PROLOGUE

2.8K 222 59
                                    

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

☆☆☆☆☆

RAWANIN TSIYA!!

A rayuwa wasu sukan sa ma kan su Girman kai na bala'i.. Sukan yi hakan ba don komai ba sai don wani abu da suke da shi.. wadannan abubuwan sune kyau, arziki, ilimi, wayewa, iya gayu da makamantan su.

Mutane masu irin wannan halin sukan qyamaci mutane tare da wulaqanta su... shin sun manta cewar Allah ne ya basu wadannan abubuwan da suke taqama da su?? shin sun manta cewar Allah da ya basu zai iya qwacewa ya ba wasu??

Hausawa dai sun ce:
Girman kai.... RAWANIN TSIYA!!

Mu sani, Allah baya tare da mai girman kai, Allah baya tare da mai wulaqanta al'umma.. Girman kai da ji-ji da kai hali ne na banza... hali wanda babu inda zai kai mai shi.. Hali ne Wanda idan har muna da shi toh muyi qoqari mu gyara domin kuwa ba abu bane mai kyau.

☆☆☆☆☆☆☆☆

HANIFA ALIYU BUGAJE ta kasance 'ya daya tak a wurin mahaifin ta.. ta kasance yarinya kyakyawa, ga ilimi, wayewa da iya gayu.. Mahaifin ta ya kasance mai arziki wanda ya sakar mata kudi take facaka da su...
'yar gata ce gaba da baya.

Wulaqanta mutane shi ya kasance halin ta.. wannan ne ya sanya mutane basu son ta ko alama.. kowa yana tir da halinta.

A duniya kaf mutum daya take girmamawa  take mutunta shi wanda bata iya tsallake duk wani umurni nashi.
Ba kowa bane wannan illa mahaifin ta!!

Hanifa dai baka isa ka sa ta yin abu ba da son ranta ba.. haka baka isa ka hana ta yin abinda ta ga daman yi ba. in other words, abinda take so shi take yi... It's more like a rayuwarta babu 'NO' a cikin dictionary dinta until he came along and changed everything.

ABUBAKAR SADIQ miskili ne na qarshe.. harkar gaban shi ita kadai ta dame shi don haka baya da lokacin damuwa da harkar wasu. Kyakyawa ne ajin farko, a no nonsense and a principled kinda guy.
Nothing much to be said about him for now.. well atleast not yet..!!

☆☆☆☆☆☆☆

Halinta na girman kai, rashin kunya da wulaqanci su suka sanya ya tsane ta.. baya qaunar ya bude idanuwa ya gan ta a gaban shi... she disgusts him!!

the feeling is mutual domin kuwa ita ma ta tsane shi.. ta tsane shi tun ranar da ta fara ganin shi... ta tsane shi saboda tunda ya shigo rayuwarta ya hana mata jin dadi kamar yadda ta saba..!!

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Qaddara ita ta hada su..
their path kept crossing as the enmity between them kept increasing..
Kwatsam sai maganar auren su ta shigo out of no where...

AURE??? 😮
OH YES 😏

HOW??? 😮
ITS FOR YOU TO FIND OUT 😜

☆☆☆☆☆☆☆

Za'a hada shi aure da yarinyar da ya fi tsana a duk fadin duniyan nan, yana da ikon qin amincewa da auren, kai babu ma aure a cikin plans dinshi toh amma kuma me????

Sadiq ya karbi auren Hanifa hannu bibbiyu.. Yayi haka ne don ya saita ta.. he vowed to make life a living hell for her wanda har sai ita da kanta ta sha wahala, ta natsu ta gyara halinta sannan ta saukar da girman kanta... daga nan kuwa ya sallame ta

☆☆☆☆☆☆☆

Za'a hada ta aure da mutumin da ta tsana a fadin duniyan nan, mutumin da ta gwammace ta mutu akan ta wayi gari ta gan ta a cikin gidan shi a matsayin matar shi.. Batada ikon qin amincewa da auren shi.. Mahaifinta ya bata sharadi akan kar ta kuskura ko da wasa ta kashe auren ta idan har ba mijinta ne ya sake ta da kanshi ba..

Hanifa ta karbi auren Sadiq hannu bibbiyu..
Tayi haka ne don kuwa ta riga ta shirya kalolin rashin mutuncin da zata yi mishi har ta qure shi ya gaji ya sake ta.. that way, she wont have problems with her Paapa!!

☆☆☆☆☆☆☆☆

HANIFA da girman kai, SADIQ da taurin kai

Zai sallame ta a duk lokacin da ta gyara hali sannan ta sauke girman kanta..

Zata karta mishi rashin mutuncin da ko kwana uku bazata yi ba a gidan zai gaji ya sallame ta

G A M E  O N

☆☆☆☆☆☆

Shin Sadiq zai gaji da halin Hanifa ya sallame ta kamar yadda take tunani???
Shin Hanifa zata sha wahala a hannun Sadiq ta saukar da girman kanta sannan ya sallame ta kamar yadda ya tsara??

Either way dai auren mutuwa zai yi..
Toh amma tambaya anan shine:

Shin baza'a zo wani lokaci da zasu yi sulhu da juna su fahimci juna komai ya zama normal ba??

Shin wannan QIYAYYAR bazata iya juyewa ta zama SOYAYYA ba???

☆☆☆☆☆☆☆

Hello my beautiful people...
I am here again with a brand new!!!

RAWANIN TSIYA..

follow me through the journey of Sadiq and Hanifa as we unravel the mystery behind their hate story..
or is it safe to call it a love story??

well, I guess not..
atleast not yet, right???

***********

Hoping to get as much support as possible..

VOTE💯
COMMENT💯
SHARE 💯
FOLLOW💯

God bless you as you do❤

⚠️PLAGIARISM NOT ALLOWED⚠️
BE WARNED

One Love❤
Fadeelarh1

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now