*_NANAH AYSHA_*
By
Mrs bb
Mom muhseenWattpad name
Humaira3461EXQUISITE WRITER'S FORUM EWF📝
(Home of Exquisite writer's)🅿️........38
Abbyn Anwar yana falonsa da yaran suna kallo momyn su tana serving dinsa abinci yajiyo jib jib na motoci aharabar gidan nasa,da mamaki yace "su waye ne sukazo?ni banda appointment da kowa!"
Ya fad'a da mamaki akan fuskarsa,tab'e baki tayi tace "to ni ina zan sani,?sai ka fita ka gani."
Kamar kau jiran umurninta yake ya maida rigarsa daya cire cikin sauri ya saka takalminsa ya fice yana tunanin waye zai zo masa haka gagab babu appointment.Guard's din da ya gani kewaye da gidan ya k'ara d'aukaka mamakinsa,idasa fitowa yayi daga kofar entrance din main falon su idonsa ya sauka *MINISTER* jikinsa na tsuma ya k'arasa wurin yana yi masa alamun girmamawa yana washe bakinsa yace"Allah ya taimakeka kaine anan gidan?yallab'ai da kanka haka?Ai da kana son ganina ba sai ka tako kazo ba wlh sainazo har office na taddaka"
Murmushi fafa yayi masa yana gyara zaman babbar rigarsa sannan ya mik'a masa hannu alamun su gaisa.
Bai musa ba ya bashi sukai musabaha fafan yace "ni kaina ban san gidan ka bane engineer sai da kafito"
Da mamaki yake cewa "to Amman yallab'ai wannan zuwan bazatar fa"
Murmushi yake yana rik'e da hannunsa suna takawa zuwa cikin gidan yace "engineer Akwai Ajiyata agidan nan naka don haka cikin yan kwana kin nan dole kayi hkr dani,har zuwa sadda zan d'auke abata."
Ras ras gaban Abby ya fad'i tunani yake ina maganarsa ta nufa,ya fahimce maganarsa ras yagane me yake nufi saidai kuma ko kusa bazai ma kawo ma ransa inda zuciyarsa ta darsa masa ba,yak'e kawai yake yi yace "yallab'ai Ajiya kuma?ani nan gidan ban aje abunda zan baka ba."
Murmushi fafa ya sake k'ayata fuskarsa dashi yace "bari dai na fito maka A mutun zahir,engineer *K'ANWAR KA RAYHANA NAZO BIKO* Abby jiyayi zuciyarsa zata fito waje saboda bugawar da tayi lokaci guda,idonsa duk awaje yake kallonsa bakinsa bud'e sai had'iyar busasshen miyau yake daker ya saita kanshi yana yak'e yace "yallab'ai wai kana nufin kaine tsohon mijinta?ya ilahi ko kad'an ban tab'a zama nayi tunanin hakan ba."
Murmushi fafa yayi kafin yace "Allah yasa zaka saka baki wurin lallashi,don wlh bazan iya daukar hkr ba"
Murmushin yak'e kawai Abby yake yace "bismillah yallab'ai mushiga daga ciki sai nayi mata magana"
Shiga gidan sukai yaja sa har zuwa hamshak'in falonsa da yake saukar manyan bak'insa suka shiga ya zauna sannan Abbyn anwar ya fito ya koma can falonsa yace "khaleesat don Allah ki tura sahura da abun tab'awa takai falon bak'ina *MINISTER SULAIMAN* ne yazo"
Jin ance minister tai saurin tashi tana washe baki tace "Allah yasa kwangilace Abbyn anwar"
Wani banzan kallo ya wurga mata yaja tsaki kawai yace "zaki je kiyi abunda nace ko kwad'ayinki zaki tsaya yi."
Ta murgud'a baki tana fita daman yaran duk sun tafi wurin karatu malamin su dake zuwa masu karin karatun qur'ani,tasleem tana can wurinsu.Ummi na zaune bedroom tana ta aiki a computer ga kwalin hollandia nan da cup tana sha time to time,yayin da takejin fad'uwar gaba na yawan zuwar mata saidai ta dafe kirjin nata tace "hazbunallahu wani imal wakil"
Adaddafe take aikin badan tana cikin natsuwa ba,don kawai ya zamar mata dole ne kawai.
Sannan mafarkin da tayi baccin bayan la'asar da tayi shine yafi komi tsaya mata arai,ita da bazata ce ta saka mus'ab aranta har haka ba duk da lokuta da dama yana fad'o mata arai har tayi mashi addua,ita tun wancen lokacin ta riga ta yafe sa tabarma Allah tunda tasan damuwarta da kukanta bazai saka ya dawo ba,balle tsawon wannan shekarun da aka d'auka ai tasan kila ma ya rasu.
Shiyasa take ciresa aranta don gudun damuwa ta saka bp d'inta hawa tasan in ya hau wahala take sha kafin ya sauka,amman mafarkinta ya saka taji tsananin son ganawa da yaronta,tana fatan ace kafin Allah ya anshi rayuwarta ta gana dashi tana cikin wannan tunanin ne taji an yi knocking bakin k'ofarta.
Cikin sanyin jiki tace "shigo"
Budewar akai ahankali ta sauke idonta akan Abbyn anwar,lumshe idonta tayi ta bud'e tace "yaya kaine?bari na fito falo to."
Ta fad'a tana aje computer saman bed side d'inta ba tare data kashe ba don bata gama ba,kallonta kawai yake yana jin zuciyarsa tana fatattakewa.
Jin bai tafi falon ba yasa ta juyo tana kallonsa,yadda taga fuskarsa ba annuri yasa gabanta ya fad'i cikin damuwa tace "yaya lafiya kuwa?,kaje falo ina zuwa don Allah."
Wani kallo yai mata kafin ya juya ya tafi falon,ajiyat zuciya tayi sannan ta d'auko mayafinta babba coffee brown da yayi shige da kayan da take sanye dasu ta yane kanta dashi sannan ta fito tana jawo k'ofar ta wuce falon,gabanta yana ta fad'uwa samunsa tayi ya dafe kanshi da duka hannayensa biyu.
Zama tayi kujerar dake kusa dashi cikin taushin murya tace "Abbyn Anwar meyake faruwa ne?ban saba ganin ka a irin wannan yana yin ba,don Allah ka sanar dani baffa ne ba lafiya"
D'ago kansa yayi yana zuba mata idanunsa jawur zaro ido tayi gabanta ya fad'i tace "innalillahi Abbyn anwar...........kinga Rayhana karki nuna wani baki san komi ba,daman nasan baki sona baki kaunata shiyasa kika biyo ta wannan hanyar don ki karya mun zuciya."
Hankalita ya tashi sosai tace cikin damuwa "Abbyn Anwar mekake cewa ne?na rantse maka da Allah ni ban san komi ba,wani abunne ya faru cikin gida?ko wani yazo yace maka wani abu akaina ne?"
Girgiza kai yayi yana huci yatashi tsaye yace "kije falon saukar bak'ina kina sa bak'o"
Yayi hanyar fita saurin tare sa tayi jikinya yana rawa da muryarta tace "kaga yaya nifa bansan nayi wani abuba,don Allah kayi mun bayani"
Kallonta yake sosai zuciyarsa na son yarda akan bata da masaniyar ma ko waye yazo wurinta,iska ya fesar yace "shige muje"
Ya fad'a yana d'aure fuska tamau ta had'iye miyau daker sannan taje ta sanyo takalma tazo ya sata gaba suka fice.
Tunda suka doshi falon takejin zuciyarta kamar ana dukanta,kamar zata daka tsalle tayo waje saboda fargaba da fad'uwar gaba.
Bakin kofar ta tsaya tana murtsikar yatsunta ya sake d'aure fuska yace "shige mana"
Jikinta har tsuma yake tace "wai waye ne don Allah?"
Harararta yayi yace "au ni kike tambaya?inkin shiga saiki ganema idonki."
Ya bude kofar ya shiga yabarta nan tafi karfin minty biyar a wurin saida ya bude ya mata magana sannan ta saka k'afarta ahankali cikin falon kamar zata shiga wuta kanta k'asa tayi sallama da siriryar muryarta.Fafa ya bud'e dukan idanunsa ya saukesu tas akanta wani sabon abu yaji ya rugo yazo ya finciki zuciyarsa,yaji wata kaunarta sabuwa dal ta sake ratsa zuciyarsa bakinsa ya kasa daina murmushi ya k'osa ta k'araso tayi masa magana yaji muryarta,shi sai yake ganin duk da ma kyanta bai nuna ba irin yanxu,ga ilimi ya ratsata ga wayewa da girman shekaru.
Abbyn anwar jiyake zuciyarsa kamar zata kece saboda kishi,jitayi wata murya da bazata tab'a iya mancewa da ita ba ta ratsa cikin kunnuwanta da cewar.
*"RAYHANA"*
amugun firgice ta d'ago kyawawan idanunta ta sauke akansa,dan danan kwalwarta ta shiga tariyo mata komi da komi kamar yanxu suke faruwa,zuciyarta da mugun sauri take bugawa kan kace me idonta ya juye daga fari ya koma jaa,fuskarta ta d'aureta tamau kamar bata tab'a sanin wata dariya ko murmushi ba,girgiza kai ta soma yi kafin ta saki murmushi bak'in ciki tace cikin kakkausar murya.
"Zaka b'ata ma kanka lokaci ne abanza a wofi *SULAIMAN*,watau ka sake dawowa rayuwata karo na biyu ko?lallai na yarda maza bakuda kunya,to bari kaji RAYHANAN daka sani da da yanxu ba d'aya bane,don haka tun wuri ka tasho kabar gidan nan don zan iya shuka maka duk wani rashin mutuncin da ke cikin kaina."
Tana gama fad'ar haka ta juya amugun fusace tabar falon,jikinta yana tsuma daker tagano dakinta.Fafa hankalinsa ba karamin tashi yayi ba,jikinsa yana rawa ya kalli Abbyn Anwar yace "engineer dama baka sanar da ita waye yazo ba,innalillahi wa inna ilaihir raju'un Aliyu ka taimaka mun ka shawo mun kanta,wlh tallahi bazan iya juriyar rasata ba.ta saurareni taji bayanina sannan tayi mun kome zatai mun ba,don Allah kayi mun wannan alfarmar."
Idonsa jawur yake maganar alamun dai hankalinsa tashe yake,Abbyn anwar kuwa yama rasa murna zai ko takaici nafarko dai yanxu yasan Rayhana ba itace ta bashi appointment ba,abun murnan kenan na biyu kuma na haishin baiga alamun minister zai hakura ba,shikuma baijin zai iya ganin wani ya aureta ba shi ba don jinta yake har cikin k'ok'on ransa.............********
*Kano*Ayi hkr da abunda ya samu wlh sai ahankali👏🏻
Mom muhseen ce✍🏻
YOU ARE READING
NANAH AYSHER
Fanfictionlabarine akan wata kyakkyawa yarinya Nanah Aysher wadda kudin mahaifinta yake dora mata girman kai da rashin daukar dan adam ba bakin komi ba,aduniyarta babu wani wanda take shayi ko shakka,bata tsoron kowa daya wuce babanta.wanan dalilin ya kaitaga...