*NERNER AYSHER*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3561🅿️............5
"Yallab'ai kayi hkr nayi silar bacin ranta."
Murmushi abbun yayi yana mik'ewa yace "kyaleta mus'ab nasan maganinta,kaidai ka cigaba da hkr dasu wataran zata canza har sai kayi mamaki."
Jinjina kai yayi sannan suka wuce inda sukai parking motocinsu suka shiga suka kara ma bujensu iska.Tafiya suke yayin da mus'ab ya bada gaba ki d'aya concen dinsa akan tukin da kuma titi,kafin yaji alert ya shigo masa lalubo wayar yayi ya duba yana yi yana duba titi.
Zaro ido yayi yana mamaki tsoro ya shigesa cikin girmamawa da ladabi yace "yallabai kamar kayi kuskuren no"
Murmushi Abbun yayi yace "Aa mus'ab ba kuskure bane ina sane,kaf kud'ad'ena ne na cikin account na turo maka inason ka ajiye su wajenka har saina nema."
Cike da ladabi yace "to yallab'ai"
Suka cigaba tafiya Abbun yace "mus'ab don Allah ina rok'onka alfarma koda baninan ka kula mani da iyalina,kazama jigonsu ka zame masu bango majingina koda baka cike masu gurbina ba ya zama karage masu rashina tatttare dasu."
Cikin damuwa da tashin hankali yace "yallab'ai meyasa kake duk wadannan maganganun?don Allah kadaina hankalina tashi yake,rayuwa ai hannun Allah take babu abunda zai sameka"
Girgiza kai yayi yace "na sani mus'ab ina fad'a ne saboda yana yin rayuwa yau kana raye ba lallai ka kai anjima ba,kaidai kayi mun wannan alkawarin."
Kamar zai kuka yace "shikenan yallabai nai maka alkawari insha Allah bazan zamo mai cin amanarka ba,domin ka fiddoni daga cikin kangin rayuwa ka kawo ma rayuwata haske wanda ban zaci san samesa ba.""Ganin farko da nayi maka zuciyata ta amunta dakai,shiyasa har na sanyaka cikin iyalina,mus'ab inson ka zama namiji jarumi kuma tsayayye ta haka ne zaka iya sarrafa *nernerh* ka daina shakkarta ka daina tsoronta,ya zama kai take tsoro ba wai kai kaji tsoronta ba.inason ka koya mata tarbiyyar dani na kasa bata,inason ka koya mata rayuwa mai kyau wadda nakasa ankarar da ita,ta gane cewar kudi basune rayuwa ba,kuma don kana da kudi bashi zai kawo farin ciki cikin rayuwar mutun ba,ta kasa fahimta har yau saboda gani take inhar kana da kudi ka wuce raini kafi karfin komi,don Allah mus'ab kayi mun wannan alkawarin"
Cikin damuwa da jimami yace "yallab'ai inajin nauyin wannan alkawarin,domin duk cikin iyalinka ba mai baud'ed'd'en hali kamar *Aysher* gyara d'abiar ta abune mai matukar wuya."
Abbun yace "karkai saurin bashi kalmar wuya,ka d'aukesa matsayin abu mai matukar dauk'i sai yazo maka da sauk'i kayi adduar Allah ya baka ikon rik'ewa da gaskiya da jajircewa,bana haufi akanka mus'ab."
Ya zaiyyi da yallab'ai bazai iya bujirema wadannan bukatun ba,amman tabbas gyaran Aysher abune mai wuya,cikin sanyin murya yace masa "shikenan yalla6ai Allah ya shige mana gaba,insha Allahu ma babu abunda xai faru kana tare da iyalinka har iyakar rayuwa."******
Da wuya abu ya saka ni kuka amman wannan cin fuskar da Abbu yayi mun saida nayi kuka sosai,ranar ban koma gidan yadidi ba hostel na wuce wajen su fadila,wadanda sukaita tambayana meya sameni amman nak'i magana saida ma saukko don kaina na hkr.
Sai kuma nadamar abunda nayima Abbun ta shigeni,ashe har wani ya isa yasaka nai fushi da Abbuna irin haka bata ta6a faruwa tsakanin mu ba,sai naji hankalina ya tashi sosai na nemo wayata jikina yana rawa na soma kiran Abbun,amman harta karaci ringing dinta ta gama bai dauka ba saida nayima Abbu kira uku bai dauka ba,hankalina ya tashi ainun.
Na kira sofy takusan katsewa ta d'auka "oyoyo yaya nanah kwana biyu in nakira bana samunki,daxun har naba Abbu sallahu idan yazo yaban ke mugaisa."
Muryata na rawa nace "sofy nashiga ukuna nakira Abbu 3x bai dauka ba don Allah ki jaraba kiranshi kiji zai dauka,idan ya dauka kice inata nemansa fah hankalina ya tashi."
Cikin damuwa sofyn tace "yaya nanah kinma Abbu laifi ko?mekika masa babba haka nasan Abbu baya fushi dake"
Kamar zan fasa ihu nace "sofy ba wannan ba kije ki kirasa yanxun saiki kirani"
Tace "to ina xuwa"
Na sauke wayar ina runtse idona,ban tab'a kiran Abbu bai d'auka har sau uku ba,duk kiran da zan masa yana kusa kuma zai dauka idan ma nakira bai dauka ba to baxan cika nabiyu ba zai biyoni,shiyasa hankalina ya tashi ainun yau.
Fadila tace "nanah wai miye haka don Allah,tun ten rabonki da abinci duk kinbi kintashi hankalinki kibarsa idan yagama fushi zai nemeki,akanme xaki damu kanki."
Kallonta nake cike da mamaki nace "fadila kanki d'aya kuwa?Abbun kike cewa na rabu dashi yagama fushin zai neman?lallai bakida hankali Abbuna nefa bacin shi wagareni aduniyar nan da yakaisa muhimmamci,shine rayuwata dole hankalina ya tashi idan yana fushi dani,saboda fushi ba d'abiar sa bace,pls don't ever said that akan Abbuna"
Tab'e baki tayi tace "ok shikenan cikinki ai ba nawa ba."
Na koma na kwanta nabila data gama sallar la'asar wai sai yanxu take sallah la'asar karfe takwas na dare.
"Nanah ki rabu da fadila ba cikekken hankali ta cika ba,ban sani ba kodan bata daraja nata mahaifin yasa take ganin kowama kalarta ne"
Cikin masifa da fad'a fadila tace "dakata nabla karki soma zagina wlh,kowa ya tsaya iyakar akidarsa da halinsa bazai yuwu ku takura mun ba ehe."
Tsaki naja nace "pls karki cika mun kunne don Allah."
Nabla tatashi tafara kokarin dora sanwa don duk cikinsu itace mai kokarin sanwa,don fadila kullin saidai saurayinta yazo yafita da ita sutai restaurant basa dawowa sai shabiyu.
Waya ta dana tusa gaba tai kara nai saurin dubawa naga no din hamid,lumshe idona nayi na dauka cikin muryarsa mai masifar dadi yace mun "dear kina lfy kuwa"
Ajiyar zuciya nayi inajin idona yana cika da kwallah nace "I'm not feeling fine *hamid*"
Saurin tashi yayi zaune cikin damuwa,ga kuma sunan data kirasa dashi yayi masa mugun dadi.
Ya tattara duka hankalinsa da natsuwarsa yace "ohh my god *lolly* what's wrong with u pls"
Kiran sofy naga yana shigowa nace "pls bari na daga waya sister na nakirana."
"Oky"
Nabla tace "zakici taliya da miyar kwai nanah,naga bakici take a away din da fadila ta ajemaki ba."
Kai na d'aga mata alamun xanci nai dialing no din sofy........."yaya nanah munyi mgn da Abbu yanxun nan,mun jima dashi yana abuja sai gobe zai dawo gida."
Cikin damuwa nace "sofy amman kin gaya masa inata kiransa"
Tace "ehy yaya nanah ya fad'a mun,cewa yayi kinyi ma yah mus'ab rashin kunya shiyasa yayi fushi,kuma yana kiranki kika kyalesa baki dawo ba,bacin donke yazo yanada abunyi ya dakatar duk don ya ganki,amman kika masa haka."
Kwalla ke silalowa bisa kuncina nace cikin rawar murya "sofy don Allah kibasa hkr kice yadauki kirana bazan sake masa haka ba,hankalina ya kasa kwanciya akan haka"
Yar dariya tayi tace "yaya nanah kibar kuka to,zan kirasa yanxu"
Sauke wayar nayi ina goge kwallata nabila tace "kinsan Abba na haka ya tab'a yimun nanah!"
Nakalle ta nace "dagaske"
Tace "wlh kuwa saida Abba yayi sati babu ruwansa dani,ko kirana baya picking idan naje gaidasa saiya tashi nashiga damuwa sosai kawai don nayiwa mai mana wanki da guga tsawa harda mari."
Nace "nima fa don nagaya ma drivernsa magana yace dole saina gaidasa da bala'i saida na gaidasa wannan bakin cikin yasa nabaro shi nai tahowata,yana kirana naki komawa shine ransa yab'aci."
Fadila ta tab'e baki ta shige toilet nabla tace "kafin mushirya kamar zan haukace,saida nai masa alkawarin bazan sake masa haka ba sanan muka shirya."
Nace "ai nima na hkr,kawai dai na tsani gay din shegen miskili ne wlh duk miskilancina yafini,ga isa kamar dan gidan shugaban kasa.abunda yafi bani haushi kenan kowa yana girmamani cikin masu aikin gidanmu amman ban dashi,kamar kashi haka yake kallona"
Dariya nabla tayi tace "wlh haka ake fama dasu"
Kiran sofy ya shigo nai saurin dauka tace "yaya nanah yace ko kin kira bazaki samu ba ya saki black list,har sai kin shiga taitayinki"
Saurin tashi nai nace "sofy Abbun ne yafada maki haka" tace " wlh yaya nanah haka yace na bashi hkr amman saiya kashe wayarsa."
Kashe wayar nayi na koma na kwanta kamar marar lafiya,lallashina nabla tai tayi har na d'an samu karfi ta xuba mana taliyar mukaci sosai kafin na haye saman gado ina tunanin abunda yafaru.
Kiran hamid ya shigo jikina amace na d'auka ina yin shiru jin bazan magana ba yace "lolly"
Idona alumshe nace "niba lollyn ka bace"
Murmushi yayi yace "meke damunki naji muryarki kamar kina cikin damuwa."
Ahankali nake maganar ko su nabla basa jina ni haka nake wayata koma dawa nake.
Cikin dan shagwa6ar da ban san ma inayi ba nace "hamid Abbu na ne yake fushi dani"
Yace "wayyo Allah laifi kikai halan?kin bashi hkr kuma"
Nace "inata kiransa baya picking,karshe ma yasani black list"
Cikin taya ni jimami yace "Ayya lolly sorry karki damu zai huce kinjiko."
Nace "uhum."Fira yake mun cikin natsuwa da sanyinsa,hamid wani irin sanyi garesa duk ajinki inkina magana dashi sai notin kanki yafara kwancewa,gashi shima d'an shagwa6ane don zan iya cewa ma yafini har mamaki nake sosai.
Yamun bayanin kansa da gidansu shine nafarko kannesa mata biyu maza biyu,matan sunyi aure saura su uku maza.ya gaya mun yayi dogon karatu har PhD,kuma yana aiki a NNPC yazo hutune na karshen shekara rabon zai hadu dani ashe.Wasa wasa har zamuyi hutu Abbu bai neman ba kullin sai na nemesa amman bata tafiya,zuwa lokacin nayi nadama tafi cikon buhu,hamid ne yake kokarin kwantar mun da hankali..........yau yace mun zai koma Abuja wajen aiki kuma yana so mu had'u,nasan yau haduwar ta musamance don kuwa har yau baice mun ya na sona ba,nasan yau firar ta abance.
Daman tuni nabaro gidan yadidi saboda tashin hankalin da akai yasa Alh ya saki kishiryar tata,ganin haka sai nabar gidan amman ina zuwar mata yawo.
Nabla tana aji so dole da fadila zantafi saboda bana son fita nikadai duk da nayarda da hamid bazai abunda zai zubda darajarsa idona ba,kwalliya nayi mai kyau wadda nasan zata dauki hankalinsa sosai.
Ban iya heavy make up ba amman na iya tsara dressing na jiki,wanda shine yake matukar daukar hankalin maza da dama tattare dani,fuskata mai kyauce kobanyi kwalliya ba so nafi gane na saka farar powder da lipstick sai idan ina ra'ayin saka janbaki sai insa,amman ko kwalli ban damu da sawa ba.
Text yayi mun inda zan samesa muka fito fadila ke tuk'amu har muka isa wajen,tun da muka fito na hangesa shigarsa tayi masifar daukar hankalina fadila naji tace "wow irin wannan had'ewa haka wlh hamid ya had'u nanah"
Sai naji raina baiji dadin yabon datai masa ba,bance komi ba muka fara takawa har wajen da yayi mana buking.
Fuskarsa cike da murmushi mai tafiyar da zuciya,mikewa yayi yaja mun kujera na zauna.
"Ur welcome dear mezaki sha"
Na yamutsa fuska nace "only water"*bazan ringa typing kullin ba,duk bayan kwana daya ko biyu zakujini*
Mrs bb
Mom muhseen✍🏻
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...