part 20

125 15 2
                                    

*_NERNER AYSHER_*

By
Mrs bb
Mom muhseen

Wattpad name
Humaira3461

🅿️........20

Wani pharmacy shorp muka tsaya ya fita yaje ya siyo mun maganin,harda robar swan ya taho da ita ya shigo ya mik'o mun tare da b'allo maganin yabani.
Ansa nai na runtse ido na jefa nabi da ruwan Allah yaso banyi amai ba don shima kaganin ba sonsa nake ba.
Magana yayi yace "ya wuce"

Kai na d'aga masa ya anshi robar ya rufe ya ajiye saman wani d'an rami dake jikin marfin motar Har muka isa ba wanda ya sake cewa d'an uwansa ci kanka.

Graduation d'in su Abdul yayi kyau sosai anbashi kyaututtuka saboda matsayinsa na d'alibi nai hazak'a da kwalwa acikin department d'insu,mus'ab ne ya zama wakilin Abbu yaje ya ansar masa akai masu hotuna sannan aka je wurin cin abincin ni kam lemu na iya sha,saida aka gama ba kowanne kyaututtukansa sannan aka fara aikin hotuna,don musamman Abdul ya samu photographer ya ringa kashe mana kala anyi hotuna sun kai talatin,dana gaji sai na koma can side na zauna ina kallonsu.

Mune bamu fito sch d'insu ba sai After la'asar munyi muguwar gajiya saida muka fara zuwa gidan su Abdul mukai salla sannan suka fita suka samo mana wani abincin saboda wancen dai ba irin wanda muka saba ci bane,saidai kaji da aka kawo kamar suyi mgn.

Dakin Abdul d'in muka sauka nida sofy saidai duk da haka na kasa samun natsuwa,saboda jikina na son wanka gashi babu kayan canzawa awurin shiyasa na hkr banyi ba,munci mun k'oshi sai bacci ya saceni don daman ina da k'ara'insa.

Ban tashi ba sai sai wurin magriba,mamaki ya kamani na juya na ga sofyn ma baccin tayi na tasheta mukai salla sannan nace ya kamata mutafi gida haka nan don gaskiya ina son nayi wanka.

Fitowa mukai falon ba kowa naja tsaki ina dafe kai don duk a k'age nake da na cire kayan jikina wlh,Abdul ne ya shigo ya ganmu nan zazzaune yace "tofah,kun tashi kenan to kuzo muje na kaiku shi yaya tuni ya tsufa agida ganin kuna bacci yasa yace idan kun tashi saina kaiku."
Tashi nai nayo gaba nabarsa da sofy suna magana,na bude motar na shiga sannan sai gasu sun fito suma.

Motar na tsayawa na fito nai ciki da alamun kamar baya nan,su sofyn suka shigo tana cewa "gidan bakowa to ina yaya yashiga."
Tab'e baki nai nikam nai daki abuna kayan na cire na wulli dasu don jinake ma wari suke saboda yinin da sukai jikina,wanka na fad'a na fara yi har wata ajiyar zuciya nake saukewa da naji ruwa ajikina ban jima ba na fito ina tsane jikina.
Sofyn ce ta shigo kamar zata fad'i tace "wlh Yaya nanah bakiji jikina ba kamar an mun dukan tsiya"
Yar dariya nai nace "Saiki hanzarta kiyi wanka zakiji dadi "

Tace "Allah sarki yaya ashe neman abinci ya fita gashi can ya dawo."

Banza nai mata na cigaba da mulke jikina da mai na gama shiryawa na saka turarukana na jawo wata yar riga tsawonta bai kai idon sawu ba,baka ce akwai wata yar falmaran jikinta navy blue sai stones ajiki.
Na saka hukar rigar bak'a na haye gado ina kunna data wayata,ina dudduba massages har sofy ta fito muna d'an firar yadda taron ya kasance,manyan mutane na gida Nigeria gasunan ganinsu arha.
Har da wasu abokan Abbu duk mun gansu mukaje muka gaidasu har ma suka yiwa Abdul kyautar kud'i a check kusan 3.5 million.

Bayan ta shirya tace"bari naje falo ke baki fitowa? yaya nanah zaman d'aki baya isarki wlh."
Nace "idan nazo falon wani abu zan maki ne?"
Tace "aidai ayi fira ko,don Allah kitaso muje na yau kawai muyi fira yaka junan mu tunda gobe jirgin dare zamu bi."
Taso wa nai nace "muje sarki uwar naci."
Dariya tayi sannan muka fice daga d'akin muka yo falon,waya yake sadda muka shigo falon da alamun dai da masu aikin restaurant ne.

Sofy yace ma "zo nan safiyya yi bugamun wannan lissafin ga warki yanxu yi sauri."

Zama tayi gefensa tana bude wayarta yana karantowa tana buga masa,idan suka taru saita fad'a masa total sai ya rubuta ga wata paper.
Sannan ya sake karanto mata still suna ta magana a waya shida faisal da ya sashi ya kula masa da wurin kafin ya dawo,estimate d'in abubuwan da za'a siyo na restaurant d'in akeyi.

NANAH AYSHERWhere stories live. Discover now