part 41

175 19 4
                                    

*_NANAH AYSHA_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)

🅿️........41&42

Duk ilahirin jikinta tsuma yake saboda dai har yau fafa kwarjini yake mata don ma yanxu babu tsoronsa irin na wancen karon daya addabamata har yaje aka aura masa ita ba tare da yardar ta ba,ta kasa zama haka ta kasa tsayiwa wuri guda sai yan jeka kadawo taie cikin office d'in nata,da sanyin AC ya gama jik'asa sai rab'a yake ga k'amshi mai dadi yana tashi.
Zuciyarta taji ta amsa lokacin da aka bude k'ofar aka shigo,tare da k'amshinsa suka shigo wanda dan danan ya mamaye office zaka d'auka ma babu wani k'amshi sai nashi,daskarewa tayi wuri guda tana had'e gabas da yamma kudu da arewa amman cikin zuciyarta gabanta keta fad'uwa ba k'ak'k'autawa.

Tsaye yayi shima daga bakin k'ofar yana kallonta kamar yadda take kallonsa,saidai shi murmushine kwance saman fuskarsa mai kyau sab'anin ita da fuskarta take had'e kamar hadarin dake shirin zubda ruwa.

Dogon tsaki taja tana kauda kanta gefe ta koma cikin kujerarta ta zauna tana dudduba file's din k'arya don babu abunda take ganewa aciki,bud'esa kawai take tana dube duben iska.

Tsinto muryarsa tayi yana cewa cike da natsuwa "DR abani izinin zama kinsan jikin tsufa ba jurar tsayuwa nake sosai ba,ba wuya kiga na zube anan."
Wani banzan kallo ta jefa masa tace cikin muryarta data dishe, "Ai bani na kiraka ba,kaga don Allah kana iya juyawa ka koma inda ka fito ni bana da lokacin saurarenka aiki nake ko baka gani ba."
Tsura mata idanunsa yayi yana ganin yadda bakinta yake magana hallau dai bai canza ba sai ma kyau da ya k'ara yi masa,miyau ya had'iye yana murmushi janye idonta tayi saboda yana iya gano weakness d'inta cikin idon,don bata iya jirar kallonsa haka koda bata iyawa balle yanxu da fafan ya k'ara zama wani k'usa kud'i da hutu da jin dadi sun ratsashi fiye da da,rungume hannunsa yayi ga kirjinsa yana sake tsareta da idonsa don tabbatar da abunda take fad'a,amman azahiri ga rikicewa da rudewa nan sun bayyana tattare da ita wanda bazai iya gane kona meye ba!.

Gyaran murya yayi yace "muddin baki bani iznin zama ba nikuma ahaka zan ta tsayuwa,wanda hakan na nufin ko lokacin tashinki yayi babu inda zaki,har sai kin saurareni."
Cike da b'acin rai take kallonsa tace "wai wane irin fitina ne wannan?meyasa kake son hargitsa mun zaman lafiyata ne?duk tsawon shekarun nan baka tashi nemana ba sai yanxu?to ni kuma ban shirya saurarenka ba,don baka da abunda zaka gaya mun yashiga kunnena balle har na yarda."
Tatashi tana harhard'a kayayyakinta don gida zata tafi bazata iya daukar wannan tension din ba,a fusace tafito daga kujerarta tana nufo k'ofa inda yake tsaye ya rungume duka hannayensa ga kirji yana kallonta kawai.
Tana zuwa taci burki tana jan numfashi taja kai gefe tace cikin raunanniyar murya kamar zata fashe da kuka, hannuwanta biyu ta had'e alamun rok'o da magiya "na rok'ek'a da girman Allah ka fita arayuwata,wlh ni bana jin son sake zama inda kake ni tuni na manta da nayi rayuwa dakai don Allah ka tafi ka manta ka tab'a sanina shine alkairin mu."
Idonta ya cika da kwallah kallon juna suke yayin da jikinsa yai masifar sanyi yana tsuma,inama zai ji rok'on da take masa!inama zai iya fita arayuwar tata!Amma inaaa bazai iya ba bayajin rayuwarsa ta cika full inhar bata dawo cikinta ba.
Muryarta da rawa tace "zan wuce ka bani hanya"
Sai ma ya sake tare wurin yana kallonta yace "inkinga na matsa daga nan wurin RAYHA to kin saurareni,wlh tallahi Rayhana ba da cuta nazo maki ba ki saurareni zaki fahimceni............babu komi cikin rayuwa dakai ba face zalinci da cuta,taya kake zaton zan sake dawowa."
Dafe kansa yayi don har ya fara sara masa yace "Rayhana wai kina son ki kashe ni ne?so kike na mutu ne akanki meyasa bazaki nami second chance ba"
Hawayenta suka fara layi ga kuncinta tace "niba Allah bace dazan kashe ka ba fafa,da zaka kyaleni wlh da zanfi jin dadi"
Idonsa ya fara kad'awa zuwa jaa yama rasa ta inda zai kamo mata,meyasa ta koyi taurin kai har haka da bata da gardama.
Ganin yadda take hawaye yasa sai ya ja gefe yana bata hanya cikin sanyin murya yace "kiyi hkr da ta kurawata ba haka nake ba,inayin hakan ne ga dukkan abunda yake da muhimmanci a rayuwata wanda na d'aukesa da daraja ne,kije bazan sake takuraki ba na dawo rayuwarki ne saboda gano wasu abubuwa da suka faru ab'oye wanda ban san dasu ba,wanda hakan yaja na rabu dake ba tare dana shiryama hakan ba,shiyasa na dawo da kwarin guiwata saboda na wanke laifina na kuma nemi yafiyarki tare da yi maki babban albishir,Amman gashi ko ganina ma bakyaso inda nake ma kokarin barisa kike.
Bazan hana ki ba Rayha kina da damar da zakiyi duk abunda kike so,kije duk sadda kika shirya saurarena k'ofa abud'e take"
Ya kamk hannunta ya saka mata card d'insa dake d'auke da sunan sa phone no d'insa da address din office d'insa,sannan ya saki hannun ya na bud'e k'ofar zai fice.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now