*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........27
Muna gama sallar isha muka fito mu duka ukun wasco ni sai Nabla wadda jamil yaketa faman kiranta awaya saidai tayi reject bama tabari ta tsinke ba,aa rejecting take yadda zai gane tana ganin kiran dauka ne bata yi.
Saidai na girgiza kai kawai nai shiru saboda dai inada tabbacin Nabla nan gaba zatai danata sanin abunda takeyi,don nayi banji dadi ba wasco keta mata masifa tana cewa.
"Ba daidai bane abunda kike yi,ai basai kin yake masa waya zai gane baki sonsa ba,ya sani kuma duk da haka ya kiraki saiki dauka koda baki maida doguwar magana ba,amman wannan salon wulakancin bai da dadi."
Dogon tsaki taja tace "bazan dauka d'in ba idan har yaji haushi yaje yace ma dady ya fasa auren hakan kawai zaiyi insan yanajin babu dadi."
Murmushi kawai nayi nace ma wasco "kinga wasila rabu da Nabla b'ata bakin ki kawai zakiyi don ba saurarenki zatai ba,kibari zata gane nan gaba."
Wani banzan kallo ta jiyo tana yi mun nace "ehy nace zaki gane nan gaba sannan karki sake ki nemoni don neman shawara ko ki kawo mun kukanki."
Tace "nasan abunda kike mun fata kuma bakin ki ya sari d'anyen kashinki na gobe da safe,kullin ina adduar kar Allah ya doramun wahalar da ya dora maki,don soyayya irin wadda kike ciki ko bana fatan nasamu kaina aciki."
Nace "saikiyi ai,nima bani na sama kaina ba kuma shi Allah idan ya tashi yin Abu baya shawara da kowa xartarwa kawai yake,don haka ki iya bakin ki don nafad'i abunda yafi naki."
Ai sai kawai mukaji ta saka kuka wiwi tana yi tana cewa "wlh inkika cigaba da mun fatan fadawa soyayyar jamil kin cuceni keda Allah bazan yafe maki ba"
Me zamuyi ba dariya ba nida wasila sosai muke mata dariya har ina tintsirawa,saboda inkaga yadda takeyi bilhakki da gaskiya kukan take tana magana tsakaninta da Allah.
Saida mukai mai isarmu sannan wasila tace "to kiyi hkr bazamu sake yi maki fatan haka ba,ki dawwama da kiyayyarsa hakan ya maki."
Ta banza damu inata yar dariyata nace "nifa ba fatan haka nake maki ba nabla,saboda ko mak'iyina bana masa fatan shiga halin da natsinci kaina kedai ki rok'i Allah zab'in Alkairi amman karki zurfafa k'iyayyarki."
Shiru tayi yana ajiyar zuciya kiran jamil d'in ya sake shigowa na kalleta nace "ki dauka kiji abunda zai ce maki kiringa tausar zuciyarki don Allah Nabla"
Ranta babu dadi ko kadan ta dauka batai magana ba,shikuma bawan Allah yace "I'm sorry inata damunki mama ce take son magana dake nazo kano ne."
Kamar ta kurma ihu haka takeji ta danne zuciyarta kamar yadda nanah tace mata tace masa cikin dishashshiyar murya.
"Inajin ka sai ka bata ai."Ya ba mamar tashi cikin faran faran tace "kina lafiya Nabila ya makaranta da jarabawa jamilu yace jarabawa kuke."
Tace "eh lafiya lau makaranta,ina wuni."
Tace "lafiya lau Nabila to Allah yabaku sa'a kinji ko Allah yasa agama asa'a."
Tace "Ameen nagode."
Sai ta mik'a ma jamil d'in wayar yace "saida safe Ayi karatu lfy."
Taja dogon tsaki tana sauke wayar cike da k'unan zuciya,yadda duk danginsa suke sonta abun yake bata haushi,ta bar hakan matsayin kwadayin dukiyar ubanta kawai suke ba son gaskiya bane.Nace "to ba shikenan ba,amman yanke wayar bai da Amfani irin yadda kikeyi"
Bata sake magana ba ta dauki kayan karatun ta tamatsa can gaba damu wasila tace "kinga nanah bari na naje department d'inmu."
Nace "sai kin dawo to."
Tana tafiya nima na bude computer na na soma karatun ahankali duk da tarin damuwar dake dank'are cikin zuciyata hakan bai sa nakasa karatun ba...........*******
Yana dawowa sallah zainab ta kawo masa tea ya ansa yana mata sannu,tsayawa tayi gefe sai ya kalleta yace "zainab akwai wani abunne?"
Ta sadda kai k'asa tace "yaya daman magana nake so nayi dakai."
Ya kurb'i black tea d'in yace "uhum ina jinki xauna a can"
Ya nuna mata kujera sai taje ta zauna tana ta tsefe yan yatsunta tace"yaya mus'ab kagafrceni da abun da zan fad'a,sadda nazo gidan nan nazo ne da nufin muyi aure nida kai,saboda hakan shine burina to bayan wani lokaci ina zaune daku sai na fahimci ni ba irin matar da ta dace dakai bace,bayan haka ma kana da matarka mai aji kyakkyawa son kowa k'in wanda ya rasa Anty nanah mace ce har mace wadda dukkan wani namiji bama kai ba zaiso ace ya mallaketa,tana da ilimi sannan wayayya yar boko kuma tana da kirki wanda ba lallai farat d'aya ka gane kirkinta ba,nasan zakai mamakin nace tana da kirki duk da yar tsamar da muke da ita,to wannan ba komi bane akan kirkin Anty nanah wannan yana daga cikin abunda yasa nace *NA HAK'URA DAKAI* yaya mus'ab saboda dai bazan iya kishi da Anty nanah ba,saboda ta ko ina ta dameni ta shanye sannan idan nai duba da irin kalubalen daka shiga akauye da irin gori da cin mutuncin da iyayena sukai maka sai inga munso kanmu idan muka nace saina aureka,shiyasa na zauna naima kaina fad'a na yanke wannan shawarar zan koma cibiyayi naje can naci gaba da zama har Allah yabani dai dai dani,kukuma nayi maku fatan alkairi arayuwarku shiyasa nace bari nazo na gaya maka sati mai zuwa saina shirya ka sani mota na koma gida."
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...