Chapter Four

1K 157 68
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

2 days later

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA-GRA

Paapa da Mamy ne a qayataccen dinning room na gidan suna dinner.

Hanifa ce ta shigo dinning room din sanye cikin wandon jogger na mata da 'yar qaramar t-shirt. Kanta babu hula don haka ta dunqule gashin kanta a tsakiyar kai.. qafafuwan ta sanye cikin slippers. Tayi kyau sossai, sai zuba qamshi take yi.

"Baby yau kinyi latti"

Tana murmushi ta qarasa kujerar da take kusa da shi wadda take fuskantar ta Mamy ta zauna yayinda take fadin "wallahi Paapa wankan ne yayi mun wahalan yi yau"

"Lazy girl" ya fada yana murmushi.

Itama murmushin tayi yayinda na ga ta danna wata na'ura akan table din wadda nake kyautata zaton bell ce. Aikuwa nan da nan na ga wata mai aiki ta shigo.

Har qasa ta russuna ta gaida Hanifa. A wulaqance tace "serve me"

Da sauri mai aikin ta shiga zuba mata kalolin abincin da ta san tana so and neatly in the right proportion. Allah dai ya taimaketa har ta gama zubawa bata yi laifi ba..

"Ki je ki gyara mun daki na yanzun"

"Toh Anty" mai aikin ta fada yayinda ta wuce sashen Hanifa.

Mamy dai tana mamakin halin banza irin na Hanifa. Yarinya qatuwa da ita ko girki bata iya ba balle gyaran gida... komai sai dai ayi mata.

She is even wondering idan tayi aure ya zatayi zaman a gidan miji?? da kanta kuma ta ba kanta amsa👉ai dayake namiji mai irin social status dinta zata aura he can afford all the luxuries for her...

"Munyi waya da Hafeez dazu yace mun he is coming back next week ko???" Paapa ya tambayi Mamy

"eh wallahi.. haka yace"

Masu karatu kar ku manta yaron Mamy mai suna Hafeez.. yayi karatun degree dinshi a Harvard University a qasar America inda ya karanci Economics.. bayan ya dawo yayi NYSC dinshi ne ya koma yayi MBA.. Finally dai yanzu ya gama shine zai dawo gida.

"Toh madallah... Allah ya dawo da shi lafiya"

Hanifa dai tana sauraron su amma fa bata ce komai ba.. ita dama idan har ta ji Paapa yana hira da Mamy bata sa baki.

Abincin ma dan kadan ta ci ta ture plate din yayinda ta dauki ruwa ta sha.

Paapa ne yace "Baby har kin qoshi??"

"Yes Paapa.. abincin bai yi dadi ba"

Mamy wadda take kallonta sossai ta cika da mamaki.. ya za'ayi Hanifa tace abincin nan bai yi dadi ba bayan ita da kanta tayi supervicing masu aiki wurin dafa shi infact kusan ma ita da dafa shi plus she is well known as a great cook.. how dare she?? ita me ya hana ta shiga ta dafa mai dadin???

"Haba Baby.. wannan abincin ne bai yi dadi ba?? gaskiya we need to question your tastebud because this dish tastes great"

Turo baki tayi tace "Paapa ni gaskiya ba wani dadi yayi ba"

"toh yanzu ya za'ayi?? ko za'a qara dafa miki wani ne... kin san bana so kina bacci on an empty stomach"

"No Paapa, I am okay"

Har ta miqe tsaye sai kuma ta koma ta zauna tace "yauwa Paapa.. dama ina so in fadi maka I need money to go shopping in Dubai and Paris.. ina buqatar new sets of clothes before I start working at the company"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now