantar wadanna mugayen ba.
Bayan nayi salla nakoma saman gado na kudundune ina adduar bacci ya daukan don idanuna har yaji suke,vibrate d'in phone d'ina naji nai saurin tashi cike da tsoro,kallon kiran nayi dan danan na sauke ajiyar zuciya ganin sunan *life partner* yana yawo saman screen d'in wayar.
Jawota nai ina sauke ajiyar xuciya,picking nayi nasaka ga kunnena.
Saidai tun kafin nayi magana zuciyata da kwalwata suka fara tuno mun da kalamansa na jiya.*_BAKE BA WANI AURE DAGA NAN HAR KARSHEN RAYUWARKI SABODA NINE MIJINKI,KUMA AURENA DAKE AUREN ZOBENE BABU SAKI DON HAKA KI GAGGAUTA SALLAMAR WANNAN GUY D'IN KAFIN KI FUSKANCI MUMMUNAN B'ACIN RAINA_*
Ras ras gabana ya soma dokawa har ban san ma hamid yana ta mun mgn ba,daker na dawo hayyacina.
"My Partner kina jina kuwa."
Lumshe idona nai wasu ruwan hawaye suka silalo mun,mai makon nayi magana sai kawai na fashe da kuka mai tsuma rai,samm ni ba ma'abociyar kuka bace kafin rasuwar Abbu,hasalima nakan mance da ana kuka don ba'amun abunda zai b'ata raina balle har nayi hawaye,amman yau gashi babu Abbun dake kokarin ganin yasaka rayuwata farin ciki,tun ranar dana rasashi idona bai k'afe ba why!? why? rayuwa take neman juya mun baya.
Rud'ewa hamid yayi kamar zai fito ta cikin wayar yace "innalillahi partner kuka kike yi?meya faru?kinga ban kira da daddare ba ko shiyasa kike kuka,don Allah kiyi hkr kinjiko akwai maganar da nakeso muyi dake kiyi hkr partner karki saka hankalina ya tashi."
Shashsheka nake ina zubar kwallah nace "hamid bazan iya rayuwa mai dadi idan bana tare dakai ba,duk wanda naka sance dashi inhar bakai bane ba zanyi farin ciki ba,kaine nake tsara duk wani mafarkina dakai ba wani ba,ya zanyi hamid! ya zanyi!"
Na sake sakin wani kukan allah sarki shikam duk ya gigice yace "kiyi hkr partner nai ma momy bayani tace ta amunce na kawoki ta ganki,dady baida wata matsala inhar kin amunce muyi auren bayan aure saiki koma makarantar."
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...