*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........33
Tun kafin ya zo ya bud'e kofar zuciyata take zillo kamar zata fito waje haka nakejin tana yi mani,bude k'ofar yayi ya tsaya yana kallona ni kuma nai k'asa dakai na kasa kallonsa sai alwallar k'uda nake da hannuwa na murmushi yayi yana kara kallonta tai kyau sosai ji yake kamar ya lasheta saboda ta zama kamar wata fulawa.
Kasa yayi da murya yace "kinxo taya ni kwana ne?"
Afirgice na d'ago ina kallonsa nai rau rau da idona daman kuma yanxu hawayena arha suke naja baya ina cewa cikin rawar murya.
"Wlh niba abunda ya kawoni ba kenan,kuma ma yadidi ce tace nazo bani nai niyyar zuwa ba."
Na juya zan koma don haushin maganar naji har raina,gani da gaske ta fiya zatai yai saurin riko hannuna yana yar dariya yace "ke baki san wasa ba ne wai?janki fa nake ai nasan daman ba zuwan kanki bane aikin yadidi ne ko?"
Na bata fuska kamar zan fashe da kuka nace "ni dai gaskiya karka sake yimun haka bana so,to mezan zo nayi adakinka."
Dariya ke cinsa yana dannewa amma duk da haka saida wata tafito yana yi yacw "to sorry zo muje muci abinci yunwa nakeji."
Yana jaye dani muka shiga dakin ni kaina saida na lumshe ido ina shakar sassanyen k'amshin mai dadi da shiga rai dakin yayi kyau sosai komi need gwanin sha'awa.
Kasa muka zauna saman lallausan kafet ya zuzzuba mana komi yana yi yana kallona,ni kuma daya kalleni saina bata fuska ina ture turen baki saidai yayi murmushi kawai,shigar sa tayi man kyau sai hasken dakin ya kara haske mun fuskarsa tayi wani fresh kamar naita shafawa da hannuna ba kamar da gashinsa na fuska ya wani kwanta irin dai asalin gashin fulanin,sajensa yatafi daidai da gemunsa mai ban sha'awa duk afakaice nake kare masa kallo,ni duk ada bana ganin wannan qualities dun nasa ayanxu nake ganin ko kusan bazan iya had'asa da hamid ba,kowa da irin type din kyansa amman ayanxu kam in zab'i za'abani ido rufe zan zab'i mus'ab har mamakin zuciyata nake yadda tai saurin narkewa akan sa."Ki daina wani satar kallona malama ki fito fili ki kalleni sosai."
Nai saurin kallonsa da mamaki yadda ya gane ina kallonsa nace "wai ni?lallai ma to ni ba kallonka nake ba baka ga daidai ba."
Zama yayi kusada ni yana daukar spoon yana fara motsa abinci cus cus ce da miyar zallar hanta yace "inba ga tsoro ba ki rantse ba satar kallona kike ba"
Na dauke kai gefe ina k'un k'uni d'ebowa yayi cikin spoon ya kawo bakina yana jefa idonsa cikin nawa yana wani irin narke mun su tare da lumshesu ban san lokacin da na shaka masa kukan shagwab'a ba ina juye juye saurin ajiye cokalin yayi yana kamo hannayena cikin sassanyar murya mai dan karen dadi dake ratsani yace "shiiiiiit menene wai?"
Nace "ba kai bane ba to kake kallona haka ni bana so wlh."
Dariya ya kama yi yana kallona yace "na rasa yadda zan nuna maki kinyi mun kyaune shiyasa na kasa daina kallonki,don Allah wane turare wannan kika sa?"
Na lumshe ido ina narke masa nace "mezakai dashi in nagaya maka"
Wani irin numfashi yaja idonsa naga ya d'an zana sai ya sake rike hannun nawa muryarsa ta yi wani iri yace "don Allah in zaki fita dai baki sawa ko?"
Yadda yayi tambayar zaka san zallar kishi ne ke cinsa nace "mezai hana insaka to?ina sawa mana"
Idonsa da suka canza kala ya zuba mun so ya tsare da su yana azabtar dani da su kasa magana yayi,sai ya dauki spoon d'insa ya fara cin abincin fuskarsa ta canza sosai babu annuri kallo daya zaka san ransa ya dagule baya cikin natsuwa har hakan ya sashi ya sark'e dan danan ya hau tari ba kakkautawa,ahaukace na jefar da wayata na zuba ruwa ina mik'a mashi hankalina ya tashi matuk'a don sosai yake yari yana dafe da kirjinsa amma memakon ya anshi ruwa sai ya ture hannuna,kuma har lokacin tarin yake sosai na rude sosai nace yayin da kwalla ke cika idona "meye haka wai,don Allah ka.....k...kasha baka ganin kana tari"
Sake ture cup d'in yayi yana tashi daga gaban abincin ya koma bakin bed ya sunkuya yana tarin kuma yak'i ansar ruwan,ai rikicewa nai sosai don inka ganshi cikin wannan halin zaka dauka asthma garesa don har numfashinsa yana daukewa.
Ban san lokacin da na saka masa kuka ba naja gefe ina saka kaina cikin guiwata saboda ban san abunyi ba,na rikice irin wannan kwarewar ce mutun har suma yana yi ban san meya fusata shi haka ba,shine zai hura kanshi da kin shan ruwa kuka nake sosai saida naji ya lafa da tarin naji hankalina ya d'an fara kwanciya,na d'ago ina kallonsa ban yi fushi ba na sake daukar cup din ruwan na matsa kusada shi muryaya da shashshekar kukan nace "kasha ruwan kaji,wlh in baka sha ba zanje ingaya ma yadidi."
Yana duk'e da kansa ya d'ago ya anshi cup d'in ya kai bakinsa yasha rabinsa ya ajiye saman soper,ya maida kanshi k'asa yana sauke numfashi mun jima ahaka ni dashi jikina duk yayi sanyi ba tare daya d'ago ba yace "kije kici abinci kije ki kwanta."
Dajin maganar kasan yana cikin damuwa sai na zauna gabansa na sake saka masa wani kukan nace "ni bazan ci ba inhar kai ma ba zaka ci ba,tunda ban san me nayi maka ba kawai zaka yi wannan abun."
D'agowa yayi idonsa sunyi jaa sosai saboda wuyar daya sha na tarin da yayi,har kirjinsa yana masa zafi sosai.
Muryar ta dishe sosai yace "baki san me kika mani ba Aysha?kika ce baki sani ba?"
Duburcewa nayi ina in ina nace "uhm.....to....ai"
Sai nayi shiru hawaye suna sulalo mani duk sai naji na zama sakara gabansa,jinai yace "taso zo nan"
Bazan iya masa musu ba na tashi na isa inda yake hannunsa ya mik'o mun na karasa ya zaunar dani gefensa muna fuskan juna,zuciyata fat fat take bugawa ya tallabo fuskata yana kallon cikin idona da ya sake sani jin ina tsuma na lumshe idona naji yace "da gaske kike kina fita da wannan turaren na jikinki.?"
Saurin bude idona nayi na sauke akansa ya jinjina mun kai yace "ki bani amsa"
Nai kasa da idona inajin yadda gabana yake beating sosai ahankali na bude bakina nace "nifa janka nake,wasa nakeyi fah ni yau ma na fara amfani dashi wlh"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "kina son ki kasheni."
Zaro idona nayi inajin iskar wurin tayi mun kad'an wurin shak'a kasa amsa shi nayi ya sake cewa "inhar kina son ki kashe ki gaya mun,don koda saud'aya kika sashi wani yaji zuciyata zata iya bugawa."
Wannan karon nafara rikicewa tashoshina sun fara toshewa na shiga ukuna!meye haka yake faruwa?wayyo Allah ban shirya ba wlh,wlh ban shirya ji yanxu ba zuciyata kar karwa take dan danan jikina ya hau tsuma.
Tashi nake niyyar yi na kasa saboda kaifin idonsa akaina muryata tana kerma nace "bari naci abincin yunwa nakeji."
Murmushin dabai shirya ba ya kubce masa ya kamani muka koma wurin cin abinci,muka fara ci ni kam a d'arare nake wurin sai tsakurar sa nake duk da yunwar dake kwalkwalata.
Jinai yace mun "da kin saki jiki kinci abinci don baki barin dakin nan sai cikin ki ya cika"
Kasa ansa shi nayi muka cigaba da ci har wanda ya zuba ya k'are na ajiye spoon d'in nace "na k'oshi Allah karka zuba wani"
Yace "ai bakici naman ba zauna "
Ya xuba mana pepe chicken d'in muna ci saiya dauki pies daya ya cire mun tsokar ya mik'o mun,har mukaci mai yawa amman can cikin raina mamakin kalaman sa na d'axun kawai nake,bana son ma nai tunanin me suke nufi don zuciyata kerma take,wai meyasa duk banji haka akan hamid ba ada can?to wai wane irin so nayi ma hamid wancen lokacin.
Jinai cikina ya cika dam tashi yayi ya shiga toilet na tattara wurin na had'e kan kwanonin na saka cikin basket din da aka had'o kayan ciki.
Fitowa yayi yace "zoki wanke hannunki."
Nace "in naje d'aki zan wanke tafiya zanyi dare yayi kuma bacci ma nakeji."
Na fad'a don dai kawai na gudu don lamarinsa ya fara bani tsoro,wai daman haka yake wannan guy d'in?wlh guduwa zan bazan iya zama ba.
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...