part 17

116 7 0
                                    

*_NERNER AYSHER_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

🅿️........ 17

Kwance yake yana kallon silin gaba ki d'aya abunda yayi yake damunsa,meyasa zai kai hannu ya daki bakinta?Laifinta baikai har haka ba,anya tsaurinsa bai yawa ba ya lura sosai mami bataji dadin abunda yafaru ba,badai ta iya tanka masa akan haka ne kawai saboda tana ganin shine yake da iko da Nanah sama da ita,amman hakan ba shine zai saka ya kai hannu da sunan duka ba,ya sani ba daidai bane dukan matarka a addinance,amman bai yi haka don son ransa ba Aysher bata jin magana baya son tana masa musu balle gardama,har ma ta kaisi ga jayayya yana fad'a tana fad'a tabbas bai kyauta ba kuma insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba,tunda har yayi nasarar saka shakkarsa da tsoronsa acikin ranta hakan ya wadatar zai samu sauk'inta,zai rage duk wata tsaurarawa da yake mata,tashi yayi yaje yayo Alwalla ya dosa nafilfilun da yake duk karfe biyu zuwa hudun asuba.

Bazan iya misalta kuncin da zuciyata take ciki ba,hakika mus'ab yana d'an dana mani wani irin bacin rai da ada ban sansa ba sai yanxu,har ni zai saka kazamin hannunsa ya daki bakina just because of wannan villege girl d'in kidahuma da bata san komi ba,baki duk gamsa kuka To kau wallahi duk bala'in da zai faru saidai yafaru duk randa na ganta koda kofar dakina ne sai tagane bata da wayau,inyaso ya saka wuk'a ya yankani ya huta imagine wai wannan yarinyar yake tarewa fad'a,halan ma sonta yake har da yake gudun abunda zai bata mata.
Kwata nai kawai ina tsaki wlh ya gama ganin hakorina balle murmushina,balle har ya samu wata damar da zai mun magana na kulasa.............
Karar wayata ne ya fargar dani nai saurin cirota daga cajin dana sata,nabla na gani nai saurin d'agawa ina cewa "hello Nabla kina jina kuwa."
Tace "ina jinki nanah,wai lafiya meya samu wayarki ne?"
Ajiyar zuciya nai nace "nabla ba wayata kadai abu ya sama ba hardani,Nabla rayuwata ta juye gabaki d'aya nabla kwata kwata bana cikin farin ciki duniyar ta canza mun."
Hawaye suka silalo mun cikin damuwa tace "nai noticing haka nanah,don tunda naji shiru baki dawo sch ba nasan akwai damuwa,sannan naita faman nemanki awaya nima da tawa damuwar amman Abun mamaki da al'ajabin dana gani shine yasaka naji tawa damuwar nafilace."
Cikin dokantuwa da sonji abunda zatace nace "lafiya menene nabla sanar dani don Allah."
Gabana yana duka sosai duk da bansan me zata gaya mun ba,cikin damuwa tace "nanah ban tab'a ganin maci amanar mutun ba irin fadila,wlh fadila kasurgumar mayaudariya ce maha'inciya,ina nadamar saninta arayuwata akan abunda taimaki."
Hankalina yai mugun tashi jikina har rawa yake muryata ta shak'e nace "nabla gaya mun da sauri kar kisa zuciyata ta daina bugawa."
Tace "nanah wlh ina mai bakin cikin sanar dake wannan abun,amman dole ne na gaya maki don bazan iya boye maki ba, nanah ko kinsan *hamid d'inki da fadila anyi engagement d'insu*"
Diffff naji komi nawa ya tsaya da aiki na yan lokuta kafin wayar ta silale saman gadon daidai da silalowar hawayena,wani kuka yazo mun na fashe dashi ina cewa "innalillahi wa inna ilaihir raju'un shikenan,shikenan tawa ta kare rayuwata ta samu matsala,nashiga ukuna ni nanah wai mena aikata haka abubuwa suke lalace mun ne?innalillahi wayyo Allah na ni NERNER AYSHER tunda na rasa Abbu abubuwa suka tab'arb'are mani,komi baya mun dadi shikenan rayuwa ta juya mun baya."
Sai kuka ya sake kubce mun sosai da sosai nake kuka kamar yaune akace mun Abbun ya rasu,nabla sai mgn take bama na jinta saboda wayar na kasa ta silale,saida na sha kukana na koshi hawaye kawai ke kwarara na dauki wayar nace "nabla yaushe?ita tagaya maki?ganinsu kikai ko calendar kika gani?"
Mugun tausayin kawarta ne ya shigeta da tausayi har kwalla taji sun ciko idonta tace "Nanah abun duniya baya buya,fadila bata gaya mun ba tana ta dai hiding abubuwa wadanda na rasa ganewa,ranan kawai a class saiga class rame yazo da sticker yana announcement cewa ansaka ranar fadila idris bala amman bata gaya ma kowa ba,ga sunan ta nan da sunan hamid.koda na tirketa da zagi da tsinuwa akan abunda tai sai ce mun tai"

"Ke nifa bari kiji nabla tun ranar farko dana had'u da guy d'inan na kamu da sonsa,tunani na zai neman ko ya anshi no dina amman sai naga hankalinsa ba kaina yake yana ga nana,nikuma nai aniyar wlh banda miji sai shi,kuma ita da aka riga aia mata miji ba saita hkr dashi ba ni nasamu,ya nuna taurin kai sai kawai naje na mik'a sunan sa ga malamina yajawo mun zuciyarsa,gashinan kamar kwallon kafa haka nake garasa sai yadda nai dashi,ko uwarsa yanxu bata isa ta hana na juyasa ba don haka saiki je kigaya mata nasan abunda kike jira kiyi kenan."

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now